Sashe 2
Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar da gaske ta dan razana laaaaa ban gani ba taja baya zata gudu Ya chafko hannun ta, Asma'u ta daka mata tsawa haba umaimah baki gani ne? Tayi ta kicin kicin ta kwace hannunta amma ya ruke su tamau, ba komi ya fada yasa dayan hannun sa ya fizgen gyalen ta ya fara kwashe plates din dake bisa jikin sa sannan ya ya ci gaba da gogewa, duk illahirin jikin sa ya baci, yarinyar nan na janyo mun asara amma zan maganin ta a yau.
Biki ya tsaya chak! Yaga kowa ya mai da hankalin kansa abinda ya tsana kenan ransa ya kara baci. Ki kwashe kwanukan kikayi tsaye, ta kalli kanta ta yaya zata ratsa dubun mutane ba gyale? Wannan wulakanci dame ya yi kama? Ga kayan duk sun matse ta....ta daka mata tsawa ko ba kyaji? Ta duka tana kwashe kayan ya yi fit! Da kallabin ta kananan kalaban da ke kanta suka watso mata ko ina ta mike da sauri zata zazzaga mishi bala'i ya ce yafa gyalen don naga baya daukar miyar sosai gashi ba towel da zan goge kayan naki sun kama da bargo.
Ji tayi an fizgeta da karfi, tana juyawa taga fiddausi, haba umaimah kinsan waye kika batawa kaya? Zo muje ki karbo towel mota kikai mishi. Figai figai babu gyale ko kallabi nake binta zarai zarai idanuna sun kawo wani ruwan bala'i.
Anyi anyi ya tashi yaje ya sauyo kaya yakiya wai zai jira a gama. Ransa kuna kawai yakeyi amma ya kasa nuna wa duk da fuskar tasa kullum tamau.
Don Allah Anty fiddausi ko kallabinki ne bani in yafa kada in kuma ratsa mutane haka. Har zata yi musu sai kuma ta kwanto ta bata kowa head ya saka amma wani ikon Allah ita fiddausi ba ta sanya ba. Tun kafin ta hau saman ta hango kallabin da gyalen a kasan kafar sa yana goge sauran miyan da suka zuba. Tuni an ci gaba da sha'anin biki amma ganin ta hawo saman sai hankalin amarya ya dawo kanta, ta mika mishi towel din tare da banka mishi harara.
Baki iya goge masa wai yau meke damunki *UMAIMAH*?
Ya maimaita sunan cikin takaici a zuciyar sa *umaimah* ta duka ta fara gogewa shi kuma ya kara shan mur, dataga hankalin asma'un ya koma can sai ta fara dangwalo wata miyar dake ajiye ta na kara yaba mishi a inda bai samu miyar ba. Hada hannu. Ya kura mata ido yana wani irin mamaki wai yarinyar nan tasan waye shi? Yaci gaba da kallon ikon Allah tasha mur sai kwaso miya takeyi tana kwaba mishi sai tasanya towel din ta dalaye. Tana gamawa zata mike ya dankwafar da ita ta koma da karfi ta zukunne, ya kalli abokin sa yace idan bazaka sha wannan naman ba kaban, ya miko mishi bai ko kalleshi ba yaci gaba da kallon yan rawa, sai kokarin dagowa takeyi shi kuma ya danne kafadarta da hannu, ya dan waiga yaga kowa hankalin sa yana gun yan rawa ya sa hannu ya bude gaban rigar ta ya kwarara mata duka miyar cikin breast ware sannan ya sake ta tafadi ta baya dabas! Ya kawar da kai kamar baisan komai ba. Na kusa dashi ya kalleta easy! Tashi mana.
Ta mike a wahale miya na zurarowa cikin rigarta duk ta bata ta nama cike cikin brezia.
Kwalla suka shatato mata wannan wulakanci da me yayi kama? Ganin tana kuka yasa yaji wani sanyi a ransa hakika yanzu ya fahimci 6acin ranta. Ta fita farfajiyar tana faman zubda hawaye fiddausi ta tareta tare da daka tsawa haba umaima ji yanda kika batan kallabi, ta dubi kallabin Wanda ya zamo tamkar makwararin juyewar miyar. Zatayi magana ta fizge abinta tayi gaba.
Ta koma bayan hall din ta duke tana kuka, kukan takaici ba gyale ba kallabi. Tayi mai isarta, har duhu ya fara nan da nan taga mutane na fitowa alamar an gama ta kara lafewa jikin bango.
*zan jira a gama fitowa in koma in dauko gyalena da kallabi cikin miya in yafa hakanan amma bana iya ratsa mutanen can haka* ta fada cikin muryar kuka.
Wallahi ko waye ubansa a garin nan sai na rama wulakanci na ta buga tsoki.
Acikin hall abokan gewaye dashi suna faman ya taso amma ya kasa ko motsi. Baya iya ratsa dubun mutanen nan haka yanda aka sanshi a gari irin daraja da kimar sa.
Ya kara hade rai na fada muku kuje zan taho nayi waya za a kawo mun mota kuyi amfani da wacce mukazo ciki key na hannun.... Gashi nan daya ya fada. Ya tabe baki okay you can go zan taho, zasu kuma magana ya ce please Ku kyaleni wallahi kuna dada sani damuwa.
Dole suka fita, a rude amarya da ango suka iso zasuyi magana kenan ya yi murmushi karku damu bazan iya fita haka ba idan kowa ya gama tafiya zanje ya kalli Asma'u karki damu da abinda kanwar ki tayi mun......... Ba kanwata bace yallabai diyar makwabta ce amma tana shigowa gidan mu kama aiki........'yar aiki? Ya maimaita a rai.
