← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 37

Sashe 18

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

...... Kayi hakuri ledojin ne sukayi mun yawa shine naga meye amfanin jakar....
Ya finciko ta baki fahimci me nace ba? Kin San kudin jakar nan kika sako mata wannan tarkacen?
Ya girgizata *dubu dari biyu da hamsin* Ta zaro ido na shiga uku, ta zazzage kayan da sukayi ragowa tana kyarma, *dubu dari biyu da hamsin* kudin kawai take maimaitawa duk ta gigice sai kawai ya rungume hannu yana kallon ta cike da takaici,
Tabar jakar nan ta shiga kwashe kayan tana kaiwa kitchen, sannan ta dawo ta dauki jakar tana dan sayar kallon sa,
Ta tarar komai an hada mata har dankalin an fere, ta shiga hadawa,
Koda ta gama ta kawo musu bisa table bata tsaya ba sai tayi ciki. Ya bita da kallo, *yarinyar nan muguwar bagidajiya ce mtseww*
Mamee ta kalleshi cike da kulawa lafiya?
Ya ce ba komai,
Ta zuba faten zata fara sha, ya kalleta
Meye ke kamshi haka?
Faten dankali ko zaka sha?
Ya danyi jimm, eh kamar hakan.
Tayi murmushi kilibabbe,
Wasa wasa sai da ya share plate biyu, a lomar karshe ya kalleta mamee dama shi kika mun tayi last time na bar dadi haka?
Tayi yar dariya au kajiye ma bakin ka kenan.
Gaskiya ya mun dadi ayi. 'Yan aikin nan naki na bada wuta kwanannan.
Na lura masu kalacin safe sunfi sauran iya abinci fa, last week ma na ci wani Dan bread da SOS ya mun dadi a office kamar na kuma waya.
Ai uwani na kokari kam don yanzu kalaci inba ita ta hada mun ba bana jin dadin sa saboda yan makulashen nan.
Uwani? Ya bukata,
Uwani fa ai karambanin ta ya wuce inda duk kake tunani, duk abinda ta ga wani yayi sai ta kwatanta.
Ga tambaya, ai tana da kwalwa.
Lallai idan akwai saura zanci da dare a ajiye mun.
Ta kalleshi da sauri *a ajiye ma Kana nufin a *dumama*? Yayi murmishi haka na ce mamee,
Umaimah kuwa tana baya ta debo uban *klin* ta zuba a katuwar roba tana ta gurzar jaka, mamee ta kwala mata kira,
Ta antayo da gudu hannun ta duk kumfa,
Ya bita da kallo duk ta jike hijab dinta,
Naga hannunki kumfa me kikeyi agogo? Mamee ta bukata tana kallon ta cike da kulawa.
Tadan murza hannun kumfan ya fado kasa tana satar kallon sa, jaka nake wankewa...... Ya dago *what a ruwa kika saka ta?*
Mamee yar nan taki wallahi duk abinda nayi mata kar kiyi magana.
*Da tayi maka me?*
Ki tambayeta gata nan, ya nuna ta da yatsa,
Uwani me kika mishi?
Ta dan kara kame jikin ta tana dan in ina....... Uwani matso nan saki jikin ki. Ta kalleshi wallahi bani son takurawa yarinyar nan da kake yi madaki tsoron ka takeyi kamar me dubi yanda jikin ta duk ya rikice da kyarma ina dalilin wannan azaba?
Ta kamota me kikayi mishi?
Jiya ne ya ban jaka ban san cewar mai tsada bace shine....... Ki faro mata daga farko.... Ya katseta.
Kai bana son shiga uku kai ka fada man mana.
Mamee yarinyar jiya zan tafi stadium na hadu da ita hanya zata je gida na taimaka mata na rage mata hanya na ganta da kudi a hannu na ce bata sawa jaka ta ce bata da ita, na biya na siya mata mai tsada shine yau ta yo cefane da ita duk kifi da karikitan data siyo ciki ta zubo shine......... Shine me?
Ina ruwanka idan wuta ta saka ta Ina ce kai dai ka bata ko?, zai yi magana ta daga mishi hannu kai bani son rashin gaskiya, daman ka siya ne don ka uzzura mata, duk tsadar ta ina ita zata san haka?
Ta kalleta kin rage dan faten? A a duka na juyo shi sai Wanda na diba a plate...... Sai ki ajiye mun shi kar ki taba.
Mamee ta bishi da kallon takaici,
Ko bakiji ba? Ta ce to zata juya, mamee ta kamota je ki ci fita batun sa,..... Haba mamee ....... Zakayi mata kurulla ne?
Sai kawai ya mike ya nufi kitchen din ya dauko. Wai madaki meke damunka?
Ai mamee idan na zauna gidan nan wata rana ma cewa zakiyi ba ki haifeni ba sai uwani ya wuce sama da plate din.
Ungo wannan je karasa cinyewa kyaleshi. Kullum ganin kansa yakeyi yaro karami shi yasa nake burin yayi *Aure* gaban umaimah ya fadi *wai ya zanyi naga madaki da wata?*
