← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 37

Sashe 10

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.....wallahi nasan za ayi haka duk laifin na mansura ne. Umar baka da hakuri ko kadan...... Ta shigo tana bambami,
Naji jiya kana son a gyara ma daki shine nabar sallahu amma bazata kara hawowa saman ba daman ni ke tilasta mata muje uwani....
Mamee yarinyar nan fa rashin kunya takeyi mani ina fada tana fada dubi jikina kawai ina fitowa naganta ciki ba halin in tambayeta?
Na fada mishi kece kika turo ni har rantsuwa nayi mishi amma bai yarda ba....anki a yarda din.
Mamee ta banka mishi harara, umaimah tayi gaba abinta, ai bazata kuma zuwa ba sai kayi hakuri da gyaran su mansuran ganin kana yabawa da natan ne yasa nake tilasta mata.....
Au ni yanzu laifi na kika gani?
Don me zanga laifin ka tunda kai ta tarar?... Mamee....ta nuna shi da yatsa rai a 6ace tunda ka nuna ban isa da kai ba kaje madaki abinda duk ka iya kayi. Yarinya marainiya ba uwa ba uwa, inda take bataji dadi ba nan din ma ka takura ta ka hana yar mutane shan ruwa? Kai haka akayi maka!
To wallahi kaji tsoron Allah na fada maka.....ta fice jikin sa yayi mugun sanyi
Tabbas yau yarinyar nan batayi niyyar biye mishi ba kureta yayi. To ai kuma ni shirun nata ke ban iya jurewa. A gurguje ya shirya ya sauko sai mazurai yakeyi ta inda zai ganta,
Simi simi ta fito tana goge kwalla fuskarta duk tayi ja.
Kawai sai yaji wani iri alamar rashin yin daidai.
Ta saci kallonsa kawai ta gittashi ya bita da kallo....
Yasan ko yabi ta wurin mamee shareshi zatayi sai kawai ya fice.....
Duk tayi sukuku ranar har yanzu gabanta bai daina faduwa ba. Ita bata taba ganin babban mutum ba kaya ba sai yau.
*madaki nada kyau amma ba shi da kirki* matarsa ta gama shiga uku ta fada a fili. Mansura ta sameta ta bata hakuri ta ce ba komi.
Tunda na gama mamah zan tafi gida.
Ta kalleta a nutse zo nan uwani ta kamo hannunta tare da zaunar da ita bisa kujera kusa da ita.
Kinyi sukuku idan kika biyewa madaki ko ruwa bazaki sha ba, haka yake kwanaki da ya taso wata mai aikina dole ta hakura da aikin wai kazama ce,
Ke kuwa yayi ya gama muna nan tare in shaa Allah aure ka rabamu,
Tayi murmushi kawai.
Duka fa yanzu karfe biyu ki yi zamanki kinji?
Zatayi magana ta ce af! Ke dauko mana tsamiyar birin nan mu birirriketa sai ta kwashe da dariya. Shi kenan ta wasanshe
Suna sha suna raha kamar kullum, ya shigo rike da jakar *system* din sa.
Tana ganin sa jikin ta yayi sanyi.
Aaaaaaa mamee kurmusun me akeyi? Ya fada idonsa na kan umaimah yana kallon yanayin yanda take tsotsar abin a bakin ta.
Murmushi mamee tayi kurmusun tsamiyar biri,
A bani in shaa... Ta dubeshi da sauri ganin ya miko hannu, ta ce uwani mika mishi ta fada tana yar dariya.
Af kinga ina zuwa inji mamee ta mike ta shiga ciki da hanzari alamar wani abu ta tuna.
Ta dauko ledar ta ajiye mishi kasan kafafun sa ta barshi da hannu sake,
A hannu zaki ban.
Ta dauko ta mika mishi, tare da mikewa zata bar wurin yayi saurin riko hannun ta,
Wai kai idan ba ka taba jikina ba baka jin dadi?
Ya yi sauri ya saketa to ki koma ki zauna sannan kidaina gigin matsawa ko ki tashi daga inda kike matukar ina miki magana..... Yanzu magana kake mun? Ka ce in baka na baka sai me?
Ya sha mur sai ki zauna ki ringa barewa kina miko mun yanda kikeyi wa mamee.... Bazan ba ko kai mamee ne?.....ya fincikota ta fada jikin sa.
Ke bakinki bai mutuwa ko? Ya matseta.... Sakarni malam ko gantsara maka cizo......mansura ta fito uwani kizo inji...... Maganar ta tsaya ganin madaki, ta yunkura ya kara riketa, jeki ce tana zuwa, tayi baya da sauri,
Kwalla suka shatato mata, ya bisu da kallo duk tsiwarta bata da wuyar kuka, ya hade hannayenta dauko kiban sannan ki tafi.
Taga ba sarki sai Allah ta dauko ga hannuwansa duka rike da ita, sai ya bude baki, ta balla mishi harara sannan ta watsa mishi.
Ya saketa barkanki yarinya da....... Tuni ta shige ciki da gudu yabi bayanta da kallo.
Gani mamah,
Zo nan ki tayani gyaran sarka,
Ya tashi yayi sama cikin nishadi yana tsotsa.
Cewa nayi a kira mun ke kada ya miki wata muguntar. Ai cikin satin nan dai zai tafi Germany ki huta.
Murmushi kawai umaimah tayi.
Mamee bazata bar yarinyar nan ta zo ba kona kira.
