← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 37

Sashe 17

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*maman Abdallah*

😘😘😘😘😘😘😘😘😘
[1/26, 9:14 AM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣1⃣8⃣

*Godiya ta musamman ga Bollywood addict members na gode da addu'o'i da kaunar Ku. Kamar su Rumaisa, sanah, secret writers, Hanan, khadycute da duk wadanda ban ambata ba ina yinku*😘😘

.... Ta zaro ido, yau na gama shiga uku ni umaimah, ya ajiye ice cream din da karfi ya tunkareta tayi baya baya ya hada da bango hannuwansa duka a kafadunta,
Duk illahirin gidan kowa ya mike kamar an tsira mishi allura kusan mutum hudu zuwa shidda suka hada baki..... *Alhaji umar madaki*????
Me yasa kike da taurin kan tsiya, Ke bakya tausayin kanki ko? Tayi shiru tana kyarma.
Ya daki bango *ki kiyaye ni zan wahalar da ke matukar baki sauya hali ba.*
Har ya juya ya dawo da sauri, bakwai idan ta wuce miki da minti daya gobe baki je aiki ba sai na 6atar dake sannan idan kin cika ke din mai taurin kai ce ki ajiye jakar nan kada kiyi amfani da ita, wallahi ko da kuskure baki dauketa ba sai na baki mamaki.
Ya juya ya fice yana huci.
Goggo hansatu ta kai mata wani uban duka *don ubanki bishi ki bashi hakuri kar ki janyo mana masifa matsiyaciya mai halin munafukai* ta ingizata da karfi, ashe bai fita ba zaure ya lafe tana zuwa ya fizgota tare da toshe mata baki yana magana rada rada.
Wannan dogon layin naku zaki bi? Ke me yasa baki da tunani ko kin manta motata nacan farkon layin. Idan kin bini wazai maidoki?
Ohh ni dai na bani. Wannan masifa har ina?
Tayi tayi ya saketa ya kiya, kwallan da take faman hadiyewa suka shatato.
Ya banka mata harara inda kikafi auki kenan ya juyata ta kalli kofar shiga gidan sai kawai ya ingizata *shiga maza* ya fice da sauri.
Tabi bayan shi da kallo, duk yau bai bata haushi ba, amma tana tausayin kanta.
Lokacin da tashiga an kachame rabon ice cream,
Kowa ya bita da harara, goggo jummai ta ce ke kuwa meye hadinki da *madaki*?
Tayi narai narai gidan sa nake aiki, matar data zo kwanaki mahaifiyarsa ce........duk suka zaburo *gidan sa*???
Ta ce eh, yanzu ma ita ce tasa ya rage mun hanya shine....... Shine don ubanki kikayi mishi mugun halin naki ko? Tsinanniya mai mugun hali.
Wallahi goggo ban san bokitin.....ke ar can munafuka ko baki akayi ki kawo mana mugun halinki zai barki ne? Shi mai kudi an fada miki yana da wannan mugun kudurin ai sai talaka irin ki jakka.
To kin daiji sharuddan shi idan kikayi wasa halaka ki zaiyi sakarai kuma wallahi ko cigiya.
Mai bakin jini ke duk inda kika raba sai an tsane ki anji ba a kaunarki. Kai ina ma amfanin yarinya irin ki shegiya, Goggo tayi karaf, ai idan ina fadi bekena ake gani.
Irin su shatu ne munafukai, idan an kirasu cin arziki sai su zake Suna nuna isa kuma ta banza tunda baka dashi.
Luba dake zaune tana ma ice cream cin tuwo da hannu ta ce,
Kun tuna mun wata munafukar yar ajin mu. Usaina 'Yar gidan kansila kawar mabaruka ce tare suke komai, to labuda kuma kawar mabaruka ce ta janyo ta itama taci arziki.
Kawai sai ta fara kiran ta da *mamana* ai kuwa usaina ta ringa jin dadi tana zabga mata abin arziki, shi kenan tana ganin wuri sai ta fara ma labuda bakin ciki tana gaba da ita, idan gaban usaina ce faran faran da sun kebe tayi mata magana sai ta kyaleta, ai kuwa kowa ya karto tsinanniya aka fara bincike sai gashi an gano ba sunan *uwarta usaina* ba makirci ne da kwadayi irin na munafukan mutane.
Kinji ko? Goggo ta fada, muma Allah kadai yasan abinda ake bamu bata kawowa munafuka.
Ice cream din da umaimah bata sha ba kenan ta nufi salloli.
Tana gamawa ta tafi gidan Alhaji yakuba.
Hajiya na ganinta ta ce me akayi miki kamar kinyi kuka?
Ta kakaro murmushi tayi tayi amma ta kasa sai kawai ta fashe da kuka, hankalinta ya tashi kwarai,
Umaimah ya akayi?
Ta dago fuska sharkaf, wallahi na rasa in da zan sa kaina inji sanyi.
Ya akayi?
Kin san nazo na karbi dubu biyar ko? Abinda ya faru....ta fada mata.
