← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 37

Sashe 12

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Gabanta yayi wani mugun faduwa, ya kura mata ido ta bala'in canza mishi, ya fara taku zuwa inda take tsaye tana yar kyarma,
Ta fara yin baya baya yana biyota har sai da ta kure ma bango, ya sa hannuwan sa duka ya dafa bangon yayi mata katanga tare da sunkuyo wa dai dai fuskarsa fuskarsa murtuk..... Ke baki iya gaisuwa ba? Ko kinfi karfin kiyi man sannu da zuwa?
Ta dago kai aiken ka nayi?
Me yasa kake da neman dalili?
Ta ingijeshi ai fa ka dawo,....ya fizgota da karfi ya buga bayanta a bango. Ai fa na dawo? Ni da gidana kike fadan aifa na dawo watan baki so na dawo ba ko?
Kwarai ban.....wata muguwar matsa yayi mata tayi shiru sai kawai ta fara kwalla...ya kura mata ido sannan ya saketa a hankali ya dan ja baya ta kwasa da gudu ya bita da kallo.
Kafin ta sauka kasa tayi saurin gyara fuskar ta, mamee na ganin ta ta ce yawwa je kikai man wadannan fridge, waccen ledar kuma ki juye mana a tray kizo da wuka,
Suna ci ya sauko janye da jaka....
Wai mamee keda yar nan taki baku da aiki sai ci?
Dariya tayi, barakallah da lafiya akeci ai,
Yayi murmushi Allah yarinyar nan ta koya miki ci duk gashi nan kunyi yan kumatu..... Kai bani son sa ido, Apple din ne ci? Uwani ma da ta tsani abinci kullum nan cikin mata fada nake,
Ta mike zata bar wurin duk ta hade rai, ya daka mata tsawa ke! Wallahi kika bar wurin nan bazan biyaki albashi ba wannan watan,
To azabau ka dawo zaka hana ta shan ruwa ,hada wallahi? Uwani zo ki zauna,
yasha mur kawai.
Ta bishi da harara ta zauna.
Yarinyar nan ta gama rainani mamee ita tafi karfin ta gaisheni ne?
Ko sannu da zuwa fa.
Kana mata wannan hayagagar zata gaisheka?
Ya kamata ki ringa nuna mata kuskurenta zata sha wahala tamm..
Ta kalleshi kai wane irin yaro ne mai taurin kan tsiya?
Shin nayi shiru, ya fada yana watsa hannu, ga tsarabar ki sauran na sama.
A a a uwani buda mu gani, mazga mazgan riguna ne irin wadanda mamin ke sawa da mayafai .
Ta kalleshi banga abinda zaiyi wa uwani anan ba,
Ai daman naki ne, ya mike kawai yayi sama abinsa,
Ta kalleta ke bishi kice yaban sauran wata kila acan ciki kya samu,
Gabanta ya fadi, in dai don ni wallahi na yafe mama haba.....ni ban yafe ba, ko dan turare ai kya samu gasu mansura can kowa da ledar sa danaji babu taki a ciki nayi tunanin tare zai hado man.
Jeki maza ki karbo ta fada tare da shigewa ciki.
Tayi tsayeeee!!! Allah gani gareka, me kuma zan tarar?
Kamar wacce kwai ya fashewa take tafiya, zan bi duk wata dokar sa in shaa Allah.
Sai da ta hadiye wani tsinkakken miyau tare da sakin ajiyar zuciya sannan ta kwankwasa,
*come in*... Ya ce daga ciki,
Ta murda a hankali *Assalamu alaikum,*.....
Allah kasa amsa sallamar yayi *he wasn't expect her now* ya tashi zumbur dama ya dan kishin gida ne,
Ta dan sati kallon sa, kwanciya dai kwanciya mtseww kamar mace, amma a fili sai ta ce,
Hajiya ce ta aiko wai ka bata sauran kayan. Ya mayar da kai kawai ya runtse ido, yafi mintuna biyu, ta dai yi tsaye tana wasa da hannunta cikin hijab kanta kasa,
Ya dago ga su can a Leda.... Ba bata lokaci ta dauka tayi hanyar fita........ Tsaya! Yace,
Gabanta ya fadi tayi chak tare da runtse ido, *to wace masifar ce kuma?*
