Sashe 29
Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
*Ayi hakuri da kadan*😃😃😃👆🏼
*Maman Abdallah taku ce*😘😘😘😘
[1/27, 7:43 AM] +234 806 091 7227: 💑 *AUREN FARI* 💑
0⃣2⃣9⃣
......ya yi murmushi, lallai kina da kawaici da zurfin ciki.
Washe gari ya tafi Abuja.
Yaya kuwa mamee na kiranta tafada mata sai ta hau zage zage wai har yaushe madakin ya sami mata ba a fada mata ba sai da aure yazo?
Bakin ciki da bacin rai ya taso mata, bata taba tunanin zai yi aure haka da wuri ba amma ga mamee ita hakan ma ya jima.
Abinda su yaya keso ko motsi mamee zatayi ta sanar dasu, sannan basa iya tsinana mata komai sai magana da gulma.
Ga hassada, ita hassada mutane basu gane ba, ciwo ce, uwa daya uba daya ana hassada. Kawai sai dai addu'a Allah ya raba mu da kullihin musulmi da ita.
Yana dawowa bayan an sha ruwa ya ce umaimah ta shirya zai kaita gida suyi bankwana .
Jikin ta yayi sanyi.
Suna fita ya kalleta ko dai bakya son zuwa?
Me ka gani?
Duk kin wani darare,
Ta ce hummm,
Kar ki damu kedai kiyo mana addu'a tare da iyayen mu.
Wai kina ma su addu'a ma kuwa?
Tayi yar dariya kwarai kuwa.
Babana fa?
Hada shi.
Ki ce Allah.
Tayi dariya .
Yau ma anan zaka tsaya? , ya gyara parking gaskiya, kinsan manzon Allah SAW ya ce idan alheri ya sameku to ku boyeshi har sai idan ya bayyana.
Ita kadai ta tafi ya zauna yana jiranta a mota,
Sallama tayi duk suka mike ana tsallen zuwan ta, yau ita ce hada dauko kujera wai ta zauna.
Dariya tayi kawai ta raba bakin tabarma. Ta kasa boye mamakin ta. Bayan sun gaisa ta fada ma su abinda ya kawo ta kowa ya fara tsalle ana bata saftu.
Su goggo ta ciki na ciki, amma basu nuna mata ba.
Har zata tafi luba ta ce wai umaimah wanene angon?
Ango? Ta bukata,
Goggo ta dan dungureta ke ban son surutu...... A a goggo kuma fa kuna taso kusan wanene.
Ban gane ba luba.
Jiya wanene yazo wurin baba aka kaishi kauye gaida iyaye?
Gabanta ya fadi, ta tuno dawowar madaki da yan buhunna.
Uhummm kawai ta ce ta tafi.
Tana fita goggo ta ce da luba bita kigano mana ko wanene watakila mai gadin gidan ko direba ne ta samu, don duk yanda akayi jikin gidan shima yake yanda naga malam nata fachaka.
Ta dawo da sauri anya ita kadai take tama shiga gidan Alhaji yakuba.
Duk suka tabe baki.
Sauri sauri ta tarar dashi ya dan kishingida yana jin gwanja.
Ko zama batayi ba ta ce, jiya kauye kuka je?
Duk da yaji faduwar gaba kuma bai san abinda aka fada mata gidan ba sai kawai ya wayance.
Eh, ina ta so in fada miki kinga na manta.
Jiya na je na sami baba akan ina neman izinin fara nemanki da aure ma'ana ( zance ) kamar yanda addini ya tanadar kada suji wai wai a dauka ko na raina su or something like that, shi ne ya ban shawarar in sami lokaci muje kauye na gaida kowa tunda shima yana da na gaba dashi.
A jiyan am free so nayi amfani da daman na ce muje kawai ko nayi laifi?
Tayi murmushi ko daya.
Ya tayar da mota, when last kika je kauye?
Tayi yar dariya gaskiya mun dade.
Shi yasa jiyan akayi ta mamaki wai har kinyi girman da zakiyi aure?
Tayi dariya kawai.
Maimakon gida ya wuce suka siyo ice cream suna tafe suna sha.
Zaki sha ice cream saudiyya mai dadi, ta danyi murmushi kawai.
Me zaki siyo mun tsaraba?
Duk abinda kake so,
A a kawai dai kiyo mun tsaraba da choice naki.
Okay I'll try my best.
Yayi murmushi ya janyo wata leda ungo ga guzurin ki kuyi amfani da dollars sunfi dadin harka.....
A a duk ka hada kabawa mamee idan ina bukata zan karba wurinta.
Ya kalleta da kyau. *Why*?, nake ga hakan zaifi.
To ai itama ga nata nan ya fiddo wata ledar, ta danyi yar dariya yawwa to hade mana wuri daya duk ka bata.......ke ban son rashin wayewa malama.
Ta dan harareshi Kaine ba kauye don Wanda ya waye baya gardama kai kuwa kullum sai anyi musu da kai.
Ya ma rasa me zai ce mata?
Kamar ya janyota ya rungume amma ba hali. Ya dan lumshe ido, Alhamdulillah wani jinkirin alkhairi ne tabbas Allah ya karbi rokona.
Ya dan kalleta,
Umaimah duk umara ko hajjin da zance wallahi addu'ata ya Allah ya bani mace ta gari wacce zata soni ta kauna ceni badon kudi ko kyawuna ba, sannan yasa ta so mahaifiyata kamar yanda nake sonta, ta tausaya mata fiye da yanda nake tausayinta.