To shine yau ya bani da cikon wancen dana wannan watan kin gansu amma INA tsoron kai kudin nan gidan mu sunyi yawa, idan suka saba ina kai kudi da yawa ranar da ban kai ba na shiga uku saboda wani irin birkitatten mutum ne.
Ikon Allah, yaro ba mutum ba sai ya girma, duk abubuwan naku yazo da yarinta umaimah, kuma wallahi kin mun Kyan kai tabbas *da* da mahaifi sai Allah kinyi zurfin tunani da baki fada mata ba, maganar kudin nan ma wallahi naga hankalinki,
Shi kam yayi wauta da yarinta a matsayin sa bai kamata ya biye miki ba, ina shi in ke?
Ta ce *Hmmmm* kawai
Ta fiddo kudin ta mika mata shine na ce bari in zo duk abinda kika gani.
Ta karba *Au yo ai ke lissafin naki hada riba ya dora* nake ga dubu Dari ne.
Tabb wallahi baki basu sarka zan siya miki dasu.
Sarka? To ke kuma fa me zaki dauka?
Tayi murmushi wallahi bani taba miki kudi kinji na rantse. Wadancen ma suna nan zamu ajiye tsaron lalura. Daga wannan watan idan ya baki zan fara miki siyayyar kayan kitchen ina ajiyewa, ki ringa basu dubu biyar din.
Allah yana tare da maraya. Kuma kayanki nacan duk na bayar dunki saura leshi da atamfa na ajiye zuwa gaba.... Wallahi nabarwa farida nima na rantse bazan karba ba.
Ta rasa me zata ce mata .
Tayi saurin canza zancen *kuma Hajiya zata sanyani makaranta.* ta kamota ki bari don Allah, Allah har an fara mun lesson ma Dana gama fahimta zan fara zuwa. Amma tace inyi shiru ,
Nima abinda zance kenan. To Alhamdulillah ai kyawawan dabi'un ki umaimah bazaki taba wulakanta ba.
Suka sha fira, umaimah ta fito zuciyarta fes! Duk wata damuwa ta rageta.
Lokacin da ta shiga kowa ya kwanta, itama tabi lafiya, amma jiya wayau, barci sama sama tunani ya hanata runtsawa.
Goggo ce ta tada ta karfe biyar da rabi, *Barcin ubanwa kikeyi* ta kai mata duka tayi firgigi, shegiya kafaffiya duk gargadin da yayi miki shine yau ma kika gyara kwanciya? Idan ke zaki janyo wa kanki da sauki muma tana iya shafar mu ja'ira mai taurin kan tsiya. Ki tashi kiyi man wanke wanke da shara.
Haka ta yi sallah ta hanzarta kada ta makara,
Daga bakin gate ya hango shigowarta tana ta uban sauri rataye da jaka, yana tsaye sama yana kallon ta har ta shige ciki. Yayi murmushi ya koma daki ya kwanta.
Ko da ta shiga babu kowa falon tayi ciki tana gunani, masifa ce kawai ko nazo ko banzo da wuri ba ina abinda ya dameshi tunda ba jirana yakeyi ba. Idan ta gaskiya ne ya zauna falo mana.
Mtsew taja tsoki.
Tana shiga mamee ta tashi zaune 'yar halak kinki ambato wallahi yanzu nake shirin kiranki a waya.
Tayi murmushi gani ta samu ne?
*Dan kifin nan* zaki siyo mana irin na rannan kiyi mun faten dankalin ki......hahahaha lallai kinji dadin sa. Kuma kamar wasa na kwatanta dana gani a *Arewa 24*
A a da dadi kam, ki siyo mun tumatur irin manyan nan. Tayi murmushi kwadon ne ko?
Kin tuna mun da *lansir* ....ai fa ta fada tana laluben inda kudin suke, ta dan juyo nawa zan dauka don zan siyo kwakwa da danyar citta...... Dauki dubu biyar ai lissafi yanzu kika fara.
Duk sukayi dariya, kifin na nawa?
Dubu daya ko yayi kadan?
Kuma zan dauki har dubu biyar? *lansir* din da na hamsin ma mugun wajiba akeyi dashi?
Ta yi yar dariya kedai dauki hakan nasan yalo, soyayyar aya duk suna can suna jiranki, suka kara dariya.
Yi sauri ko kya dawo.
Saboda duk kasuwan kowa na sammakon siyayya saboda juma'a ce sai goma saura ta dawo, tana shigowa ta tarar dashi zaune ya hada gabas da yamma. Simi simi zata wuce ya daka mata tsawa...
*Daga ina kike?*
Ta yi chak!
Ko ba kya ji?
Kasuwa, ta fada kai sunkuye
Ya banka mata harara tare da yamutsa fuska *kasuwa?*
Ya mike , ta yi sauri ta bude jaka wallahi kaga mama ta aikeni na siyo kifi, tumatur, lansir ta fara fiddo kaya ruwan kifin duk sun bata jakar da na tumatur.
Ya zaro ido *What?*
*Umaimah kina hauka ne jakar *200+ kika sako wannan shits din*????

Barkan mu da rana
*Maman Abdallah*
😘😘😘😘😘😘😘
[1/26, 9:59 AM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣1⃣9⃣
Chapter 17 · 0% Book details