← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 37

Sashe 24

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fi mintuna ashirin bai ce qala ba kafin Ya dago kai yana murmushi, ko alokacin jahiliyya ranka shi dade ban taba jin anyi haka ba. Hasali ma idan son yarinyar kakeyi kaine zaka tarar da iyayenta komin kudin ka komin mulkin ka ba iyayen yarinyar zasu kawo kansu ba kamar yanda mukayi yanzu. Aure rahama ne yana daya daga cikin dokokin Allah da manzon sa cewar a girmama aure a kuma daratta shi, umaimah marainiya ce ni na saki nono mahaifin ta ya kama. Wallahi matukar nayi mata haka ba la'antar Allah kadai ba tsinuwar dangi da mutanen gari bazasu taba sanya ni in zauna lafiya ba. Amma ina mai baka hakuri idan abin da na fada bai ma dai dai ba. Ya juya Allah shi gafarta malam ga maganata akwai gyara? Ba liman yayi magana ba *madaki* ne yayi Hakika babu gyara ga maganar ka baba. Kuma naji dadin maganganun ka . kafin in sanar da kai dalilina ina son ka amsa mun tambayoyi biyu zuwa uku, Na farko me yasa kabar gidan ka sakaka babu kula?, ya akayi duk yaranka na makaranta banda umaimah?, sannan minene ka gwammace tabi gidaje aiki akan zaman gida bata aikin komai. Saboda ko kafin umaimah ta fara aiki gidana ta dade da fara bauta gidajen unguwar mu? Yayi shiruuuu.... Kafin ya nisa, idan ma na boye muku to bazan boyewa mahalicci na ba. Na farko ina iya kacin bakin kokarina a kan gida matsala daya aka sami da na karo mata ta uku shine cin mutunci ya fara shiga har matan nawa suna zagina ko su sanya 'ya'yansu manya su nemi sa'in sa dani. Sai na yanke shawarar idan na fita kasuwa tun bayan fitowata sallar asubah sai talatainin dare sannan zan dawo. Umaimah kuwa, gaba daya daukota ma da nayi shi ne ya kara jagula duk wata matsala, ko na fita na barta zata tafi makaranta to bata zuwa, tsinke wannan idan na siyo da sunan ta tabbas ranar na janyo mata masifa da ni kaina shi yasa na tattara na watsar. Aiki gidaje kuwa shi ne in da tafi ko ina samun natsuwa, zata ci zata sha zasu bata tsumma ta daura. Wannan shine dalilina na barinta tana yi don kada yunwa ta kassarata. Ya juya gun su liman Malam kunji da kunnen Ku? Hakika munji yallabai. Suka fada. Ya ce good, Baba, kayi hakuri amma maganar gaskiya dalilin da yasa na kiraka anan shine da ka kuskura an daura Aure na da umaimah wallahi da sai na sa an daureka don ka tabbata baka San *Hakkin Dan Adam* ba, idan kuma baka amince ba to shi yasa na kira malamai don kamar yanda na ji bayanin ka na tabbatar akwai rashi ko karancin ilimi sai Suyi maka wa'azi. Ina Neman afuwar ka baba....... Ya sunkuyar da kai haba haba babu komai, babu komai. Liman yayi gyaran murya, to Alhamdulillah, shi musulunci sauki gareshi kuma Aure kamar yanda ka fada ne babba. Namiji ga gidan sa shi *Linzami* ne, shi yasa Allah SWA ya ce *ARRIJALU QAWWAMUNA ALAN NISA'I....