← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 37

Sashe 22

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

........ Luba ta fara barci takai hannu luba tashi.
Ta murtsuke fuska ya akayi?
Ta fara bude leda tashi Musha..... Zumbur tayi, ashe ba ice cream kadai bane hada biscuit biscuit masu tsada da gasassar kaza.
Ta zaro ido ina kika sameshi?
Don Allah kedai kiyi shiru muci. Ta wuntsilo suna ci suna yar fira.
Ta mika mata tsohuwar wayar ta ungo na baki.
Ta kara fiddo idanu ke umaimah da gaske?
Na taba miki wasa? Allah na bar miki. Amma ina so karki fadawa kowa ga abinda muka ci yau. Ki debi biscuit din Wanda kike so saura kisa mun jaka ta.
Ta wawusa da sauri kai wallahi na gode. Amma umaimah waya canza miki waya? Zatayi magana kenan wayar tayi kara.
Ta ce *Ai fa na bani*
Luba ta bita da kallo.
Ta dauka hello. Malama da kika ji shiru ba sai ki kira ba?
Ta yi murmushi, ina gun baba ne zan kira. Kawai ta kashe.
Luba ta bita da kallo *Wanene*? Ke kyale shi ni nasan ma ko waye?
Madaki kuwa ya bi wayar sa da kallo cike da takaici *Haka zamuyi da yarinyar nan*? Ya mike tsaye *ni zata jama aji?*
Yana kira yaji wayar a kashe.
Kasusuwan luba taje can kasan bola ta tusa ledar. Sukayi kwanciyar su da kyar umaimah ta sami barci ya sace ta.
Zullumin zuwa gidan kawai takeyi, salon soyayyar madaki na bata tsoro gaskiya.
Shi kuwa tunda ya tashi yake faman zarya mamee na kula dashi tayi kamar bata san yanayi ba ko kalaci yakiyi gashi sai waya ake mishi office yaki tafiya.
Ransa ya baci matuka, ya zauna tare da dafe kai yayi shiru.... Goma saura ta shigo yana ganin ta ya mike kawai yayi sama.
Ta gayar da mamee tana ta sunne kai ta wuce ciki. Ta bita ta ido tana 'yar dariya *Wannan soyayya ni dai an mini kancal*
Ya sauko yana ta fushi mamee sai na dawo..... Ta kalleshi *Kalacin fa ko zaka aiko?* na koshi ya wuce, ta bishi da kallo.
Koda umaimah ta gama yan gyare gyaren ta sai tayi baya gurin su mansura.
Har ta tafi bai dawo ba.
Da daddare taci gayu ta ce zata je gidan Alhaji yakuba amma tayi tsaye zaure tana jiransa amma shiru ta fita waje tafi kusan awa daya amma bashi.
Duk sai ta shiga damuwa ta kwanta sukuku,
Washe gari karfe shidda yabar gidan, mamee ta rutsata daki tana janta da labari har ta dan saki.
Ni uwani kwanakin nan duk bana jin dadin yanda nake ganin ki ko kin fara gajiya dani?
A a mamah ta fada tana yar dariya,
Allah kuwa, sai nake gane kamar kin gaji dani in ba haka bane to ki saki jikin ki kamar farko. Kin ji ko?
Ta ce toh, tana murmushi,
Ta danyi shiru, uwani na daukeki tamkar 'yar da na haifa don haka ki saki jikin ki kada abinda ya shiga tsakanina da ke kinji?
Ta ce toh,
Idan kika ga mutum ya bata rai da ke ko ya ce kin mishi laifi kada kiyi girman kai ki bashi hakuri kinji?
Ta ce toh mamah kiyi hakuri. Tayi murmushi bani ba ina nufin abokan zama kinji? Ta ce toh.
Lallai mamee ta iya siyasa ta gama karto cewar *madaki* fushi yakeyi da umaimar. Duk da bata san dalilin Fushin ba,
zaman falo dai ya gagari umaimah yanzu saboda kunya , mamee na zaune ya shigo da sauri ya haye sama tayi saurin kwadawa umaimah kira ta zo da gudu saboda yanayin kiran.
Ta ce maza hau sama ki dauko mun kwalin ruwa. Ta ce to ta wuce domin tasan bai gidan.
Ta na hawa shi kuma zai sauko saura kadan su hade yayi baya da sauri, har zaiyi magana sai kuma ya fasa kawai ya raba ta ya wuce.
Ta bishi da kallo *Wai fushi yakeyi dani?*
Me na mishi? Sai kawai taji itama ranta ya baci.
Mamee na hangoshi ya taho tasan bai kula ta ba.
Gaban ta ya fadi ko uwani ba ta karbi soyayyar tasa bane.
Ita ma umaimar ta sauko rai a bace ta ajiye mata ruwan ta shige ciki. *Ikon Allah ta kame baki*
Ta rasa me ke mata dadi, duniya ta yi ta zumbure zumburen baki.
Mamee ta shige kewaye ta ringa dariya sosai.
Har bayan magriba umaimah taki tafiya gida,
Uwani yau bakya gudun dare? Mamee ta isketa daki zaune ta rabka uban tagumi,
Ta mike yanzu zan tafi cikina ne bana jin dadin sa, ta sumke dariya, assshhha cikin ne yau ma? Tayi shiru ta dauki hijab ta wuce kawai.
Tana zuwa gida ta bude waya ta tura mishi sako da turanci saboda bata iya rubutun Hausa ba,
*Pls what did I do?*
Ya na ganin message din ya tashi zumbur dama kishingide yake.
*good kin fahimci kinyi wani abu kenan*
Wani ya kara shigowa , *Sorry*
Ya bi wayar da kallo yana murmushi *naki wasa ne yarinya*
Tafi mintuna talatin rike da wayar amma bai maido amsa ba ta kara tura mishi:,
*I know whatever happened, Should not have happened the way it did, But, I am really sorry on my part, My intention was not this from the start, So please forgive me!*
Tsalle ya buga yana wani irin ihu. *Billahil azim ta kamu*
Ya koma ya kwanta *Sai kin fada da bakin ki yarinya*
Tayi shiru, kai jama'a wannan da me yayi kama nifa bana son yawan fushi. Anya zanji dadin zama da *madaki* a matsayin miji?
Ta yi saurin sauya zancen *tabb duniya akwai namijin da zai taba birgeni bayan shi?*
Ta kara tura mishi sako,

