Sashe 19
Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
....... Tana shiga ko zama batayi ba goggo jummai ta nuna mata tulin kayan wankin ta ita da yara,
Ko sallar magriba batayi ba ta shiga yi don ko hijabi ta nufi cirewa ta tabbatar sai ta daketa,
Karfe takwas da rabi taci dunin wankin sosai, duk suna bisa tabarma ana ta shewa ita ta basu baya.
Tsit taji gidan yayi kamar wuta ta dauke ta juyo da sauri, katti ta gani ko wane da bakaken kaya tadan ware ido nan da nan ta gane ko su waye, ta mike zumbur dai dai shi ma ya shigo wasu na binsa a baya.
Duk su goggo suka makure sun kasa ko motsi ganin ko wane da bindiga,
*Sannu da zuwa*..... Ta fada hannunta jage jage da kumfa, ya kalleta Tun daga sama har kasa sannan ya fara waiwaye ya hango tulun wankin da ke ajiye da kuma Wanda ke a robobi manya.
Ya sha mur *Zuwa na yi in miki gargadi na karshe*
Tunda mamee ta na ce sai kin mata aiki to babu yanda zanyi domin duk abinda takeso bana kin sa matsalar bazan taba daukar *Kazanta ba* duk yan aikin gidana babu kazama irin ki, ya nufeta kamar zai shaketa tayi baya ya dan bita, *Kinga wannan jakar?* kaya ne a ciki Su zaki ringa sakawa kina zuwa aiki na san ko kala nawa ne don ni na siyo, ko wane turare, sabulu, mai da duk abinda ke ciki nasan kamshin sa da adadin da zaiyi.
Ya fizgota na sanki da *Taurin kai* ki bada ko toothpaste ne kiga yanda zan *halaka ki da Wanda kika ba din*
Su goggo kowane ya zaro ido tare da hadiye wani dunkulallen miyau.
Ya kalli lubabatu dake bakin tabar ma *Ina ne take kwana?* ya daka mata tsawa. Ta tsira hannu *Gashi can*!
Ba tare da yayi magana ba cikin kattin wani ya yi ciki da jakar.
Ta kalleshi cike da takaici wannan mutum akwai wulakantacce ni zai kira *kazama*? Ji yanda yazo yana mun hayagaga har gidan mu ban tsira ba. Kai ohh ni umaimah na jefa kaina a jafa'i.
Ya kalleta sosai *Ki rufawa kanki asiri ki bi doka ta* ya juya kawai duk suka bi bayansa.
Ta bishi da harara ta wuce wurin wankin ta.
Lubabatu ta saki ajiyar zuciya, goggo jummai ta ce yau naga masifa, wannan matsiyaciyar yarinya zata janyo mana bala'i.
Kowa na tofa albarkacin bakin sa amma goggo hansatu ko motsi sai da luba ta lura sannan ta tabo ta *inna*..... Tayi firgigi ta ce *Wayyo mun shiga uku*....... Duk aka kwashe da dariya ta mike da gudu ta suri buta tayi kewaye.
Umaimah me zatayi ba dariya ba. Ta ce su goggo manya wannan 'yar barazanar ta firgitata da sune yake ma wujijjigawar da nakesha wataran mussai zasuyi. Ta kara tuntsirewa da dariya sai kawai ta ganta tsaye gabanta tana nishi idanu duk sun fito, kyayi dariya don ubanki hankalin ki ya kwanta ki kawo mana ajalinmu har gida.
Ta shiga bambami kowa ya dunga zagin umaimah.
Ta waigo goggo haka fa yake da wannan masifar ta babu gaira, saboda Allah luba bana tsafta idan zan tafi?
Duk suka kwalalo ido *Anya yarinyar nan bata tare da aljannu?* firar yau batayi tsawo ba kowa ya shige daki.
Sai goma saura ta gama tayi salloli, ta kura ma jakar ido gabanta ya fadi *Ohh ni umaimah*
Ta juya luba kinyi barci?
A a ido na biyu.
Au, kuma kikayi lamo? Tashi mu danyi fira bana jin barci wallahi.
Ta janyo jakar ta bude sai kawai ta dafe kirji *Na shiga uku* wasu irin kayana ta gani ta ce luba zo ki gani.
Mi? Tabb um um , sai kawai ta bata baya kada ma ta hango wani abin ya birgeta. Tayi murmushi ta dauka wasa takeyi sai ma tayi mata banza.
