Sashe 27
Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
*Maman Abdallah*
😘😘😘😘😘😘😘😘
Na gode da addu'o'in Ku.
Aunty rabi na godiya matuka🤝🏼😘
[1/27, 7:42 AM] +234 806 091 7227: 💑 *AUREN FARI* 💑
0⃣2⃣7⃣
*Abincin wani gubar wani ina rokon duk Wanda labarin nan bai mishi ba don girman Allah kada a karanta don Anyi shi ne kawai don ilimantarwa da nishadantar wa, duk wani marubuci mai hikima yana kokarin fiddo abinda ya zama ruwan dare a rayuwa ya misaltashi kafin ya nuna illar sa. Maganar runguma da akeyi ai gashi nan a universities 'yayan hausawan mu suna chudanya da maza rike hannu da rungumar basu daukeshi bakin komai ba, mafi yawa kuma sakacin iyaye ne, saboda haka ina sane da abinda nake rubutawa a daina sauri ana zarbabi, masoyana kuma ku sani labarin AUREN FARI wallahi na rubuta shi don girman SOYAYYA saboda haka ni bani raina masoyina duk in da yake kuma ko yaya yake. Ku sani nafi kaunar ku fiye da yanda kuke son labarin AUREN FARI wallahi, Allah yabar so da yarda. Kada a manta don HAJIYA RABI BADAWI MAMAN IBRAHIM DA NURY na rubuta AUREN FARI da duk daukacin masoyana.*
...... Ya kalleta ta kalleshi, suka kwashe da dariya, ni ban taba kwanan zaune ba yau gashi ka janyo mun,
Mamee ta fito, me zatayi ba salati ba, anan kuke zaune har assalatu?
Umaimah ta buga hamma,
Ya kalli mamee to tunda kin sa mun ido zanyi mussai a cikin gida ba dole ni in shawo kan abata ba,
Ta wurga mishi harara, mamee tayi yar dariya au ka bayar da hakurin?
Dole na ma,
Kuma shine ka tsare mun 'ya har assalatu, duk kuna cewa me?
Ohh yauni na shigesu da mamee fira mukeyi da begen juna ko bakiga kwanakin da muka kwashe ba tana gudu na,
Ya mike samira zata janyo mun ko ma in ce ta janyo mun bala'i.
Au wai duk fitinar akan samira ce?
Dai dai ya zauna bisa dining wallahi mamee ita ce daga *Hugging* yarinyar nan ta birkice mun,
Da kyau......mameee ta fada itama lokacin tana zama.
Uwani taso muyi sahur kike ta hamma daga zaune,
Da kyau fa kika ce mamee,
Eh mana, ta mun dai dai kaga yanzu sai ka fahimci abinda kake aikatawa bashi da kyau lokacin da nake fada ma dariya ma na baka irin ban waye ba to yanzu kaga wayewa zata bi da kai don da alama uwani ba sakarkarun matan nan bane...
Ya bata fuska, mamee ban tunanin gidan nan zaki taba ganin laifin yarinyar nan, maimakon kiyi mata fada ta sanyawa ranta hakuri ki kwatanta mata yanayin huldodina da mutanena shine zaki kara zuga ta?
Akan me?, ko kadan wallahi, huldodin banza sai aka ce hulda dole da mata za ayi ka kamo hannun waccen ka riko waccen.?
Mameee......... Haba wannan wace irin shaidata ce kin mayar dani magnet.
Ai na daina ko sunan mace bana son ji yanzu,
Ta tuntsure da dariya, da sauranka yaro.
Umaimah na gama hada musu ta dauki nata tayi ciki yayi kiran duniya ko waige, da basu yi haka ba kamota zaiyi ya bita da kallon takaici, duba kiga abinda takeyi man mamee tana jina tayi shiru in rikota yau in wuni cikin azaba........ Kaii ni *madaki* naga ta kaina.
Me mamee zatayi ba dariya ba. Ai uwani na birgeni wallahi ka sami mata dai dai da halinka. Saboda duk wacce ka aura tana jin tsoronka ko tana binka saboda dukiyar ka bazata taba fada ma gaskiya ba, bazaka taba gane kayi kuskure ba haka zalika baza ka taba gane rayuwar aure ba har abada.
Amma a yanzu uwani ta fara bi dakai hanya.......haba mamee,
Tayi yar dariya na yi karya ne?
Zaiyi magana canza zancen, jiya *Yaya ta kirani*
Watan babbar yayarsu ta Kaduna,
Ya bata fuska su Aunty jamila sun kai mata gulma ko?
Madaki..... Ka dubi girman Allah ka daratta yan uwana bana son kana nuna masu ko ka shiga maganar da ba taka ba. Ya ajiye spoon shi kenan na daina in shaa Allah.
Me ta ce miki?
Tambayata takeyi da gaske ka sami mata cikin yan aiki?
Na ce mata eh amma ba yar aiki ba ce.
Kika bata bakin ki? Sai ki bita da eh,tana da abinyi ne?
Mamee na fama da yan uwanta, yaya ta kaduna ita ce babba sai ita mamee din sannan anty jamila da aunty murja, Aunty jamila ita ce munafuka duk wani motsi da mamee zatayi ita ce ke kwarmata wa sauran.
Mijin yaya yafi madaki kudi nesa ba kusa ba. Amma idan sabga ta tashi mamee ce dawainiyar su da komai, basa tausayin ta ko kadan, yaya bata wata bata fita wata kasa ba, amma ko sabulu bata taba kawo wa mamee ba da sunan tsaraba.
Mamee kuwa da yake tafiye tafiyen bai dameta ba sai kamar ko umara daga can su biya kasa daya ko biyu, haka zata bi su da kayayyaki designers su da ya'yen su, idan sallah ta tashi haka zata dunke 'yayansu da tsadaddun kaya. Ta aika mota a dauko su tela ya auna su.
Amma sai yayar ta ce ana ma yaranta dunkin banza a ringa kawo mata suna badawa dunki.
Kullum dadi sukeji madaki yaki aure har suna gulmar koda kudi ba sai da farin jini ba?
Jin ya sami mata yar aiki kuma yanzu surutu ya karu.
Ya riko hannunta, mamee ki kwantar da hankalinki kada duk abinda zasuyi ya dameki.
Ko kadan kawai ina takaicin uwa daya uba daya amma bakinciki ya shiga zumunci da jin zafi.
Cuta ce mamee, hassada sukeyi miki kuma sune a kasa kada ki fasa kyautata masu, kullum ina fada miki daga naira daya zuwa miliyan dubu mamee kada kiji shakkar tambayata koda kina sha'awar kawai in baki kisa masu wuta.
Tayi yar dariya Allah yayi Maka albarka umar, Allah ya kara maka arziki mai amfani kaima ya baka yaran da zasu ji kanka su tausaya maka su kula ka kamar yanda kayi mani.
Aamminnnn mamee, amin.
Ina so daman muyi magana,
Tsakanin ki da Allah mamee Umaimah ta miki? I mean uwani,
Tayi murmushi, kwarai kuwa, hasali ma ni uwani tayi wa kafin tayi maka......ya kyalkyace da dariya na sani.
Ina maganar fa AURE. Ta daga kai tabbas kuwa ta yi mani wallahi bani da matsala ko kadan da uwani, yarinya ce mai hankali, barkwanci, girmama na gaba da ita, tausayi, bata da kwadayi uwani bata sata, na auna yarinyar nan yafi sau dari amma wallahi daga baya ma sai da na ji kunya,
Yanda duk baka tunani ina son uwani ummaru.
Ya fadada fara'ar sa to ina son kiyi man alfarma in je in nemo auren ta a daura mana aure ranar sallah.
Ta zaro ido baiyi sauri ba? Karatun ta fa?
Duk ina sane dashi wallahi wallahi bazan taba hanata karatu ba mamee ko PHD take son yi zan kyaleta amma aiki ne bazatayi ba.
Maganar sauri kuma zanje Abuja muyi magana da baba Lawal da baba Nura sune zasu sanar da sauran.
Zan biya Kaduna da kaina na fadawa...... A a ita dai ka bari na fada masu.
Amma ka fara tuntubar uwanin kuyi shawara sannn.....mamee rigimar yarinyar nan nake tsoro kada ta birkice mun kuma,
Dariya mamee keyi hada kwalla wai yau *Madaki* ke Shakkar wani abu a rayuwar sa,
Yayi murmushi, Allah kuwa rigimammiya ce.
To kasan abinda za ayi?
Ka je kuyi magana da mahaifin ta komi ya ce shi kenan...... Haka za ayi ya fiddo waya,
Kai bani son hauka.....amma ina har ta fara ringing, ya ce to ai yanzu yana sallame sallah zai fita gara in fada mishi ya jira in zo.
Hakan kuwa akayi.
Yana dawowa sallah ya shirya kawai ya fi ce,
Umaimah kuwa tana sallame sallah itama ta kudundune a bargo, mamee na shigowa ta tarar da ita, sai kawai ta rage mata A.C ta ja mata dakin ta koma falo.
Malam bawa ya share zaure da kansa ya shinfida tabar ma yana jiran Madaki.
Shi kadai yazo, bayan sun gaisa yana ta tsumayen yau kuma da me yazo?
Ya dan yi jimm, baba adaiyi hakuri don Allah...
Haba haba wallahi babu komai in ce dai lafiya?
To kusan lafiyar dai zance, wallahi wata alfarma na zo nema da kuma shawarar ka,
Ya kalleshi a mamaki yallabai tami kuma?
A gaskiya baba ina son umaimah kuma so na aure hasali ma idan za a taimaka man baba ina son auren kada ya wuce sallar nan idan muna da rabon kaiwa.
Yadan yi shiru, jin malam bawa bai ce komai ba ya ci gaba da cewa,
Wallahi bana son ko tsinke naku na yafe ita kadai nake so ku bani sannan zan dauki duk wata dawainiya ta bangaren ku.
Wannan ita ce alfarmar da nake nema, shawara kuma,
Ina zullumin kada umaimar taki amincewa don yanzu haka na sanya ta karatu tanayi kuma na yi alkawarin wallahi zan barta ta karasa duk inda take son kaiwa a matakin karatu. Shin in sanar da ita ko inyi shiru?
Ya dan yi shiruuuu!!....
Ya langabe baba don Girman Allah ka taimaka man.
Haba yallabai, babu abinda zaka roka in hanaka, matsalar ina da yan uwa kauye zan so na sahawar...... Idan har kana ganin babu damuwa na amince mu je yau ka gabatar dani. Kafin iyayena su koma.
Ya danyi murmushi yallabai hakanan zaka wahalar da kanka in shaa Allah zan je da kaina.
Baba kayi hakuri don Allah ..... To shi kenan bari na shiga na fito kada rana tayi mana hanyar bata da kyau.
To baba maganar umaimah fa in fada mata?
Rabu da ja'ira ni zan mata magana da kaina don kada ta ga laifin ka tunda har kana da tabbacin zata iya birkicewa.... Ya shige gida in ba iyeshe na yaran yanzu ba ita har tana da abinda yafi auren a wannan maraicin nata?
Sai biyu da rabi suka dawo, Madaki na ta murna yanda aka tarbeshi kai wadannan mutane da mutunci suke,
Shima malam bawa yana ta jin dadin yanda madakin ya saki jiki kuma ya girmama yan uwansa ba tare da raini ko nuna kyama ma.
Suna zaune falo ita da mamee ya shigo yayi lilis don gajiya, mamee ta kalleshi yanda ya zauna da kyar,
Wash wallahi na gaji mistake daya nayi da na tuka mota yau.
Ke baki iya cewa sannu da zuwa darling?
Mamee ta harareshi ka dawo zaka sa miyon bakina kafewa ina ka tafi yau wayar ka ma bata samuwa?
Bari mamee wallahi mutanen nan na dade ban ga masu mutuncin su ba, mota ta nacen cike da buhunnan wake da aka bani.
Nan da nan mamee ta dago shi ta kalli umaimah uwani jeki karasa man gyaran durowar kinji....... Kiyi sauri danayi sallah zamuyi zance.
Ta yi ciki tana dariya mamee ta bishi da harara, ina sauraron ka ni ra sa kunya.....
Ya kwashe duk yanda akayi ya fada mata.
To amma kai yanzu ga azumi ya zakayi da wadannan tafiye tafiye ga hada kayan aure, ....ya mike tabbb ni kuwa nasan yanda zanyi mamee ya haye sama
.......