Ya dauki waya hello mamee don girman Allah kibar yarinyar nan tazo ta gyara man daki wallahi kinji nayi rantsuwa bazan kuma sata kuka ba. Na daina biye mata please.
Ka tabbatar? Wallahi eh kinji nayi rantsuwa.
Shi kenan ta ajiye, Uwani jeki gyara mishi dakin ki sauko.
Bata San lokacin da ta ce innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ba. Ta kalleta zuwa saman keda wannan salatin? To bazaki ba wallahi ina dalili. Kyaleshi ai shi ya jiyo.
Ta langwabar da kai don Allah mamah tunda na gama in tafi?
Tausayinta ya kamata yanzu har tafi sha'awar tafiya gida da zama da ita saboda masifar madaki.
Tashi ki tafi kinji.
Zumbur ta mike tana murna ta bita da kallo.
Shiru shiru sai kawai ya sauko, baisan ko wacece ba zata wuce ya ce ke ina yariyar mamee?
Yanzu kuwa ta tafi gida..... *what* ? Da daka tsawa har ta dan firgita. Yayi ciki mamee! mamee!! Ya na bude kofa ya fara masifa,
Kinga abinda na ke fada miki ko? Yarinyar nan fa gida ta tafi.....eh ina sane da hakan. Yayi turus!
Ka firgita 'yar mutane kwata kwata yanzu bata sha'awar zama gidan nan duk ta tsorata ka hanata sakewa wannan masifar taka ta yi yawa.
Shine kika bata dama ta tafi? Fine! Kawai ya juya yayi sama.
Gashi ya rarratsa wayar da yake da numberta don bai wani tsaya saving ba, mtsewww yaja dogon tsaki sai kawai ya fara hada jakunkuna.
Umaimah kuwa tana fita gidan ta mance komai cikin sa'a tana zuwa ta tarar an maido wuta ta kwashi kayanta ta nufi gidan Alhaji yakuba guga.
Karfe shida na safe tana lazimi ya shigo, mamee zan tafi Germany sai Allah ya mana dawowa.
Yau ne? Ina ce sai jibi,
Eh akwai shirye shiryen da zanyi ne. Ya mike. Tabishi da kallo a dawo lafiya.....
Ya wuce yana fushi, tunanin umaimah zai zautashi mamee kuma na babbakewa gara yayi nisa da gidan wata kila zai mance dasu din.
Abinda madaki bai sani ba zaman sa gidan a haka ne saukin sa, domin da ya tafi sai da ya gwammace kida da karatu kusan zaucewa yayi hatta matan kasar sai suka ringa rikidewa suna koma mishi umaimah,
Kam bala'i kada fa ace son yarinyar nan nakeyi? Innalillahi ya Allah kada kayi mun wannan jarabawar .
Umaimah kuwa gida yazamo mata gwanin dadi ta warware, ga kwanciyar hankali ba fitinar madaki ga cimar dadi nan da nan jikin ta ya canza duk inda yake a dame ya taso, gida kuma ta kulle ita da lubabatu saboda hasafin da takeyi mata a boye, ko kayanta ma ta daina tabawa, ta karbi kudi gun hajiya ta yanko wasu yan material masu arha kala kala akayi mata dogayen rigunakala uku wasu kuma tayi da skirt kala biyu. Sannan ta yanko hijabai ita da mamee kala kala har ta baiwa lubabatu biyu ciki.
Umaimah na da kokari har ta shiga hizif na talatin ta kuma gama hadisai biyu *haqqul mubeen* 1&2 ta shiga *bulugul maram*
Duk yaran gidan yanzu ita ke masu kari.
Cikin sati uku ta canza sosai girma yazo mata lokaci daya kirjinta ya cika sosai.
Duk bayan kwana biyu take hawa sama tana gyara masa, haka zata kunna gwanja tayi ta tikar rawa tana aiki sannan idan ta gama tayi mai isarta sannan ta sauko,
Ko sunan madaki bata son taji an ambata ta gama tsanar sa a zuci yar ta bata kaunar kara gajinsa.
Gareshi kuwa a bin ba haka yake ba, ya kagara ya dawo wani lokacin yana jin hayaniyarta idan suna waya da mamee kamar yace mata bani ita.
Ko tambayarta ya kasa yi ina uwaninki.
Ya dankaro mata tsaraba, dogayen riguna, kayan shafa da turaruka, tunda ya siyi kayan yake tunani idan zai bata me zai ce ko kuwa yaba mamee ta bata kara taki karba? Haka dai ake kullum ba canji oga umar madaki.
Sanye take da doguwar rigar material fari da flowers pink dinkin ya kame mata kugu ta kaso kallabi tana faman gyara mishi gado.....
Mamee na falo taga mutum kamar daga sama,
Ta washe baki saukar bazata...??? Yayi yar dariya suka gaisa, ya fara dube dube,
Kamar uwani tasan da zuwanka wallahi, tana ta cewa sai gobe zata gyara ma sama kome ta gani? Kuma dai ta tafi, yanzu ma ai ta kusa gamawa.....zumbur ya mike ku hau man da jakunkuna sama yabi bayan su mamee bari nadan watsa ruwa na gaji. Ai dole da gajiya kam,
Daya ke dakin bude yake sai kawai taga ana shigowa da jakunkuna...... Ta zaro ido, tayo tsalle ta dirko *ya dawo ne*?
*Ga ma shaida*...... Ya fada lokacin da ya kunno kai...........

*maman Abdallah*

😘😘😘😘😘
[1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣1⃣3⃣
Chapter 10 · 0% Book details