* a wurin Allah wannan ba hujja ba ce, Suka fara mishi wa'azi daki daki hakkin iyali, hukuncin Wanda ya zalunci maraya da sauran wa'azi. Iyakar kunya malam bawa yaji ta, sannan ya tausaya ma kansa akan saken da yayi. Ya sallami su liman sanna ya ce wadannan kudin baba ka dauki dauri biyu ka ba aminin ka daya, Ku kara jari. Zamu je da kai can gida kaga inda umaimar take domin hankalin ka ya kwanta....... Babu damuwa. Malam nasidi ya ce nikam zan koma rumfa mun baro yaro marar wayau. Mansurah ta dunga tuntsurar dariyar keta, Wai ke ya akayi ne? Sai da tayi mai isarta sannan ta fada masu. Bilki ta zaro ido anya kina cikin hankalin ki kuwa? Kin manta duka gidan ko ina akwai kamara da yallabai ke ganin komai? Kina tunanin zaiyi shiru bazai bincika ba?..... Bata rufe baki ba mansura ta baza da gudu tana zuwa ta tarar da kawar khausar ita kadai, daman ta wuto su a kitchen. Ta ce kije inji khausar tana fita tayi saurin bude jakar ta mayar da kayan dai dai lokacin da dayar ta fito toilet. Tayi waje da Sauri, ta bita da kallo cikin tsarguwa. Suka fara mata dariyar har taji babu dadi, ke kin fiye sauri irin gidan nan an fada miki haka kawai zaka bigi gaba kayi tuggu? Ko kuwa duk wannan feleken da daukakar da uwani ta samu an fada miki haka kawai ta shigo zikau bata shirya ba? Bilky cikin dariya ta ce, ai idan baki fitar da ita ba ke kya fita saurin me kikeyi? Suna gama cin abincin suka tafi. Ita kuma ta kabbara sallah, raka'ar karshe mamee ta fara kwala mata kira, tana karasawa ko addu'a batayi ba ta ruga sanye da hijab din mamin domin ita da gyale tazo, Gani mamah, Aunty murja ta kalleta Tun daga sama har kasa *Ina kika sami gadararriyar yar aiki?* Aunty jamila ta yamutsa fuska, yaya mai mutane.... Saboda samun wuri yar aikin ce da hijab dinki? Ashe jita jitan da mukeji da gaske ne tabdi. Lallai zamu kowa Aunty yaya da bayani....... Au har kunji labarin uwanin? Kwarai kuwa ance ta raina kowa ke da madaki ma tsoron ta kukeyi to........ What? Aunty jamila kuna hauka ne?...... Mamee ta daga mishi hannu. Sam bata yarda ya raina mata yan uwa ko Kadan. Babu Wanda yaga shigowar sa. Sukayi sukutiii don tsoron sa sukeyi kamar me. Baba bisimillah ya daga murya. Umaimah ta zaro ido baba ta tareshi tana yar dariya. Mamee ta kalleshi alamar tambaya *Baban ta ne* ya fada tare da zama bisa kujera. Mamee ta washe baki kai maraba maraba. Ya nuna mishi kujera ya dago suka hada ido da aunty murja, kawai ta mike ita ma jamilar tabi bayanta. Munafukan banza ya fada cikin rai. Bayan gaisuwa da mutunta juna. Mamee ta kalli sadauki wallahi kayi kokari kayi Kyan kai. Wanin uwani bai taba zuwa gidan nan ba. Ta mike tsaye sannu baba. Mamee zama zakiyi na sameshi ne akan umaimah ta zauna anan zuwa bayan sallah kada zaryar tayi mata yawa ga azumi. Mamee ta fadada fara'ar to ya amince da hakan? Umaimah dake kusa dashi ta taunkulo cinyar sa tare da girgiza mishi kai wai yace A'a . sai ya kwashe da dariya ya kai mata duka aka, kaniyar ki da mintsili na....... Mintsili????? Me zasuyi ba dariya ba. Wallahi mintsili na tayi wai in ce A'a. Mamee ta kasa magana don dariya, madaki ya kalleta *Yanzu baban kike mintsili?