← Book details Bakar Izaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 28

Sashe 15

Bakar Izaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

juyawa tayi tafice daga palon dan bata taba tunanin haisham zaiyi hakaba ita atunaninta zaitashine yayima Nafi tas kuma yafada mata ko ita wacece wurinshi

komawa tayi dakin da aka saukeso jiki asanyayi nanfa suka fara tambayarta ina angon

karya taimasu nacewa tundazo akace yabar gidan wai wani aikine yataso mashi nagaggawa

sundai jitane kawai amma basu yarda ba inshi yatafi to ina matarshi ita baza tazo sugaisa ba nandai suka gama shiri suka dauki hanyar kd

akabar amarya da angonta yayinda haisham yakejin wani tsoranta azuciyarshi dan yanaji zai iya batawa dakowa akanta

dan koda mahaifiyarshi takirashi tanuna mashi bacin ranta kan abinda yayi chaye ai laifin hajiya fadilar ne dan ita tashigo masu tunda safe kamar yace shibazai jeba

tunda yafadi haka hajiya maryam takashe waya dan tasan haisham baya cikin hankalinshi wanda baitaba yi mata musuba amma yau gashi harda gaya mata mgn akan yar uwarta

koda tagayama alhaji hamza baice komiba addu'a yace kawai susashi dan sai da yakoma kauyansu nafin dan hankalinshi yakasa kwanciya da abinda tsohon nan yafada mashi

aiko yana komawa yayi binkice saiso saiga gaskiya tafito to lakaci yariga daya qore har andaura aure shiyasa yayi haquri kawai yaci gaba dayi mashi addu,a

yanxu dai haisham da Nafi suna cikin wata3 amma haryanxu baije ganin gida ba wanda da bai iya sati1 baijeba

amma yau gashi har wata3 babushi babu lbrn shi dan ko waya aka kirashi kashe take

yayinda Nafi nachan na milkinta dan tazama itace mijin shine matar su Dr bash likkafa taci gaba

rugar jalo

wata uwar ashar tasa wace tafirgita hainan zonan dan ubanki kigayaman miye arigarki

salati uwale tasaki bayan tajayo Hainan ta ida tube mata rigar

nina shiga ukku uwale yanxu yarinyar nan harkin girma ammaba masun suni

hmmm kajiki uwale ke kamarba saida kika kai shekara20 kana kikai auran ba inji my daughter Lol

kamin taqara wata mgn mlm iro yashigo lfy uwale tunchan nakejin haya niyarki

kaidai bari mlm wai hainan hartaga hannunta amma
ba masunsine kuda yake wama zayace zai aureta taje takashe banxa

yaudai mlm iro yace bari yataba uwale
kallanta yayi yana murmushi uwale bakisan har shekara20 anakaiwa ba

batace mashi komiba tajuya tashige dakinta dan tasan mgn yaga yamata

yayinda yajuyo wurin Hainan yadaka mata tsawa ubanmi akai kika tsaya kina kallona da sauri tasadda kanta kasa tadauki rigarta tasa

tafita daga gidan gidan yaha tashiga tadauki tulo tatafi rafi tana xowa daidai kangon taga yazama gida maikyau wanda bata taba ganin irinshi ba da sauri tashige cikin gidan

😘Ansholly😘
😭BAKAR IZAYA😭
57_58

😘ANSHOLLY😘

haisham ne yafito sanye da jallabiya palon yakarasu inda ya iske kananshi Ameen da alhajinsu sunata lbr

shima wuri yasamu yaxauna kana yagaida mahaifin nashi cikin farin ciki ya amsa

Ameen ne yagaiyar dashi yaya anxo lfy

lfy kawai yace mashi dan yasan halin Ameen inhar yabiye mashi to yanxu xaici gabada zaulayarshi

duk da daura fuskar dayayi baisa Amern qyaleshi ba

yayana inadaiji yau allurar sojojin tamutsa naga sai wani cin mgni kake kuma

kamin yayi wata mgn haisham yakatse shi jeka dauko man abinci daga saman dining kakawo manshi nan

hajiya maryam ce dake fitowa daga dakinta tace aigwara daka turashi dauko abincin nan inba haka duk saiya cika maka kunnuwa da surutunshi