Ta kasa juyowa,
Ki miko mun jaka gata can...lokacin ta juyo da sauri, tayi hanyar inda yake nunawa,
Ta ajiye mishi kawai zata juya, *idan kina so ki dauka idan kuma bakya so kibarta nan*......sai kawai ta juya abinta ya daka mata tsawa cikinta ya murda ya dirko gabanta *bakiji me na fada ba?*
Ta kalleshi a wulakance ni kuwa na jika, ka ce idan ina so in dauka idan kuma bana so in barsu nan, haka ne? Ta bukata tana hararar sa sama da kasa tayi kicin kicin da rai, shine kaga na barsu din *domin bani bukata*......ya yi mata wata irin chafka har zaiyi magana kuma sai ya fasa ya bankada ta tayi baya baya taga taga zata fadi.
Ko kallon sa batayi ba tayi fice warta,
Dan rainin wayo wannan uwar jakar zaice in dauka to duk meye aciki watan in dauka ya gana man wata azabar, kai *madaki ya shiga uku da masifa* INA dalili.
Ledar magungunan mamee din ne da take sha na hawan jini tare da sauran maganin da take shafawa a kafafu.
Mtseww ta buga tsaki, kyaleshi uwani ai zan tafi umara nima tsaraba sai kin ture.
Ta yi yar dariya kwarai kuwa mama.
Wai tana nufin zanyi asara ne? Tabb ya zabura sai wayarsa tayi kara.
*Yeah Ku shigo ina sama* ya kashe
Abokansa ne wadanda ke kula da wasu kamfanonin sa zasuyi meeting.
Ya kira mamee, a kawo mana abincin mutum goma .
Yayi ta zuba ido yaga umaimah amma bata ciki, abinci ma baici ba don takaici, da la'asar ya sauko, tana ta faman gyara wasu duwatsu kaman na sarka,
Ya kura mata ido yana kallo, babu abinda yake kwantar masa da hankali yanzu irin kallon ta,
Ta dago kai kawai taga ita yake kallo ya sakar mata murmushi ta balla mishi harara kawai taci gaba da aikin ta.
Kai ni kike harara?
Yarinyar nan kin rainani ko?
Tayi mishi banza
Kije ki dauko jakar nan ko kuma wannan watan baki da albashi......ta dago zatayi magana yace wallahi zan hanaki kudinki kin San zan iya ko?
Ta mike ta shiga ciki, sallama tayo wa mamee kawai ta fito tayi hanyar waje,
Ya yunkuro ya kamota da karfi *me yasa kin fiye taurin kai?* ta lumshe ido tare da dafe kanta tana magagi kamar me shirin somewa, ya kara matsarta ya daga murya, kina ganin zaki iya ja dani........luuu ta tafi ya tareta a kirjinsa tare da zaro ido *UMAIMAH*...Ya firgice ya rikice ya waiga ya waiga ba kowa, ya sungumeta yayi bisa kujera ya kwantar yayi ciki da gudu ya dauko ruwa..... Ta bude ido a hankali koda taga ya shige sai ta mike tare da kwasawa da gudu.
Ya fito da kofin ruwa a rude.....kawai yaga wayam. Ya kwala kira umaimah...garam yaji anja kofa. Nan da nan ya fahimci me tayi ya yi wurgi da kofin da ruwa ji kakeyi ratsatsatsa..............

*Maman Abdallah*

Good morning to you all😘😘
[1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣1⃣4⃣
*A rubutu na idan kuka ga MZ to ina nufin MOTHER a hausan ce ina cewa MOZA*
*Ba kowa ke da sunan ba sai Babbar masoyiyata SALAMATU DAHIRU wasu na kiranta SALAME DAHIRU kamar yanda kuke son wannan labarin to tabbatas ita ce jagoran siya mun data ba tare da tayi shawara da kowa ba don in muku rubutun AUREN FARI ku nishadantu ku kuma ilimantar. Zata sami addu'a daga gareku? To ina bara domin nima na ce ALLAH YA KARA DAUKAKA SANA'AR TA YA SHIRYA MATA ZURI'A YA RABATA DA IYAYE DA DUNIYA LAFIYA SANNAN YA KARA FAHIMTA ITA DA MAI GIDA AMIN.* KE MI KIKA CE???😊
Chapter 12 · 0% Book details