← Book details Bakar Izaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 28

Sashe 11

Bakar Izaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da sannu duhun yasoma yayewa lawai suka hango kwance rai ahannun Allah ga dukkan alamu suma yaye hainan sukaga tayi kanshi tana dariya idanta nazubar da jini

daga bulalar hannunta tayi wace suka gani tamkar anqara mata girma tashau da mashi cikin firgici yatashi kamin yai wani motsi tafisgeshi tawurga shi cikin su yalwa kara yasaki wace ga dukkan alamu kafarshi takare

ganin da sukayi tayo kansu yasasu shiga taita yinsu bakamar yalwa wace tasan xafin dukan hainan tun tana yarinya ma to ina gayanxu ta girma

ya yinda mlm iro yaqara gyara xama yasan dai bazata dakeshi ba tunda shi ubanta ne har cikin zuciyarshi yanada wannan yaqinin dan yasan daxuma data hada harda shi tadaka dan yana cikin duhu

saukar bulalar dayaji ajikinshi itace tasashi shedewa wanda saida tuna ninshi ya dauke nawucin gadi kamin yadawo daga tunanin yaqara jin wata aituni yai kasa sumamme

wata bulalar yaqaraji wace takusa sanadin fitar numfashinshi ga dukkan alamu bataso tana dukan mutum ya suma dumin inka suma to wacce xataima saikaji inama baka sumaba

suduka dukansu take tamkar tasamu jakkai duk jikinsu yai jina jina amma ba alamar tausayi ko gajiya awurinta Dan dariya ma take abun mamaki gata ita kadai ke dukan amma suduka jisuke ana zaula masu bulala

cikinsu ba wanda bai samu tijaba ga jini nazuba tamkar anyanka dabba mlm iro ko yafita haiya cinshi sosai dan tunda yake duniya bai taba shan bakar ixaya irinta yauba

bama amaganar su uwale domin da qyarne incikin da ake taqama dashi bai zube ba

yalwa kamtasha ixaya dan yau harta iyayanta sunsha zagi da suka haifota dantana ganin dabasu haifotaba baxatasha
wannan bakar ixayar ba sai kuma uwale wace tace abuta da ita takare koda itace tarage mace daya aduniya

*Ansholly*😭BAKAR IZAYA😭

40_41

😘Ansholly😘

*wannan pagen nakune masoya bakar izaya ina godiya da kaunarku*

*today I'm very happy welcome home baba buhari Allah yaqarama lafiya mai amfani yakareka daga sharrin maqiya*

cikin aman murya boka yafara mgn kinxo adai dai domin dabaki zoba to asirinku nagab da tonuwa dan yau yai niyar zuwa garinsu wurin matar daya saka

dayaje zata fada mashi itabata da aids kinga xaiyi bincike sosai kuma dole ne yagano ku

hotan haisham ne yamaye duka bangon dakin tamkar ana kallo yana zaune yana daura agogo acikin qaya tatcen bedroom dinshi kallansu boka yayi kana yafara magana acikin muryarshi marar dadin sauraro

kunga wannan shirin dayake yi to xaije wurin tsohowar matarshi ne amma tunda kunxo yanxu zan dakatar dashi

wasu surutai ya shigayi cikin lokaci kanqani saiga wani dan yaran aljani yazo jikinshi duk jini

bokan yafara yima wannan aljanin magana tareda nuna mashi photan haisham kaga wance nakeso kaje kamantar dashi matarshi karya qara tunaninta koda sunanta yaji bazai iya tunataba

kana inka gama aikinka zasu baka jini jinin yarinya kakeso kona babba da hannu kawai yaima bokan alama yabace bat shi bokan yasan komi yace

juyowa yayi wurinsu nafi kunasan kuce miyasa nace abatar wa haisham tunanin hafsa to hafsa kadaice wace xata tuna maku asiri kuma baxata iya zuwaga haisham ba harsai inshi yaje gareta
domin munsa mata wata katanga tsakanunsu

yau zamu tunxuroshi yazo gareki kisa manyan kaya kiyi shigar mutunci kana xamu mantar dashi cutar dake jikinshi domin bikinku yayi dadi inba hakaba bazai yiwata hidima ba

