← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 37

Sashe 4

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

0⃣0⃣4⃣
......... Ya sharara mata wani kwakkwaran mari. Ta gigice ta kidime ta runtse ido kanta na juyawa ta rasa duniyar da take, tana jin hancin ta na tsiyaya amma bata San shin majina ce, ruwa ne ko jini ba, sama sama take jiyo amon muryar sa. Wallahi wallahi ranar da kika kara ambaton sunan nan da wannan shegen bakin naki sai kin gane kurenki. Ya ingizata tayi baya ta fadi saman bokitin da ya harbar. Kin ga layin nan? Idan kika kara biyoshi na rantse da Allah sai na batar dake Nigeria ko kuwa waye ubanki......
Ya sa kafa ya shuri dambun naman dake baje kasa ya watsa mata ga jiki.
Hazo hazo take ganin tafiyar sa har ya isa inda motocin suke, tafi mintuna ashirin kafin kanta ya fara saisaita, ganin jini face face a jikin hijabin ta yasa ta kara kidimewa. Tayi saurin toshe hancin da sauri cike da tsoron irin jinin dake zuba. Ta rushe da wani irin kuka wannan masifa dame tayi kama ni umaimah?
Yau mashin ta hawo ba inda tayi ma tsinke sai gidan Alhaji yakuba. Hankalin hajiya ya tashi amma sai tayi mata karya da hatsari sukayi a hanya, barin fuskarta kumbure. Wallahi sai na zubda mishi jini nima ta fada a hankali.
Hajiya ki dauki kayan nan na baki idan naje dasu gida kin tabbar masifar da zasu janyo mun.
A a zan dai ajiye miki, babu abinda zanyi dasu nikam,
Wallahi na baki, ai ba roko na kikayi ba hasali ma duka daga ciki ba abinda zan iya amfani dashi.
Shiru kawai tayi mata.
Tana shiga gida ta iske su lubabatu sun fiddo jakar kayan ta suna ta rububin rabawa, tana shigowa rayya tayi saurin tarar ta ina son na jikin ta wallahi na riga.
Ko kadan bataji komai ba domin idan da sabo ta saba tana yin magana iyayen zasu ce tabar musu tunda gobe ma wasu zata samo. Su kuma sai su duba tsofaffi da suka gaji dasu cikin nasu su bata, kai kawai ta girgiza ta wuce tana cewa qala za a fadawa yaya Abba karya da gaskiya ace ta zagi iyayen ta ya lakada mata tsinannen duka da waya.
Ta dauki naira goma ta siyo reza sabuwa ta daure a habar kallabi.
Baban su idan ya fita shidda na safe baya dawowa sai shabiyun dare kasuwa kullum.
Mamar umar kuwa waya ta dauka ta kira hajiya, bayan sun gaisa ta ce bakuwa ta dawo lafiya?
Wane lafiya dan adaidaita ya tandarata da kasa duk ta jeme fuska, subhanallahi tana ina? Ta tafi gida ai da sauki na bata magani nan.
Duk sai ta kidime, kwantar da hankalinki wallahi da sauki, to shi kenan ta ajiye waya, amma ta kasa daurewa sai kawai tace azo a kaita, tana kwance daki suka shigo da goggo, zumbur ta mike, ohh uwani ashe haduwa kikayi da tsautsayi haka? Tayi zuru zuru mutanen gidan chirko chirko....... Mamah da hajiya ta aikeni gidan ki wajen dawowa muka fadi da adaidaita ai da sauki ta karasa maganar tana satar kallon su goggo.
Zata kara magana tayi saurin cewa gasu goggo da yan uwana hajiya.
Ai mun gaisa, ya jikin?
Alhamdulillah,
Zaki shiga wurin hajiyar?
Data zo zatayi magana sai umaimar ta kakalo wata har hajiyar ta fahimta tunda ba yarinya bace, Allah ya bada lafiya ta mike, Don Allah idan mahaifinta yazo ina neman alfarma a bani umaimah tana zuwa tana kama mun aiki ni din yar uwar hajiya....umaimah tayi karaf gidan Alhaji yakuba hajiyar su fiddausi , ta balle jaka ta damtso yan dari biyar biyar ta bawa goggo jummai ga wannan a rabawa yara.
Wufff goggo hansatu ta wafce too too Allah ya biya hajiya za a fada mishi ai duk an zama daya, sukayi daki umaimah ta rakata har mota sannan ta dawo, bata bi ta Kansu ba domin tasan naira babu ita ciki,
Suna isa ta tarar dashi falo a tsaye, yana safa da marwa, mamee ya tunkaro ta rai bace lillahi wa rasuluhi wannan dame yayi kama yaya zaki ringa fita any how na dawo kowa yace baisan Ina... Gidan uwaka naje, wai har yaushe zakayi hankali umar don iyayenka nice na haifeka ko kaine ka haifeni?
