Sashe 25
Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
sai anjima ba.......ya kyalkyace da dariya yanzu dai rufo kofar kafin sauro ya halakamu. *kut*.....kishi umaimah ki ce na shiga uku. Tayi kicin kicin ita dole fushi takeyi ya kwanto jikin ta ya janyo kofar tare da locking kawai ya baje bisa kafafunta....... Malam daga ni banda kwari kada ka karya ni. Ya mata banza ya latso lambar da aka kirashi, yasa hands free, hello sir, Yawwa ina jinki menene? Dama jirgin nan ne da zai sauka lagos da kaya yazo, na port Harcourt kuma munyi waya in the next two hours zai iso. Okay yayi kyau sai ki kira *BASHIR* Suyi magana da Agents. Okay sir, ya kashe yana kallon umaimah, *What next?* Ta danyi murmushi yo wani abu na ce? Sai kince wani abu? Gashi zaki gudu kuma wai ni duk ina kokarin baki full time bana son wani issue ya shiga lokacin ki. Wasa fa nake... Ya tallabo fuskarta karya kikeyi wallahi kishi ne. Ta runtse ido *Wayyo Allah* ya tashi da sauri lafiya? Kafafu na sukayi *Yami* Ya kyalkyace da dariya wallahi baki kyautawa yami kamar wani kwanannen abinci? Ya bata labarin yanda sukayi da Babanta, ta ce, Ohh Allah sarki. Ashe Allah yamun *Alam nasharaha* ta banka mishi harara ai wallahi da kauye zan gudu. Ina zullumin gobe wallahi saboda zama kusa da mamee takurani yakeyi banga dalilin da zaisa ka assasa sai na dawo gidan da kwana ba. *Baza ki gane bane yarinya* Gobe zan aiko a daukeki da safen saboda kayanki....... Bana so. Ya yi murmushi to kawo wannan nayi miki gaba dasu. Hmmm kawai ta ce, Sai sha daya saura suka rabu. Karfe tara ta fito gida amma anan waje ta tarar da drivern shi. Babu yanda ta iya dole ta shiga, su lubabatu na ta mamaki. Malam bawa kuma yaki cema kowa komai. Isarta bata tarar dasu Aunty jamila ba madaki ya masu korar kare jiya bayan ya koma ya tarar sun tsare namee suna mata tambayoyi da maganganu akan umaimah. Karfe goma ya sauko zai tafi office mamee ina uwani? Ta na ciki tana shiri, Shiri? Eh zan aiketa cikin gari ne. Okay to tayi sauri na ajiyeta daga nan mu biya office kawai ta dawo miki da sakon, Kwarai kuwa kaga har na manta da munyi maganar. Ta fito cikin atamfa dinkin doguwar riga yasha stones, ta yafo dan gyale batayi tunanin yana falon ba ta fito da gyalen a hannu tana gyara dauri. Mamee ta washe fuska, fara'ar ta ta karu, Uwani ashe kin dinka atamfar nan? Nima kuwa yau tawa zan saka kai amma naji dadi. Ta danyi yar dariya, waya miki dinkin nan? Hajiya ce ta bada mun......au haba? Ya kasa motsi kamar ya rukota yakeji kalacin da bai karasa ba kenan ya ce muje kawai, Ta kalleshi tana harara....... Mamee fada mata kada ta batan lokaci ya fara duba agogo. Zai ajiyeki ne amma zaki karbo mun sako wurin sa. Ta ce toh, suka fita, Yana rufe kofa ya janyo ta *Wai ke yaushe zaki waye?* Me nayi? Ba ko gaisuwa? To sakeni dai ka kalli gabanka, bai saketa ya dan waiga masu gadi ne da jama'an gida suka taho gaisuwa. Ya kara riketa ya sha mur, Haka ya gaisa da kowa duk wanda ya gaidashi sai ya ce *Ranki shi dade barka da safiya* mutum biyu ta amsawa, kunya ta dunga tsunkulin sa ta baya yayi mata banza. Suna shiga mota ya shako wuyanta ke wai *Yar fari ce?* ........ *kuma auta* ta fada. Kina mintsili na gaban mutane. Allah cizonka zanyi. Ya kyalkyace da dariya. Yanzu ni zan gaisheki ko kuwa kece? Wanda duk ka zaba . Yayi murmushi ina kwana, An tashi lafiya? Ya kara yin dariya naga kin fara *Wulakanci da rai* ta yi murmushi *Wai ma* Ya na zuwa office ya tarar da dandazon yan jaridu, yaki fita mota ya ce maza ace su tafi sai karfe biyu su dawo baida appointment da kowa yanzu. Sai da ya tabbatar sun watse sannan suka fito shida umaimah taki jerawa dashi daya Dan waigo sai ta nemi kwasawa da gudu ta rike riga, Ya sha mur meye kikeyi haka? Eh anji wuce dai muje zan bika abaya. Murmushi kawai yayi ya wuce body guards sun baibayeshi sunata mazurai. Dai dai an bude mishi kofa wata matashiyar mata ta iso..... *Yaro matashi*.......ya waigo da sauri yana murmushi tana zuwa ta fada jikinsa sukayi *Hugging* umaimah ta ja baya da sauri tare da fiddo ido kirjinta ya buga da karfi. Tare suka fara shiga office din , umaimah na ganin haka ta yi baya tabar wurin da gudu. Tana fita harabar office din ta tari mashin tare da fadin *TAL'UDU*................