domin abun nadamunshi azuciya wani maganine yaba nafi karbi hannu naqerma takarba wannan inyazo kamin kifita kitabbatar kinyi wanka dashi wani yakuma miko mata da kwalli da turare wannan turaran inhar kika shafashi yaji kamshin shi to soyayyarki xataimai dirar mikiya

wannan kwallin ko inhar kika shafa karki kuskura kikalli wani inbashi ba akwai qalo bale wurin iyayanshi dan haka dole kikoma wurin uwarki kamin lakacin

nafi mgnr boka tabata tsoro totaya zata koma wurin mutanan da shekara goma yanxu bata qara wai wayarsu ba tasanma bazata karbu garesu ba

bokane yakatse mata tunanin datake kidaina tunanin cewa basu karbeki ba domin kina dani kina cika mana duk alqawarin dakika daukar mana dan haka aljani dan kundalo yana tare dake

nafi batayi mamaki ba jin boka nazai yano mata abinda take tunani domin tasaba jin abinda yafi haka indai wurin boka maigani har hanjine

wani magani ya bata mai kamar turare dakin dauki hanyar garin naku to kishafa wannan ba abinda suka isa suce maki

kallanshi yadawo dashi kan sadi da idanuwan shi masu firgita mutum babu wani alheri acikin tarar yaki da wanda kika kawo nan dan tunda kuka hadu nasani nima nahana yakusance ki domin yana dauke da aids ke kuma kina ganin kobaki maiba shiyasa bayasan kusantarki to kirabu dashi

ga bikin nafi zan hadaki da wanda yafishi yanxu bazan baki komi ba sai lokacin

ke kuma nafi wannan karin aljani dan kundalo jarirai yakeso guda biyu domin aikin yanada wahala kinga haryan xu yakasa shiga jikin haisham harya dauki hanyar kaduna saukima ba ajirgi yatafi ba amotane

nafi bata damuba jin boka yabukace jinin yara awajan domin dama tasaba duk sadda tazo saita bada jini shiyasa ake mata aiki mai kyau abinda yasama

gabanta yafadi jin abinda boka yace mata wai har yanxu dan kundalo baishiga jikin haisham ba

dariya boka yasa chan kuma ya daure fuskar tamkar gunki karkiji komi kamin ya isa nasan saiya mantar dashi

wata uwar tsawa yadaka kutashi kufice man dagani da sauri sukayo waje kayanda suka tube suka dauka sukasa dominshi aqa idarshi ba ashigar mai fada koda da dankwali ne

suna fitowa daga dajin sadi tasauke wata uwar ajiyar zuciya wai qawata boka yatai makeni ke inba danshi ba dayanxu nazama lbr

kedai bari sadi shiyasa nakejin maganar bokan nan domin da bazarshi nake rawa ke inba danshi ba da tuni bashir dinda nake taqama dashi yaguje ni nifa koda cewa yayi nacigaba da bauta mashi to wallahi xanyi

wa ixubillah Allah kakaremu da zuciyoyin mu fadawa halaka

motarta tatada suka qara gaba

haisham yana cikin mota dagashi sai PA dinshi sai drive sauran motocin cike suke da sojoji sai jiniya suke saki

cikin motarshi kuma karatun alqur'anine ketashi kira arar sudas domin yasaba duk sadda zaiyi tafiya indai amotane to kira aceke tashi

to shiyasa aljani dan kundalo yakasa shiga wurin amma dayake shi shedani ne saida yashiga duk yadda jikinshi ke konewa amma yahaqura

haisham ne yatashi da sauri kai kukashe wannan karatun akwai wani pilat nawa koki samanshi daga PA dinshi har drive saida suka dago suka kalleshi