Duk sai taji babu dadi *wannan ai mugun hali ne* ta fada a hankali. Kiri kiri yazo ya firgita jama'a. Dogayen riguna masu kyau wasu matsattsu wasu budaddu, turaruka, Mayan shafa wani abin ma bata San ya ake amfani dashi ba,Gyaluluwa kai kaya barkatai , kunya ta kamata ganin brezias mtsew ta buga tsoki ta rufe jakar.
Luba dai na jinta tayi lamo.
*Madaki* kuwa suna fita yaji kamar ya koma ya dauko umaimah su tafi gida. Yarinyar nan tana wahala gidan can. Wanki hada na yara?
Amma mutanen nan akwai matsiyata, zasuci ubansu, ya kuta.
Sai na gama ci masu uwa sannan in dauketa in mayar da ita gidana zan fara nemo waye uban tukun shima dayan *shashashan*
Yayi dan murmushi Matsoratan banza duk sun rikice ganin bindiga. Sai na mayar dasu ma'aikatan ta a gidan *nasu wasa ne*
Da safe ta fito da shirin ta normal zata tafi , tayi karo da goggo lami, ta kalleta sama da kasa Sai kawai ta fizgota ta fara bugu, duk mutanen gidan suka fito lafiya?
Ta kallesu tana nishi Ku dubi duk gargadin da yarinyar nan tasha jiya a haka zata tafi. Kowa ya dauki salati nan suka yo kanta mai kulli nayi mai kwanya nayi, suka tasa ta a gaba tana ta kwalla har gaban jakar , goggo tasa hannu ta fiddo wata bakar riga tasha ado da duwatsu rigar ta yi kyau matuka da dan gyalenta karami, suka tsareta ta saka, sanan suka dauko turaruka suna feffesawa suna ci gaba da dankwasar ta *Shegiya mai kunnen kashi* baki gudun wahala baki gudar ma wani.
Ta kalli kanta ta kallesu tana kuka goggo haka zan fita da wannan dan mayafin in ratsa gari?........ Gam goggo hansatu ta buge bakin , wannan shegen bakin zai yi shiru ne? Idan ba da shi da uwaki zaki tafi?
Ta jefa mata wasu golden brown din takalma maza kisa ki tafi suka rufe jakar, duk tulin kayan babu wanda ma yabi ta kansu har su birgesu.
Karfe bakwai da rabi ta shigo tayi sama da gudu cikin bacin rai don kagare take ta iso gidan, yana kwance daki bisa gado yana ta sharar barci, haka kawai yau yaji barci kamar me,
Ta dunga bugun kofar da karfi ya tashi firgigi da jallabiya tunda ya dawo sallar asubah.
Ya kasa magana ya taso da sauri ya bude a hasale, yana ganin ta yayi turus yaja baya tayo kansa tana bala'i, me kake nufi dani ne, ya dunga baya baya tana binshi, ka firgita man iyaye ka rikitatsu ka kara jefa ni masifa, *Why are u increasing my problems?* ya zaro ido jin tayi turanci, yana kaiwa ta bango Sai ya daga hannuwan sa sama *am sorry* ta daki kirjin sa bazan yi ba wallahi na gaji da halayen ka ...... Ya ce, Ammmmm.... Ta kura mishi ido.
Kayan nan sun miki kyau. Ya bita da kallo tun daga sama har kasa yana dan murmushi, taja tsaki tare da juyawa ya fincikota ya maida ga bangon fuskarsa daf da tata ya sunkuyo, ya zaki tayar dani barci ki gudu ai yau muna nan.
Ta zaro ido..... Ya balla mata harara kilibabba an kwana tunanina zaki wani taho a 360 kina wani borin kunya.... Ya buge bakin zatayi magana naji ba haka bane kwalliya aka zo nuna mun in yaba ko?
Ta ture shi da karfi zata gudu ya maidota tabaya a jikin sa ya leko da kansa ta wuyanta, *Ke bakya godiya idan an miki abin arziki ko?* tsikar jikin ta ya tashi ta rasa in da zata sa kanta, ya lumshe ido yana shakar kamshin jikin ta.
Duk sukayi shiruuu kowa najin abin da yakeji a zuciya.
Shine mai karfin hali ya dan saketa amma Sai ya ruko hannunwan ta muje can kasan ya dan fizgeta..... Ta jiyo muryar mamee ta yi saurin turjewa ya kalleta *ya dai?*
Kai ni dai sakeni don Allah.
Ya kara fizgarta bazan saki ba haka zamu sauka sai kawai ta zukunne *Na tuba wallahi ga mamee can*!!!! ...... Shi ma ya zukunna kina jin kunyar ta ne?..........
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH
💑 *AUREN FARI* 💑
0⃣2⃣1⃣
https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH