Sashe 3
Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tsawa ta daka musu, ina zaku kaita? Ga kafar ta gyaru ta jujjuyata, suka dire ta, hajiya ta ce ikon Allah umaimah ikon Allah karambanin naki hada gyara rauni?
Ta dawo sannu mama haka akeyi idan anyi tirjiya baban mu yana gyarawa...... Na sani tabbas na san haka.
Ta dalla musu harara kuje waje Ku jira, tsiraran mutanen da ke dakin suka ci gaba da yi mata sannu, umaimah ta duka tana kara shafa mata Robb.
Na gode nagode sannu na gode, bakin ta ya kasa dainawa har sai da ta kalleta tana yar dariya haba ai kece da sannu.
Tabar dakin ta tafi tana gyara kitchen. Wannan yarinya da hankali take hajiya suwaiba wallahi na yaba da kulawar ta sosai.
Hmmm umaimah kenan yarinya ce mai himma wallahi. 'Ya ce ko jika?
Ko daya marainiya ce iyayen duk sun rassu, tana nan makwabcin mu dan uwan mahaifin ta ya dauko riko, shine take shigowa tana dan kama mana aiki. Bata da kiwa ko kadan yarinyar nada dadin zama ga kazar kazar.
Allah sarki. Ta ce
Tana can baya tana hado kwanukan wanke wanke idan an wanke tana kaiwa kitchen dattijuwar da hajiya suka isko ta.
Umaimah hajiya ta kwala mata kira
Da sauri takaraso tana murmushi.
Ganin su biyu sai ta ce Aaaaaa kafa ta taku, ta karasa maganar tana yar dariya duk suka bushe da dariya hajiya ta ce to uwar iyeshege keda baki bar kowa ba.
Tafiya zatayi tace a kira ki rike mata kaya zuwa mota.
Tayi hanzarin warware hijabin da tayi damara dashi tace au to tare da karbar kayan.
Har get hajiya ta raka ta suka fita tare suna magana,
Ina ne gidan naku?
Umaimah ta daga kai kin hango jarkokin manja gasu can.... Ta daga ido inda baranda take?
Kwarai nan ne gidan mu.
Allah sarki.
Yaushe zaki zo Mani ziyara?
Umaimah ta zaro ido a ina?
Sai tayi yar dariya a gidana mana nima ki gyare man daki ki saman dan tsintsiyar kamshi. Ta kwashe da dariya kai wannan hajiya ce ta fada miki ko?
Tayi murmushi ai naji dadin yanda kika nunan kulawa yanzu idan za a barki gobe kizo don Allah uwani?
Umaimah nake ba uwani ba. Na sani sunan mahaifiyata gareki. Ashe diyata na taimaka duk suka kwashe da dariya.
Dai dai sun kawo inda motar, mutanen ta sunyi cirko cirko, lokacin umaimah ta gane watan yan tsaro ne, duk ta bisu da harara tana rike da ledojin.
Ta fiddo waya suka dauki hotuna tare , Ta kalleta bayan ta zauna zaki zo goben? In shaa Allah zanzo mama da karfe nawa? Bani no. Ki sai in kiraki. Woooo bani da waya ina ne gidan kiyi man kwatancen da zan fadawa dan adaidaita, tayi murmushi, kice a kaiki lamido crescent dai dai gidan *Umar madaki*
Umar madaki nasu hajiya bilkisu? Nasan gidan muna wucewa ai sananne ne daga nan ina zan tambaya?
Au kin San gidan? To ana da kinzo bakin kofa ki bada wannan katin......... Hannunta ya sagale ta zaro ido gidannnnn???? Ta fada da karfi.
Wannan karon dariya tayi ta ce karki damu ni mahaifiyar sa ce goben kizo don Allah. Ta kalli matan nan a tsorace ta kawar da kai to hajiya zan zo ta fada a sanyaye.
Ta miko mata dubu dubu dunkule bata san ko nawa bane ta ce ungo ki hawo dan sahun,
A'a haba wallahi bazan karba ba , tayi gaba abinta.
Tunani ya baibayeta, umar madaki yaro matashi mai tashen mahaukatan kudi Wanda babansa ya mutu yabar masa kamfanoni da tarin dukiya yaron da gwamnati ke tsoron sa labarin sa kaf ta sani abakin su hajiya.
Baima cika zama Nigeria ba yana yawon kasashe anyi anyi yayi aure yakiya. Shi kadai mahaifin sa ya haifa kuma matarsa daya, tsohon mai kudi ne, bada labarin sa bata lokaci ne sai gaba za a ringa fahimta.
Tana isa gida ta tara ma aikatan gate ta Nuna musu hoto tace gobe zata zo kunji? Wallahi kada Wanda ya tsorata ta.
Yana kishin gide ta shigo kallo daya yayi mata ya fahimci ba daidai take takawa ba, ya wuntsulo har ya tsoratata mamee lafiya? Me ya sami kafar kike dingishi.
Yanzu har kaga ina dingishi?
Menene ya faru? Ya bukata rude,
Tuzgunewa nayi amma da sauki ai motsuwa ce ba rauni..... Eh doctor maza kazo da sauri, ta kalleshi uwar wa zaimun doctor din na ce lafiya ko?
Amma bai yarda ba sai da doctor yace ba rauni.
Haka yayi ta sunturi, tace haka fa yarinyar nan uwani ta damu wallahi bacin ita ai da ina asibiti...... Wacece uwani? Ta bashi labarin abinda ya faru yanda ta dunga zabga wa masu tsaronta masifa.
That's very good amma she is very intelligence. Wannan shine fada mai dalili ba na wasu yan iskan yaran marar tarbiyya ba. Ya kara sa maganar yana tunano partyn jiya.
To wai yarinyar ko a billboard bata lura da hotunan sa da labaru,jaridu? To wai waye baisan *Umar madaki* ba don ubanta?..... Ka rage wannan zafin ran ai komai ya wuce tunda gashi Alhamdulillah kafar ba rauni.
Nan sukayi fira sai goma ya haye sama,
Umaimah kuwa hajiya ta samu ta fada mata yanda sukayi. Ke umaimah kada fa ta kwace man ke don bazan bata ba, kinga Asma'u tayi aure su fiddausi kuma makaranta.
Tayi murmushi hajiya ba wannan ma ba kina ganin inje ba matsala? Kwarai kuwa babu kije ai duk gida ne nan da can nida ita ai kusan daya ne, gidan su idan zata kai sha biyun dare babu mai cigiya, washe gari ta shirya cikin kayan Asma'u ta saka wani material ruwan hoda taci gayun ta tace ta tafi gidan Alhaji yakuba. Yan kudaden da hajiya ta bata tayi amfani dasu, misalin karfe sha daya na rana, ga mamakin ta kowa ya ganeta akayi mata iso. Ta ware ido tayi ta kallo tana mamakin gidan, saboda tafiya har ta fara tsorata, tana shiga falon yana hayewa sama, yaji motsin shigowa amma bai waigo ba yana rufe kofa ta kalla. Murna tsalle, duk bakin umaimah sai ya mutu har hajiyar tayi mamaki tace yau uwani kinyi shiru.
Tayi murmushi kawai, nan da nan ta fahimceta ke saki jikin ki don Allah ta fara janta da labari, nan da nan ta washe har ana kyalkyatar dariya, dambun nama, kilishi, farfesun yan ciki, kaji, tsoka, peppe chicken shinkafa da miya, shawarma. Kai abinci barkatai umaimah ta kalle su mamah wannan gara haka sai dai kin manta da abu daya, da sauri tace menene?
Ja da yellow maganin zawo. Me zatayi ba dariya ba dariya takeyi har tana kwanciya. Umaimah ta na murmushi tace yo toh.
Wayarta tayi kara tasa hands free mamee ke dawa kike dariya haka? Kada fa kiyi ciwon ciki.
AF zo ka gaisa da uwani nayi tunanin ko kana barci ne,
Ina zuwa zan dauki wata waya mamee ya kashe, suka ci gaba da cin abincin.
Tana gamawa tace zata tafi. Tayi tayi ta jira ayi la'asar tace karfe uku zataje islamiya, ance umar baya da mata to ina aka samo yaran da keta guje guje?
Umaimah zata bar tambaya babu amsa? Tabbb
Mamah yaran waye wadannan wai?
'Ya ya nane kin San akwai kanne na biyu dake zaune da matayen su anan gidan.
Ta girgiza kai.
Ta kwaso mata kaya lesussuka atamfofi , turaruka da kudi masu yawa, aka bata bokitin dambun nama ta kira daya daga cikin yan aikin tace akirawo direba.
A'a hajiya zan hau adaidai ta kin San halin mutane yanzu aga mota ta ajiye ni unguwar mu sai a fara surutu kibarshi kawai. Ta kara yabawa da hankalin yarinyar.
Ta na fita ya fito sorry mamee ina bakuwar zanje meeting Lagos ya fada yana sauri sauri.
Ta tafi , a dawo lafiya. Ta bashi amsa a takaice, ya wuce da sauri, gaba daya layin gidan gewaye yake da sojoji, ta raba can gaba tana jiran adaidaita. Motocin suka raba ta suka wuce wani mugun birki aka ci ba tare da sunyo baya ba taga mutum ya fito yau sanye yake da suite ruwan toka duk da gabanta yau sai da ya fadi amma bata yarda ya gane ba.
Ubanwa ya baki ikon tsayawa layin nan?
Ta kalleshi a wulakance ta tabe baki kayya dai, ga mutum har mutum amma *fanko* yanzu kai baka jin kunyar zagi?
Ke ya daka mata tsawa tare da shako wuyanta ita ma tace kai..... Ko an fada ma wadancen jerin gwanon abokan ka naka zasu firgitani. Tuni nasan baka iya tare fada da kanka sai kayi gayya ga katti can majiya karfi a waje ka kasa biye musu sai ni to gaba da gabanta wallahi sojojin gidanmu zansa yau suyi maka mugun duka. Ya kalleta sakaka sojoji? Ko kana wasa inyi waya?
Yasa kafa ya harbar da bokitin dambun ya tarwatse a titi ya ce sojojin gidan ubanwa?
Ta harzuka na gidan *yaya umar madaki*...........
*Maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘
💑 *AUREN FARI* 💑