dariya sukai dan gidan kowa yasan surutun Ameen gashidai yashiga 22years amma baibar abin yaraba kodan yana ganinshi autane

nandai suka zauna anata lbrn duniya

chan alhaji hamxa yayi gyaran murya kana yafara mgn

haisham kaimana laifin da banyi tunanin ko Ameenulah xai iyashibs to amma danai wani tunanin sainaga haka Allah yahukunta domin aure rai gareshi amma duk da haka nahaneka da saurin saki

sakinma wanda Allah bayaso wato saki ukku duk abinda mace xataima karka qara hukunci da Saki kajini ko

insha Allahu Abba zan kiyaye to alhamdulillahi saika gayaman wacece wadda kakesan dan bana fatan kakai sati dayaba mata amma kasani inbata da tarbiyya baxan bari ka aureta bs

ko dar haisham baijiba dan yasan nafinshi tanada tarbiyya shi tun daxu daya kerata yace sun sauka har yanxuma baikara kiranta ba

mgnr abbanshi tadawo dashi daga tunanin sahibarshi kai mike saurare kayi mana shiru

lbrn da Nafi tabashi shiyabasu batare daya rage komiba

shiru yabiyo baya saida aka kusan 5min kana alhaji hamza yayi mgn to Allah yatabbatar mana da alkairi jibi in Allah yakaimu zanje sulajer nayi binkice kamar yada addini yace

kana yada dawo da kallansh wajan matarshi dan yaji batace komiba

yanaji kinyi shiru maryam to mixance alhaji sabida Allah haisham yarasa inda zaije naiman aure sai akauye bama wannan ba ni yarinyar bata kwanta manba duk da banganta

haba maryam baidace kice hakaba kedai kiyi mai addu'a Allah yasa yazame mai alkairi dan koni banji yariyan tayimanba amma ita mgnr aure intataho Allah akebarma xabi

su haisham din yakalla tashi kuwuce kuma adunga addu'a akan Allah yai zabi na alkairi
Amin sukace

kana yatashi yawuce part dinshi danji yake dazai iya haquri da Nafi dayayi tunda iyayanshi basuso saidai baxai iyaba

yana shiga ya dauko wayarshi yakira Nafi

*bayan kwana biyu*

angyara gidansu Nafi yayi kyau sosai dan tasakarma masu ginin kudi shiyasa saikai mata aiki da sauri
har sundawo tamkar bagidan ba

alhaji hamza yazo sulaja yayi binkice amma baisamu wani bad news ba dan Nafi tasayesu da kudi sai wurin mutum daya yaji baki yachanxa wanda yace mashi itace tai silar kashe ubanta kana tatafi yawan karuwanci

duk da mgnr wannan dan tsoho tayi tasiri xuciyar alhaji hamza amma saiya barta dan shikadene yabada wannan shedar saiyai la akari da mutanan dasukaita yaban halinta

anxu anyi gaisuwar aure kana suka roqi alfarmar sunaso ayi biki nanda sati daya kuma basusan komi na amarya

waliyan amarya sun yarda dan dama sungama mgn da nafin

*biki wan shagali*

ango yazubarda naira wanda shikanshi baisan nawa yakashe ba dan hatta kayan gidanshi saida aka kwashe aka zuba komi sabo

anyi chasu kala kala inda duk kayan amarya yan bariki ne sadi ma an aje auren karya agefe ankama samari

shidai haisham kallan ikon Allah kawai yake sai yanxu wani shashe na zuciyarshi yake hango mashi illar Nafi domin duk wanda yai mata kallo daya yaga tantiriyar yar bariki to shida miyasa bai gani ba sai yanxu

wani bangare na zuciyarshi yace sanda kake mata

tabbas yaga irin kallan da yan uwanshi kemata yasan dasun koma zasu faraba hajiyarshi lbrn yar barikice ya auro

ga Ameen ma duk party dinda akai daya yaje tunda yaje baisake zowa ba

miyasa yafara dana sani tunyanxu wanda yau yaci ace yana cikin farin ciki

juyawa yayi saman bed din turo qofar akayi ahankali Nafi ce gotashi cikin wata arniyar sleeping dress wace da ita dababu ita duk dayace