Yarinya tazo guna girma da arziki ta yi hatsari sai in ki zuwa dubo ta? Mamee kuma ko waya bazakiyi man ba kin San sarai abubuwan dake faruwa....bazan kiraka ba din na ce anki a kiraka ya wuce cikin fushi sai kuma ya yi sukuku ya bita mamee nifa duk abin nan lafiyar ki nake ji .... Ta juyo a hasale ni kuma lafiyar uwani nake ji....
Sai ya rungumota ta baya wai wacece wannan uwani dake Neman kwace man mamee? Na fara kishi fa ya saketa tare da tirjewa kamar karamin yaro yanda yakeyi mata ta ingijeshi kai tafi can ta shige daki,bya bita yayi ta lallashi har sai da ta washe, na dauko uwani aiki zaka ringa biyanta albashi, yayi murmushi an gama nawa kika yanka mata? Dubu talatin.....talatin mamee hada bangwayen gidan zata ringa wankewa? Idan baka iyawa ni na biyata..... Inji waye ko miliyan kika ce air dole a biya mamee duk sukayi dariya, Karfe biyar goggo ta tasheta, Ke tashi Alhaji ya amince da zuwa aikin ki maza kiyi man wanke wanke don ki tafi da wuri, bata ce komai ba ta tashi bayan ta gama sallah ta hau gyarawa bakwai tabar gidan ta sami hajiya ta fada mata komai har ta na kwallah. Nasan za a rina kawai raina yaban sai ta amsheki , ki kyalesu Kansu suke wulakantawa umaimah kedai ki ci gaba da tsare gaskiyar ki baki sata na shaide ki kada ki yarda ki wulakanta kanki kinji?
Tun daga farkon layi tace a ajiyeta ta fiddo reza ta damtse a hannu ya Allah ka hada ni da mugun nan azzalumi, tafe take amma layin kamar anyi Shara shigowa farkon layin sojoji ne tsare da ba kowa suke bari ya ratso ba itama ansan da zuwanta tun jiya, ta fara hango tsiraran sojoji na kara kaina data fara dumfarar gidan kamar ance ta waiga baya kawai taga mutum na sassarfa da kayan gudu. Ta ware ido wallahi shine tafe kawai sai ta tsaya chak!
Daya, biyu, uku,..... Tara...... Kawai yazo zai gifta ta kunnen sa da ear piece ko alama bai lura da mutum ba hanakalin sa na can hannu tasa ta damko cinyar hannun sa ya dawo baya da sauri kafin ya hankalta ta farde mishi tsakiyar hannu ta kwasa a guje. Jini ya fartso ya dafe hannun innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ya bita da kallo har ta kule, nan ta kwana? Yarinyar nan ko aljana ce ni umar?
Jini ke tarara kamar fanfo haka ya kara gidan yace maza a tado doctor, sai da akayi mishi dinki, azabar duniya ta addabeshi yazanyi da yarinyar nan kada tasa inyi abinda ban da niyya anya bazan kashe ta ba kuwa?
Idanun sa jawur kamar yayi ta kurma ihu, a kidime mamee ta shigo umar rauni kaji? Wallahi mamee Yankewa nayi,
Dami?
Yayi shiru...
Kai dami ka yanke?
Ina jin ko wuka ce?
Kana jin? Baka da tabbas ne? Yayi dabur dabur wuka ce mamee ya ballo magunguna ya sha ta bishi da kallo umar menene ya faru?
Ya kakaro murmushi is okay mamee bari in watsa ruwa ya mike zuwa toilet ta bishi da ido kawai, ya hada kai da bango ya dafe kansa kashe ta zanyi tabbas wani yayi hayar yarinyar nan don ta shigo rayuwa ta negatively I must kill her.....
Mama lafiya? Umaimah ta riketa, kaini yau naga masifa wallahi umar ne yayi mugun rauni, wannan zafin rai na wannan yaro ya Allah ka rage mishi.
Ta zaunar da ita Amin mamah ungo tea kisha ko in kwaso miki kalacin nan?
A a barshi ya shiga wanka daya fito zamu karya. Mama karfe sha daya fa bakyajin yunwa? Ko ina ji dole in jirashi in ba haka ba to bazai ci komai ba zai fita, gashi baya cin abincin ko ina sai nan.
To shi kenan yanzu ni meye aikina, eh wallahi har yanzu tunani ma nakeyi
Ikon Allah umaimah tace a hankali ta mike muje bisa table kafin ya fito. Kema dauko plate ki ajiye nan ta nuna mata kujera jeri jeri haka ake ta zarya zuwa gaida ta ma'aikatan gidan da matan kannen ta, duk Wanda yazo sai tace ga uwani itama daga yau a gidan nan zata ringa zama...... karar rufewar kofar ya antayo wani mugun da dadden kamshi tayi saurin kallon inda karar ta fito zumbur ta mike akayi rashin sa'a kujerar tayi baya a wuntsula tayi saurin tashi tana baya baya a firgice, ke uwani lafiya kai rike man ita mamee ta fada ganin tana niyyar kwasawa da gudu duk ta fita hayyacinta.
Step din karshe idanun sa suka sauka kanta ya kara bude ido ko mafarki yakeyi................

