← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 37

Sashe 20

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

....... Ya kyalkyace da dariya ta bishi da wani irin kallo. Mamaki ya baibayeta wai meke damun *madaki sometimes?*
Ta langabe don girman Allah kayi hakuri ba don ni ba wallahi bazan kara ba...
Baza ki kara me ba?
Ta yi shiru, kinji?
Don Allah ni dai kayi hakuri.
Okay naji zanyi amma da sharadi kullum da kinzo zaki wuce sama ki fara gayar dani kafin ki shiga inda mamee take kin amince?
Eh na amince duk ta kagara ta sauka,
Ya kalleta idan kika saba menene hukuncin ki?....ka rike albashina na amince,
No! Banda wannan... Ta kalleshi cikin kosawa duk abinda kaga dama na amince kayi man.... Ko menene? Ta daga kai eh na amince bama zan saba maka ba kayi hakuri ,
Kiyi man alkawari duk abinda nayi miki zaki rama. Ta kalleshi ya daga kai *yes*! Idan na mareki kema zaki dalla man mari. Ta sunkuyar da kai na amince, no! Kiyi rantsuwa Kice wallahi zan rama. Ta dan kalleshi kaikaice *wallahi zan rama*
Ya danyi yar dariya *Good girl* ya maida hannuwan sa baya yadan kishingida kin ce ko menene fa?
Haka na ce ta fada tare da yin hanyar falon mamee. Ya bita da kallo yana yar dariya.
Saukowa takeyi mamee ta bita da kallo har ta kusa karasowa kusa da ita, sai mamee ta dauki salati..... La'ilaha ilallahu mahammadu rasulullah tana tafa hannuwa *Uwani?* gabanta ya yi wani mummunan faduwa....
Kallon ki kawai nakeyi ina tunanin ina muka sami 'yar balarabiyar budurwa tun da sassafe kuma daga saman bene? Ta karasa maganar tana yar dariya.
Ta zumburo baki kai *Mamah* ta kyalkyace da dariya wallahi da gaske nake waya baki tsarabar makka ko kudin naki ne kika kwashe kika siyo..... Kai mamah wai ya akayi? Ta karasa gunta tana yar dariya.
Ta dago fuskar ta anya *Uwani na ce yau*? Kai wallahi kinyi kyau. Ko kefa don Allah ki ringa sauya shiga amma kullum cikin kodaddun kaya kamar almajira kina fama da hijabi balam balam kai kace matar liman. Duk suka kwashe da dariya.
Allah kullum ina son miki magana amma bana son kiji babu dadi tun da ban san tanadin naki ba.
Ta mike zuwa ciki tana yar dariya ta bita da kallo ohh uwani yarinya ce har yarinya talauci babu abinda baya boyewa kuma sai ta zamo tana da hakuri da rashin kwadayi.
Kamar kullum *Mr Samuel* yazo ta fita lesson. Yana bala'in jin dadin koya mata saboda bai taba tambayarta sau biyu ba, ya dade baiga mai kokarin umaimah ba.
Ya kalleta da yake bayajin hausa ko kadan wata biyu ta gama kwarewa da turancin sa tana ganewa kawai wajen maidawa ne wani lokacin take samun matsala amma yana gyara mata to an wuce wurin.
Ya kalleta yana murmushi *primary certificate din ki ya kammala* zan bawa oga shawara ya sanyaki js 3 kawai ina da tabbacin zaki iya. Kinga da kin je SS2 kawai kiyi WAEC.
Ta washe baki haba? Lallai naji dadi. To wane school zasu amince? Ta bukata , yayi murmushi *Madaki international school* ta zaro ido yana da makaranta?
Makarantu dai ai duk kasar nan babu inda baida branch.
Yanzu haka private university yake ginawa, kano, Kaduna, Abuja, Lagos da katsina. Zaiyi lunching a lokaci daya.
Tabb lallai ta fada.
Ya kalleta ke ai kilan anan cikin gida zakiyi ta ki.
Ta kyalkyace da dariya sai kawai taga mutum kamar an jefo shi ya kalleshi *koya mata kakeyi ko maganganun banza?*
Ya mike yana kyarma no sir is part of our lesson...... Shut up, ya kalleta 6ace man da gani kada in miki rauni...tayi ciki da gudu.
