← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 37

Sashe 34

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

*Dinner* madaki da umaimah ba a taba irinta ba a kano. Da aka yanka *Cake* ya debo ya bata ta mika hannu aka fara dariya sai zumburo baki takeyi tana fushi ya tabe baki ya sanya mata aka dau *sowa*, wurin bashi nan ma sai da akayi daru ya kawo hannun ya kai bakin sa da kansa, ta wurga mishi harara. Abikan sa sukayi ta kyalkyatar dariya *kai madaki yau na shan harara* shamsu ya fada, bashir ya ce ashe duk kun lura.
Shagali har kusan biyu sannan aka tashi maganar ciye ciye da liki ba sai an fada ba.
Umaimah dai da ance amarya da ango su fito sai tayi tsaye, yayi yayi suyi rawa takiya shi ma sai ya basar.
A gida kuwa , su yaya bayan an tafi party suka hau sama ganin dakuna ana tabe baki,
Ta kalli jamila duk shi yayi komai 'yar kawai aka bashi.
*Hummm* ai ta raina mu kina ganin damu da banza duk daya sai su *maryam hamza* su ne gaba gaba dasu ake komai.
Haka suka yi ta gulma da korafi ko *dinner* sai da kowa ya tafi har an fara suka isa, ko wace ta ledojin ta a jaka na kullar abinda duk aka ci.
A mota suna zaune anata tafiya da mutane, tayi shiruuu kanta sunkuye gani kawai takeyi tamkar a mafarki.Ya mata rada a kunne *Ko sai na siyi bakin za amun magana?*
Kirjinta sai bugawa yakeyi.
Dabara ta fado mishi, ya dan kawar da fuska ina so in fada miki jiya da sai dai kiji mamee a asibiti...... Ta juyo da sauri *Me ya sameta?* ya sha mur hayaniyar mutane ce kawai.
Muryar ta duk tayi sanyi ta canza ta ce *Amma da sauki yanzu ko?*
To ban dai sani ba saboda yau din sau daya ma na ganta...... Ta ce hummm
Ya kusa yin dariya. Me na yi kuma? Ko ban kyauta ba dana fada miki?
Amma da ka kara komawa ka dubota ...... Ya kyalkyace da dariya.
Nan da nan ta gano shi.
Ta yi kasa da kai tana murmushi.
Ya kalleta duk kin rame kin sa ma kanki damuwa zaki zo gidan *Madaki*
Ko kuwa ramar ta an dade ba a kawo ki bane?......... Ya mu ta fi ko?
Bababa ya shigo yana kokarin tayar da mota.
Ya harareshi yi ka sauke mu na gaji da kai *Disturber*.
Suna isa, wani abokin sa ya zo suna magana ta sulale ta gudu.............
Bai kara ganin ta ba sai washe gari da yamma an fiddo ta sashen mamee tana gaisawa da mutane ya hangota lullube, har ya juya zai tafi bashir ya fizgeshi sukayi waje............😃

Ba nan na so tsayawa ba na gaji aradu😃

*Maman Abdallah*😘😘😘😘 juma@ mabruk
💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣3⃣3⃣

*NURY*😘😘😘😘 *only u!*
Chapter 34 · 0% Book details