* ta zumburo baki ta noke kai, Uwani hoo, mamee ta fada Ba zaki zauna ba kenan? Baba ya amince kyaleta mamee ita tana tausayin kanta ne? Ta bishi da harara, Inji waye uwani zaki zauna ko kuwa...... Haba hajiya shawara za ayi da ita? Ya mike tayi zamanta can din me takeyi daman ai barci ne kawai ke maida ta. *Madaki* ya buga kafa *Good papa* mamee ta baka mishi harara. Malam bawa dai kansa kasa yana ta murmushi. Su Aunty murja na labe, anya wurin can babu alamar tambaya? Hmmm ai muna ganin ikon Allah ni jamila. Ya mike zan tafi Allah ya kara arziki. Ta mike ai nima lokacin tafiya ta yayi gobe na dawo da kayana duka, Madaki zaiyi magana mamee ta daga mishi hannu dole yanaji yana gani tabi baban ta. Suna zuwa suka tarar da himilin kayan abinci buhu buhu da jarkunan mai banda kayan shayi ba abinda babu. Matan suka tare shi, suna mishi bayani. Ya ce eh na san dasu daga gidan aikin umaimah ne suka bamu zakka...... Ya wuce ciki. Umaimar ce ta tsaya yi musu bayanin gidan zatayi azumi. Luba kuwa ta dunga kuka saboda dan kurmusun da sukeyi cikin dare. A gidan Alhaji yakuba tayi sallar magriba. Ba karamin dadi taji ba amma har yau kunya ta hana umaimah fada mata cewar madaki na son ta. Tana gidan ya kirata a waya yana jiranta a mota. Bata yarda hajiyar ta ga wayar ba tana soke cikin zane, lokacin da ya kira kuma ta dan fita, ta ce zata koma gida ta shirya kaya. Ta fiddo mata sunkunan ta ta ce ungo tafi da su. Yana hangota ya fito tare da bude mata kofar mota, *Barka da isowa ranki shi dade* ta dan bata fuska *Ya kake*? Yayi murmushi ya rufe yana shiga ya ce lafiya garas tunda gani gabanki. Ta ce *Good*....... Malama wai lafiya kike wani basarwa ko nayi wani laifin ne? Ta girgiza kai ko daya naga dai *Kaima haka kake wulakanci da rai* idan ana baka girma..... Dariya yakeyi har yana kwanciya, *Kai umaimah ke karshe ce* watan wulakanci nake da rai. Tayi murmushi eh mana suyi ta kyarma suna tsoron ka....... Ya kara yin dariya ai ke bakya tsoro na ko? Tayi yar dariya Allah ina tsoron ka..... Ko maganar ka naji sai gabana ya fadi. Ki ce Allah! Allah kuwa, Tabb wallahi nima haka, Ta kalleshi da sauri yayi murmushi, da gaske nake wallahi dana tunkaro gida sai gabana yayi ta faduwa. More especially idan fararen kaya ne jikina, a office wani lokacin har zabura nakeyi ina firgita idan na tuno masifar ki. Ba wani nan, kullum kai ne ke tokala ta, Ai matsalar da na ganki sai inji kawai mu kafsa, saboda ko gardama ba'a taba yi dani ba ko bakiga yanda nake *wulakanci da rai ba*? Tayi yar dariya na gani kuwa. Ya kai mata duka,...... Da an canza ma suna yau. Ai nasan hannunka sai ya taba ni. Ya tuntsire da dariya kin San kuwa dana fara son ki burina kawai mu hadu kina bala'i ni kuma ina rungumrki......laaaaaa ta ce tana hararar sa. Meye kika kawo mun a leda? Ba komai dun kuna ne...... Allah? Cewa zakiyi gayu zan sha, ta dan harareshi *Wai ma*...... Wayar sa ta fara ringing ya duba kamar ba zai dauka ba ta tsareshi da ido, yana dagawa ya saisaita murya kamar bashi ne ne raha yanzu ba. Hellooo..... Lafiya, zan kiraki zuwa anjima ya kashe wayar.... Umaimah ta bude marfin mota yayi saurin fizgota ke ina zuwa? Ta murtuke fuska zan baka wuri ne don ka sami halin kiran nata ba ma
Chapter 24 · 0% Book details