wata irin tsanarta haisham yaji takowa tayi tazo kusa dashi kamshin turaranta daya shaka yasashi rungumota dan wani santa yaji sb azuciyarshi nan suka cigaba da aikama juna sakonni

duk qwarewar haisham a romance saiyaji Nafi tazartashi abubuwan datake mashi har sunwuce tunaninshi remote yalatsa take hasken dakin yamutu

tom nima nace asuba tagari birgediya

*Ansholly*
😭BAKAR IZAYA😭
64_65

this pg.for mmn zee an mmn fatee tnx for du,a

😘ANSHOLLY😘

dariya mm sadiya take sosai yayinda habib yafita yai alamar kamar sannan yashigo

kallan hainan yayi yaga yadda tatsure take wata dariya tazo mashi amma saiya dake

qarasawa yayi dai dai inda sukeyayi nunawa yayi tamkar baisan abinda yafaruba mm miyasa ki dariya harara tadalla mai kana tace bansani ba

hainan kuwa tunda taga Habib tamiqe tsaye tana qare mashi kallo daya ba kyanshi dan bata taba ganin kyakkyawa kamar shiba

kallanshi take ko kyaftawa batayi juyowa yayi yai mata murmushi dan dagashi har mm sadiya sunga irin kallan datake mai

itama murmushin tayi mai yayinda takalli mm sadiya tace mama wannan mai kyan dankine gyada mata Kai tayi alamar eh

wurinshi hainan tataho kai yayana ne shima gyada mata kai yayi to ina babanmu yayi tafiya yace da ita to inya dawo zai daukeni

eh yace mata nandai taita tambayar shi shikuma yana bata amsa murmushi kawai mm sadiya keyi dan tana ganin shirman hainan yanxufa tagama kukan

kar ayanke mata kai amma gashi harta manta yaro yarone

kallansu tayi kana tace diyata zonan ba wata gardama tataho qasa tazauna

Habib bamu wuri tashi yayi yafita kallan Hainan tayi kana tafara mgn yanxu kin yarda damu kinsan baxan iya cere maki kaiba gyada kai tayi

to karki kuma irin wannan tunanin kinji to tace

kinaso nadinga koya maki karatu cikin murna ta amsa duk da batasan wane irin karatu ba

to yanxu xamu fara kallanta hainan tayi to mama ke baki baccine kamarni eh tace mata kana tajawo wani lttf da br

tafara rbt kallanta kawai hainan take dan tagama burgeta chan komi tatuna tatashi da sauri zata fita

ina zaki taji amfada juyowa tayi takalli mm sadiya amma tamkarba ita tayi mgnr ba ruwan dana ibo zankai dawo kizauna

anriga da ankai tanajin bata iyayi mata musu haka tadawo tazauna amma xuciyarta cike take fal da tsoro dan tasan inhar gari yawaye Allah kadaine xai amsheta wurin uwale ABCD tarubuta mata

mika mata tayi kana tacigaba da koya mata kamin safe ta iya har rubutawa take da kanta ko mama tayaba mata da qoqarinta

saita koma matasu alifun ba un haka taitayi saidai dan lokaci ta dago takallit mm sadiya

murmushi kawai take mata dan tasan tanaso taje gidane jeki kimaza kidawo

ajiye littafin tayi tafita da gudu dan tsoranta Allah tsoranta uwale amma tana zuwa gidan ta iske angama komi kuma tasan uwale bazata yiba tana cikin wannan tunanin uwale tafito adaki

wata irin tsawa tadaka mata dan ubanki mikike man cikin gida banace maki dakin gama aikin dakike ba kina fita kiban wuri

batace mata komiba tajuya tafita duk saida tabiya sauran gida jan taga duk ammasu komi kana takoma gidan mm sadiya isketa tayi tana sallah

itama tanaso tayi amma batasan ina xatayi alwala ba xama tayi har tagama inda hainan taqura mata ido tana kallon duk yadda yatake

saida tagama addu'oin ta kana tatashi kallan hainan tayi harkin dawo eh tace
kana tace ngd
Chapter 15 · 0% Book details