......what ever ba komi kuje nayi waya za a zo a daukeni.
San in ko waye yasa sukayi gaba.
Umaimah kuwa lekowar da zatayi sai taga motar karshe ta fice yayin da wata ke shigowa ta zuro a guje sai taga sojoji biyu sun fito cikin wacce ta shigo din, tayi cikin hall din a rude, dai dai zai mike ya hangota ranshi ya bashi lallai gyalen ta biyo, ya kwashesu duk ya cusa aljihu duk da suke sharkaf da miya. Ganin shi bai wani daga mata hankalin ba domin ta gama rikicewa da dare gashi kowa ya watse, duddube duddube takeyi tana zare idanu shi kuwa yayi tsaye yaji ko zata tanka mishi sai kawai tayi hanyar fita ya zabura ya damko ta, kamar tana jira ta harzuka wai kai *maye* ne? To kurwata tafi karfin ka, meye hadina dakai yauni naga bala'i.... Ina kika ga bala'i wallahi yau sai nayi maganin ki ya figeta sukayi waje yana dube dube yana faman zare ido, kawai sai taga jelar gyalen a aljihunsa. Ta kalleshi taga lallai ya fara rasa hankalinshi don fushi, to me zai Mani? Ganin sojojin nan na tunkaro su yasa ta gantsara mishi cizo a yatsa kamar zata cire ya fasa kara *kaiiiiii* yana sakin ta tayi wajen *gate* din a dari da sittin.
Daya daga cikin sojojin ya yunkura zai kamota yayi saurin tsayar dashi.
Allah ya taimaketa tana fita ta samu adaidaita da kamar bazai dauketa ba tace party tazo bata gari suka biyota.
A kofar gidansu ya ajiyeta, ta karbi dari gurin sham'unu mai manja ta bashi, ta shige gida ana babban falo ana kallo ta sadada taje ta sauyo kayan.
Washe gari wunin biki taki lekawa hajia tayi aiken duniya sai ma tabar gidan.
Karfe bakwai na safiyar walima hajiyar ta aiko kanwarta ba halin kara wata dabarar saboda ta ce kafarta kafar umaimah. Ko kalaci batayi ba.
Tana shiga tasanya ta gyaran daki tana fada kin San idan bake kika gyara man dakin nan ba bana jin dadi amma hiratan jiya kika ki lekowa to yau ai kyasha aiki ko fidda dattin tayil dinan kadai ya isheki.
Ga kayan ki can na kulle miki amma ina gyalena dana ara miki? Gabanta ya fadi tayi dan kasake kafin tace, yana gida zan wanke ne, to ba komi tayi waje.
Ta shiga gyaran dakin tayi mishi fes cikin yan mintoci saboda bata da nawa, anata shirin walima ta ce umaimah maza shirya ku tafi walima,
A'a yau bana jin dadin jikina hajia kuma idan na tafi wazai gyara baranda? Ki bari su tafi sai in karasa gyara miki gidan.
Allah yayi miki albarka ya zaba miki miji na gari, ta washe baki amin hajiyar mu. Tayi waje da wasu kwanuka ta ce ina zanje mu kara haduwa da mugun nan? Inba rigima irin tau ba inani ina haye ma irin su?
Su hudu suka shigo tana ta faman hada kayan wanke wanke, kafar dattijuwar ta murguda tayi kichaaaaa zata fadi umaimah ta saki kwano tayo kanta ta tare sai ta fada jikin umaimah amma duk da hakan kana jin karar da kafar tayi kat!
Subhanallahi sannu mamah ta fada yayin da dattijuwar tace washhh!
Sai kawai cikin Matan nan wata ta ingije umaimah move... Ta tallabo matar.
Cikin fushi umaimah ta kalleta ta ce *move*? To anki ayi move din ta hankade ta ta tallabo matar duk suka zaburo kan umaimah, kada wacce ta matso, matar ta fadi a hankali. Sorry mama suka fada suna ja baya,
Au da taron dangi zasuyi mun? Ashe kuna sonta zaku barta ta fadi? Data kai kasa ai da kun ce *move* da hujja aikin banza.
Ta juya sannu mamah ita kuwa sai bin umaimah take da kallo bayan *Umar* ashe akwai Wanda zai iya fada kan lafiyar ta haka?
Kukayi kototo ku kamota mukaita daki ta daka musu tsawa.
Qalu innalillahi hajiya bilkisu lafiya? Sai bayan da suka ajiye ta saman kujerar sannan ta ce wallahi turjewa nayi. Tana faman runtse ido saboda azaba.
Umaimah tayi saurin zuwa gidan su cikin kayanta ta dauko kwankwalaton Robb tana shigowa hajiya ta ce yanzu nake Neman ki jekira sadi a kira mai kamu ya duba kafar, ta ce to bari in shafa mata Robb na dauko gida tukun saboda zogi.
Bata jira sun kuma magana ba ta tallabo kafar tana shafa Robb din a hankali mamaki ya cika hajiya bilkisu kallonta kawai takeyi, ita kuwa umaimah tana son gyara kafar data dago sai taga ita take kallo, hajiya na ajiye plate din nama umaimar ta zabura kamar wani abu, suna duban wurin ta mayar da kafar kowa yaji ta ce kas!!! Tare da karar da hajiya bilkisu ta saki. Sama akayi da umaimah ita dai taga anyi hanyar waje da ita.....
❤ *Maman Abdallah*❤
💑 *AUREN FARI*💑
0⃣0⃣3⃣