Tayi ciki tana karasa wanke jakar,
Ta ringa jiyo hayaniyar mutane, ta sami mamee daki ta ce, kamar baki nakeji falo.
Wannan fitinannen ke meeting ai shirin zuwan su ne jiya na wuni baya ina gargadin su mansurah, manya manyan manajojin sa ne,
Au, ta fada a takaice.
Firatan ya ki hawa sama duk ya takura kowa.
Madaki kuwa yasan yau wuni zaiyi tare dasu gashi baya son umaimah ta tafi bai sani akwai maganar da zaiyi da ita.
Karfe uku aka fara shirya musu abinci kamar yanda ya tsara, umaimah an dage aiki baji ba gani, magana yakeyi amma hankalin sa na gunta idan ya hangota ta fito.
Ashe shima cikin manajojin shi daya ya hangota nan da nan hanakalin sa ya dauku. Ya dan juyo yana sosa keya,
'Yallabai ni fa na hango iri.
Ya maida hankalin sa gareshi sosai saboda shine babban manager da yake ji dashi a Lagos yake,
Iri na me?
Dai dai ta fito ya ce waccen yarinyar....... Ya sha mur *Bana son maganar banza* abinda ya kawo ka kenan?
Nan da nan ya kame kansa saboda suna bala'in tsoron sa.
Suka tafi zuwa dining, Sun fara cin abinci kenan sai gata da tray an nado kaji gasassu. Rashin sani ta ajiye gaban manager ya dago kai tare da dan murmushi ita ma ta mayar mishi, ya ce sannu....... Wata fizga yayi mata sukayi ciki ya kaita har kofar dakin mamee ya ingizata *wallahi kika kara fitowa sai na bata miki rai* ya juya.
Ta bishi da kallon takaici, su manager na ganin haka jikin kowa yayi la'asar ya dawo yanata mazurai ya nuna ma kowa plate *serve your self*
Kowa sukuku ana ci ana tattaunawa. Yana sauraron kowa yana kurbar lemu yaki cin komai.
Umaimah kuwa tana shiga ta ce mamah mun gama bari na dan huta , suka fara fira,
Bayan sunyi sallah suka dauko gyada mai bawo soyayya data siyo kasuwa ta juyo ta a tray suna ci.
Gashi an rufe kofar baya ya ce kada Wanda ya bude, ga shidda ta wuce tana son tafiya gida, ta rasa yanda zatayi. Kamar mamee ta karance ta, Uwani yau ko fira za a mun naga baki fara wannan saurin naki ba gudu gudu.
Ta danyi murmushi, na ga har yanzu suna falo kada ya ce ina mishi sintiri.... Ke kama hanya ki tafi gida kinji gobe kin san akwai lesson kuma na safe.
Taji wani kwarin guywa ta fito simi simi *ya daka mata tsawa bana ce karki fito*.......tayi baya guje
Mamee ta ganta kamar an jefo ta. Ke lafiya waya biyoki?
Tayi shiru tana kallon kofa.
Ya mike tsaye, kowa na iya tafiya gobe ma karasa by 8:00am. Yana gama fada ya haye sama da sauri.
Mamee ta ce muje ta taso ta a gaba. Ba kowa falon umaimah tayi turus.
Kama hanya ki tafi gida yanzu kyaji kiran sallah.
Ta ringa hada kafafu don sauri gudu gudu ta fito tana rufo kofa taga mutum tsaye.
Ya figeta sukayi wata hanya, me yasa ke kullum kin fi so kiga ina miki hayagaga?
Ta sunkuyar da kai.
Ya bita da kallo wai yarinyar nan yanzu bata biye mun?
Da ke nake magana . tayi shiru, idan kika kara fitowa nayi baki sai ranki ya baci daga yau.
Ta ce toh a hankali. Ya kalleta sosai, ko bakiji ba?
Naji, ta ce kanta a kasa.
Ya dan saketa ga jakar ki can da kika ki karba ta tsaraba na ce maikudi ya kaiki gida kije yana jiranki...... Ta kalleshi da sauri maikudi drivern sa da baya tuka kowa?
Ta girgiza kai bana shiga.
Dalili?
Haka nan,
Idan na ce dole fa?
Malam bafa zan shiga motar ka ba, kawai sai aga cewar waccen motar ta ajiyeni wane kallo za ayi mani?
Zai kara magana ta hada hannuwa don Allah ka kyaleni haka nan na kai makura..... Har jakar bazaki dauka ba?
Ko na karba zan raba ka da su ne ba tare da nima na amfana dasu ba to meye amfamin amsar?
Ya kalleta har zaiyi magana ya ingijeta ya wuce....
Ta bishi da kallo ohh wannan akwai bahagon mutum ta wuce tana yan tunane tunane.
Ya wuce masallaci yana magana kasa kasa cikin fada, gidan nasu zan je in kyare masu warning duk shegen da ya yi amfani da kayan inci uwashi. Ai na karanci matsiyata tun jiya.......

*Mukwana lafiya*

😘😘😘😘😘😘😘😘
[1/26, 9:18 AM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣2⃣0⃣
Chapter 18 · 0% Book details