Ya nuna shi da yatsa *Ka shiga hankalinka*
Ya fara bashi hakuri. Lesson din da ba a kara ba ya hana.
Washe gari kamar yanda tayi alkawari ta wuce sama direct yau idonsa biyu, kwankwasawa daya tayi ya ce *Shigo*
Tana bude kofa ta durkusa ina kwana?
Ya dan harareta da Allah malama shigo ciki.
Ai kaji matsalar, nasan bazai taba amsa gaisuwa ta ba. Ta fada a zuci tare da shigewa ta rabe a bago.
Kinga leda can da jaka ki dauko, uniform din ki ne da school bag. Ta washe fuska ta nufi wurin da sauri.
Monday zaki fara zuwa idan kika saki kika kasa maida hankali sai na miki bugun kudina don bazan yi asara ba.
*Ta durkusa guywa biyu* na gode Allah ya saka da alkhairi ya kara arziki mai amfani.
Ya dade yana kallonta har ta ji ba dadi tunda kanta a kasa yake.
Ya ce amin.
Magana ta karshe makarantar *mix* ce wallahi kika kula wani namiji kin gama karatun daga ranar..... Ta banka mishi harara ya zaburo *Au baki dauka ba?*
Ta kwashi kayan tayi waje da gudu tana fadin *Nima so kake in tsofe irin ka ba aure*?
Ya biyota da gudu yana iyye yarinyar nan kin gama rainani ji kakeyi daf daf daf....da da da.... Karar gudu dai dai mamee na fitowa tayi bayanta wayyo mamah ..wayyo zai dakeni.
Ta tattare kai tsaya wallahi ka taba ta sai ranka ya baci. Me ta maka?
Umaimah daga bayanta ta ce uniform ya bani zan fara zuwa makaranta litinin wai idan na kula maza na gama daga ranar. Don na ce so yake in tsofe kamarshi ba aure shine ya biyoni zai daka......
Mamee ta zaro ido ta kalleshi sai wani mazuran borin kunya yakeyi. Sai kawai tayi murmushi, kayi hakuri toh bazata kara ba.
Mamee yarinyar nan fa ..... Na ce kayi hakuri *uwani shige ciki* ta ruga da gudu kuwa.
Ya bita da kallo kamar yanda mamee itama ta tsareshi da idanu.
Fakam fakam yayi sama.
Ta koma ta zauna bisa kujera *Haba wallahi koda naji* fitinar nan ta uwani da madaki ta isa watan *Son ta yakeyi shi ne yaketa wannan haukan*
Wani sanyi ya diri zuciyarta bani da matsala da uwani wallahi. Ta rike haba *ohh*....
Ta yi ciki ta tarar da ita zaune. Ta na ta nishi.
Ta kalleta taji ta kara sonta fiye da *da* wannan kauna da nakeyi ma uwani ta isa, ashe surukuta zanyi da ita.
Ta zauna kusa da ita, uwani?. Ta kalleta kawai, ki daina biye mishi kina wannan mugun gudun wata rana sai kinyi wa kanki rauni. Idan ya taso ki tsaya kiga zai kasheki?
Duk sharuddan da ya kindaya miki to kibi su babu kuskure matukar kina son Ku zauna lafiya ya daina wahalar da ke.
Ta ce toh, ta kalleta wai rigunan da yawa kika siya haka naga ta yau tafi ta jiya kyawu.
Ta yi murmushi mamah wadannan kayan fa *Madaki* ya kawo mun ta zaro ido *madaki* ta kwashe duk yanda akayi ta fada mata sai kawai ta hau dariya *Au har mutanen gidan naku ma basu tsira ba?*
Lallai abun nashi azimun ne. Shawara daya zan baki ki daina hawa sama idan yana nan in ba wani kwakkwaran dalili ba ko gyara idan zakiyi ki bari sai ya fita office ranar da duk bai fita ba to ki kyaleshi.
Ta ce toh.
Ranar litinin tunda safe ta iso a falo ta tarar da shi nan suka gaisa tayi ciki don shirin makaranta.
Ta dora hannu a kai *Na shiga uku* dan skirt ne bai karasa kai guywa ba hade da karamin wandon sa sai farar riga yar shirt mai karamin hannu tare da neck tie. Ta zaro ido wai makarantar su Khausar zanje? Irin kayan su ne ta shirya tsaf, da doguwar safa sai farin takalmi *camp bus* sai yar hula karama daman tayi sabuwar kalaba kanana amma duk ta hadeta wuri gida ta kulle, shiru shiru ta fito mamee ta shiga ta ganta tsaye. Ke fa kadai bus ke jira gasu can suna *oda*
Mamah haka zanje? Ta zaro ido babu ruwansu da ke makarantar duk turawa ke koyawa..... Kirjinta ya harba. Mamee ta kamo hannunta ta sagalo jakar sai rinjayarta takeyi saboda nauyin litattafai. Ya bita da kallo wani kishi ya turnukeshi ya daga murya.
Mamee.... Ta juyo da sauri
Sai kawai yasha mur ya kalli umaimah *Ke jeki sanyo doguwar hijabi idan kinje makarantar kya cire*
Mamee ta dankara mishi harara ke muje ta fizgeta.
Ya taso da sauri suna fita ya hango su baffa cike a motar suna jiranta. *Cikin gardawan can zata tafi?*
Wuf, ya fizgota hannun mamee ya daga murya *kai isma'ila tafi kawai zan kawo ta*...........Ya yi ciki da ita yana zuwa falo yayi sama ya dauko key din *private car* din sa.
Mamee na waje tayi tsaye tana dariya kamar me?
*Ta gama tabbatar ma zargin ta* farinciki kamar me tana jin motsin fitowar su tayi baya da sauri.
Umaimah dai simi simi ta rasa inda zata kanta don kunya tayi shiru kanta kasa.
Tuki yakeyi yana faman tsaki duk karatun nata ya bashi haushi. Kadan kadan yayi tsoki yana ta sake sake,
Mamee ta ce tohh abin haka yake ashe ina ta wahalar da kaina a waje ashe rabon na tare dani. In na haukan madaki ba an taba so da *Masifa*? Ta kyalkyace da dariya yau naga ikon Allah ni jikar buzaye.
Ya kaita har bakin kofar office din principal ya ce ki shiga zasu kaiki class idan an tashi kuma ki jira zan aiko..... Ta fita da sauri ta kyaleshi.
Ya bita da harara kawai ya juya a guje.
A class din su khausar aka kaita SS1 wurin zaman su daya. Hankalin kowa ya dawo kanta. Khausar ta gabatar da ita amatsayin yar uwa hakan yayi mata dadi sosai.
Umaimah na cikin matsala da farko don bata ganewa sosai saboda ta riga tasa tsoro a ranta bata taba zama aji ba. Sai da khausar da wata kawar khausar da suke kira *Yar gata* sukayi ta karfafa mata guywa. Cikin sati biyu sai ta ware.
Tun da ta shiga makaranta bata da lokacin kanta ga azumi ya kusa,
Idan ta dawo makaranta karfe biyu kafin ta gama wa mamee kintse kintse hudu tayi ta tafi karatun islamiya shidda tana yi gudu gudu zata bar gidan.
Ranar wata asabar tazo karfe takwas ta tarar mamee da baki falo ta shiga musu hidima yi wancen dauko wannan. Har ya shirya ya fita ransa a jagule.
Washe gari tana zuwa ta tarar har ya yi wanka yana faman daura agogo ta durkusa kenan ya ce *ta shi kawai* yau ranar punishment ce , tasan za ayi haka gabanta ya fadi ganin yanda ya 6ata rai. Ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta.
Ya tako zuwa inda take kin tuna da alkawarin da kikayi cewar zaki rama duk abinda nayi miki ko?
Ta daiyi shiru ya fizgota ta fada jikinsa ...... Jikinta ya fara kyarma ya kai bakin sa kunnen ta *Kinyi alkawari*..... Tsikar jikin ta ya tashi ta yi baya zata zulle ya maidota da sauri wannan karon fuskarta ya tallabo kawai taji ya mata *kiss*.............
Chapter 20 · 0% Book details