*Please forgive me for what I did, My intention was pure I admit, I did not want to hurt you a bit, I am really sorry for what I did!*
Ya kara tashi zaune yana kara kallon rubutun , yarinyar nan yaushe ta iya turanci haka?
Wani sakon ya shigo har kyarma yakeyi,
*Madaki , Things are not the same without your company, I am missing you a lot, and I told you sorry, Please forgive me and start a new chapter, This won't ever happen again!*
Ai sai yayi mutuwar zaune, motsi ya kasayi duk illahirin jikin sa kasala ne,
Da ta kara jin shiru sai kawai kwalla suka zubo mata ta kashe wayar,
Lokacin da hankalin sa ya dawo sai kawai ya nemi kiranta yaji *Switched off*
Ya dora hannu aka ya ce *na gama banuwa*......Ya ziri makulli kamar mahaukaci ya fito, yana zuwa falo agogo na bugawa karfe sha biyun dare, ya koma da karfi bayansa ya daki bango ya runtse ido cikin wani irin radadi.
Dukkansu babu Wanda ya sami damar runtsawa,
Karfe shidda tayi sammako, shi kuwa tun biyar ya gama shiri ko da ya fito sallar asubah bai shiga ciki ba yana zaune bisa dan dakalin kofar shiga.
Daga nesa ta hangoshi zaune, Sam baiyi tsammanin ta ba yasan zata kai takwas zuwa tara, kansa duke yana lazimi ta iso,
Yaga alamun tsayuwar mutum ya dago da sauri , Ta rike kugu idanun ta sun kawo ruwa *Wai me na maka?*
Saura kadan dariya ta kufce mishi. Ya sha mur *laifi*
*bana baka hakuri ba?*
Ya dan dukar da akai don gaf yake da ya kwafsa,
Yaushe?
Tayi shiru tana kokarin maida kwallan bata so su zubo kafin ta ce, jiya na maka text.
Ya tabe baki ya dan watsa hannuwa ban gani ba.
Meye kika ce a text din?
Ta fiddo waya a hasale ta budo page din *Duk gashi* duba gashi kuma yaje na tabbatar tana faman scrolling.
Ya kyalkyace da dariya. Ta bishi da kallo nan da nan ta tsargu kunya duk ta baibayeta ta balla mishi harara ta wuce ya janyo ta ta fada jikin sa.
Lallai ana kauna ta *kut*
Ta fara kokarin zamewa ya ce *ke kilibabba* dadi na san zai halaka ki ne abinda kikayi missing kenan duk kin rikice.
Ya kamo hannun ta zo muje in baki labari nima ai na wahala....ya rike hannun ta sukayi ciki yana dariya. Suna shiga ya tarar da mamee zaune tayi tayi ta fizge ya riketa gam,
Ta yi sukutii... Kamar da gaske sai mamee tasha mur *ina zaka je da ita?*
Ya jata da karfi zasu wuce ya ce gyara zata mun sama.
Ta daka mishi tsawa zaka saketa ko kuwa?
Bana hanaka yi mata wannan zillar ba? Har yaushe zaka kyale yarinyar nan ta sarara?
Uwani wuce ciki daga yau na sa miki doka baki kara hawa sama...........

😃😃😃😃

*maman Abdallah* 😘😘😘😘
[1/26, 10:10 AM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 AUREN FARI 💑

0⃣2⃣4⃣

DAFATAN ZAKU SAKA TA ADDU'A AKODA YAUSHE HAJIYA RABI BADAWI MAMAN IBRAHIM DA NURY
Chapter 22 · 0% Book details