*Ansholly*
😭BAKAR IZAYA😭
42_43

*Aunty ta baxan gaji dayi maki godiya ba nagode sosai Allah yabar zuminci*

su mlm iro sun galabaita iya galabaita amma hainan ko ajikinta dariyarta kawai take

gashi koda mutum yasuma bawai zata qyaleshi bane saisunji inama basu sumaba

haka taita dukansu Abu tun bakwai na safe har akai kiran sallah magariba kana taqyalesu suduka basusan inda kansu yakeba itama sulalewa tayi akasa sume

yayinda cikin rugar kowa yake mamakin ardo dan bainuna wata damuwa ba nanfa yan gulma suka fara kawo mashi gulmar cewa yaqori mlm iro daga cikin rugar tunda har abin yaxo kanshi

taka masu birki yayi yace bazai koresuba shiya dauki kaddara yasan kuma Allan daya bashi yusif shiya amshe shi baxai xama daga cikin jahilan mutane ba

ya yinda mutane dayawa bahaka suka soba sunso aima mlm iro korar kare tuntini

ammashi ardon yaqi to yanxu zasusa tunda abin yatabashi zai dauwani mataki domin da suna ganin Dan abin vaixo kanshi bane shiyasa yaqi daukar wani mataki

juyawa sukai kowa yakama gabanshi dan sunsan koda zasu kwana awurin suna cemashi yakori iro bazai yiba

duk cikin yan uwan su lawai ba Wanda yaqara tunaninsu

saida akai kiran sallah kana matar lawai tatuna cewa tundazu daya fita xuwa gidan mlm iro baidawo ba da sauri tayi hanyar soro tana tunanin ya akaima bata tuna dashiba sai yanxu

tana fita takira wan mijinta tafada mashi abinda yafaru dawowa yayi yafa dama sauran mutanan dake wurin abinda ke faruwa kowa sai yanzu yake tunanin ya akai suka manta da lawai bayan shiya dace yarife danshi

wanine yafara magana dazufa naga audu yake ceman gidan iro xaixo dan matarshi ta mutu shikuma bazai yarda ba dole saiya dauki mataki

amma abun mamaki har yanxu ban qara ganinshi ba kuma koda mukaje maqabarta rife matarshi banda shi mukaje

wan lawai ne yayi magana yanxu dai mutashi mije miyi sallah inmun gama saimu shiga gidan iron muga lafiya ke kuma kikoma cikin gidan harmu dawo to kawai tace mashi

su sukai hanyar masallaci itakuma takoma cikin gidan tana shiga yan uwan lawai mata suka kama tambayarta wai ina yake

nan tagaya masu komi yafaru shiru sukai ba Wanda yaqara magana

koda aka gama sallah wan lawai tashi yayi yafa dama mutane abinda yake faruwa nanfa kowa yafara cewa shima baiga dan uwanshi

liman ne yace sutashi suje gidan iron sugani ba wanda yayi musu haka suka fito suka kama hanya

suna isa qofar gidan suka iske mata cike da qofar ba wanda yai masu magana cikinsu liman domin sunsan matan wa inda ke cikin gidan mlm iro ne sai kuma yan uwansu

shegewa sukai cikin gidan amma asoro sukaci karo da gawar auwalu wanda yafito yabarsu mlm iro

ihu matarshi tasaka shikenan ankashe man miji aradun Allah baxan yarda ba arado nima saina kasheta

ba wanda yatan kamata domin kowa zuciyarshi iya wuya take dan suna tinanin dukta kashesu

suna shiga cikin gidan suka iskesu yashe kasa wanda saika qura ido sosai kana kagane suna nunfashi

ya yinda hainan take chan gefe ayashe amma shigowar mutane yasata tashi zaune cikin firgita

kamin ta tabbatar da wani yanayi take ciki matar auwalu tashigo tamkar kububuwa tayi kan hainan amma kamin taqarasa akai wani irin juyi da ita aka bugata kasa wani irin ihu tayi wanda gadukkan alamu tasamu tija qafa da hannu kowa yaji tausayinta yayinda hainan kanta yake duqe tsakanun
cinyoyin tana jiran taji duka

amma mai makon haka saitaji ihu da sauri tadago kanta wacce tagani ayashe kasace tayi mamaki ita data taho dukanta to ya akai hakan yafaru

wurinsu lawai sukayi matarshi da sauri tayi kan mijinta yadda taganshi yasa hankalinta tashi domin duk jikinshi jini yake fitarwa

cikin sauri take mgn mlm waye yaimaka wannan aikin aradun Allah kowa nene baxan barshi ba domin ita har azuciyarta batai tunanin hainan xata iya yimasu haka ba
Chapter 11 · 0% Book details