*Maman Abdallah*

😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘

💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣0⃣5⃣

.....Mafarki yakeyi ko me?
Da gudu ya karasa saukowa ganin ta kwasa guje, karku bari ta fita...... Ya fada da karfi damka daya kawu karami yayi mata sai kawai ta sulale kasa tare da kurma ihu wayyo na shiga uku.........
Mamee ta rikice ganin umar ya finciko 'yar mutane ubanwa kika zo yi anan....kai dakata, ta finciko ta da karfi ta kuwa makalkaleta ki dubi Allah da manzon sa ki ceceni na tuba mugu ne...... Ya zagayo zai damko ta yana huci duk suka juya tare da mameee kai wai meye haka, wallahi yau sai naga bayan yarinyar nan na amince idan ta mutu nima a kasheni.
Hankalin mamee ya tashi matuka don haihuwar danayi maka umar ka saurara man.....
Umaimah ta hadiye wani mugun miyau tana tuno maganar sa, *wallahi wallahi ko layin gidan nan kika kara biyowa sai na sanya an batar dake......*

Ta zaro ido abubuwan da suka dunga faruwa suna dawo mata. Na shiga uku na jefa kaina masifa ni umaimah cikin ta ya dunga wani irin rugugi. Yunkuri yakeyi mamee na karewa, mamee ki dubi Allah ki matsa, bazan matsa ba kayi aika aika, to kyale yarinyar nan tabar gidan nan kada in saba umarnin ki yau.
Sai dai in bita mu tafi tare,......ya zaro ido what??
Chapter 4 · 0% Book details