← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 37

Sashe 30

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta danyi murmushi, kaima da wata magana, su iyaye ai na kowa ne, wallahi ko na sona ko baka sona mamee ta dauketa tamkar mahaifiyata, bata kyamace ni ba, bata taba zargina ko guduna da duk wani abu nata ba, ta dauki yardar duniya ta dora mun ta yaya zan taba gudunta ko wani abu ya nemi hadani da ita,?
Wallahi ko a lokacin da bama jituwa idan bala'in yayi bala'i naso guduwa sai in tuna yanda ta amince mun sai na gwammace in hakura da takurawar taka in mata halacci.
Ya runtse ido tare da danna hon....masu gadi suka rugo ya shige da motar,
Na ga irin kulawar da kike bata, naga yanda kuke son junan Ku umaimah wallahi nima na yarda dake 100%, kuma ban taba zargin ki ba.
Ya kashe mota lokacin da kike mun gyaran daki baki ga kudade ba?
Na gani wallahi.
Ya juya ya kalleta sosai, wallahi ko buhun kudi na ajiye aka taba ina ganewa, lokacin da na kunna CCTV ina kallon yanda kike kara gyara man kudin hankalina ya tashi domin Wanda duk kika San ya shiga dakin nan wallahi sai an mun sata, shi yasa na hana kowa.
You are different umaimah, cikin dubu da kyar za a sami goma irinki.
I love you with all my heart, ni kadai nadan yanda nake feeling, ta danyi murmushi ko? Ni ma haka.
Suka fito tare da jerawa, yana fada mata yanda ya kagara ta zama matar shi. Sai dai tayi murmushi ta ce *Uhumm*
Mamee na kishin gide falo suka shigo hannuwan sa da ledijin kudin su, ita kuma da dan kingin ice cream,
Cewa zakuyi kwadayi kuka biya shi yasa naji shiru. Mamee ta fada tana ta kokarin tashi zaune,
Ya dan zauna umaimah kuma ta tafi can kusa da ita, gashi ma na rago miki nayi nayi ya siyo dake yace a a.
Ya zaro ido ke.....
Mamee ta karba tare da hararar sa na sani uwani nasan babu yanda zaki mance dani.
Ta yi mishi gwalo, mamee na satar kallonta.
Ya nunata da yatsa nafiki iyawa yarinya.
Mamee ta ce kwarai kuwa ka fita iya rowa.
Suka yi dariya ita da umaimah ya sha mur ni zaku hade ma kai?
Ta kama kunne sowie wasa ne ko mamee?
Shi yasan hakan ne,
Ya kyalkyace da dariya dole aban hakuri........ Ohhh son girma kamar maruru!!
Me umaimah zatayi ba dariya ba kaii mamee wai maruru.
Ya mika mata ledojin kudin ga guzurunku, kince kowa na ware mishi gata nan taki karba tace sai dai na hade duka na baki idan tana bukata sai ta karba.
Mamee ta kalleta da sauri , dalili,????
Zatayi magana ta sha mur ke bani son iyashege yanda nake fama dake anan ina ciwon baki ki dauki kudi kiyo siyayya haka ma can kike so inyi ta babatu?
Maza karba kada ranki ya baci,
Ta dan langwabe kai, haba mamee ni fa ce uwani, kin manta ni ke rokon kudin tsamiyar biri......... Ungo ta yi mata dakuwa, naira ashirin hamsin din?
Ta turbune fuska tare da mikewa, so kawai kike yayi mana dariya kin gwasaleni ta wuce tana zumburo baki.
Ya kyalkyace da dariya na ganku a rana....
Ta harareshi kai tafi can samna, yanzu kai matsayin ka na miji baka iya dabara da lallashi ta karbi kudin ko?.
Nasan uwani da kawaici wallahi kunya bazata taba barinta ko taga abu ta nuna tana so ba, in kuwa hannunta suke tafi sakewa.
Ya watsa hannuwa kawai kiyi ta zuwa da ita kina nunnuna mata amma kada ki bari ta siyi zinari ko zobe, kuci dadi kusha dadi please.
Sai yan kayan kyale kyale sannan kuyo mun tsaraba don ta dawo mun hannu biyu akwai rigima.
Mamee ta mike kilibabbe sai ka ce tayo ma ba muyo ma tsaraba ba.
Kai Allah yasa maka kunya ni *Rabi'atu* ta wuce ciki.Washe gari karfe sha biyun rana su umaimah aka tantsa kasa mai tsarki a *Madaki airline* an kame first class anata wulakanci da rai, da jirgin zai daga yan cikin ta suka yamutse ta kama mamee gammm tace *Wayyooooooo yan hanjina*
Mamee ta tuno umaimah fa bata taba hawa jirgi ba sai ta hau tofa mata ayatul kursiyu. Ta na warwarewa ta kalli mamee *Kut yau na jiyo kamshin lahira*
Me mamee zatayi ba dariya ba?
Madaki kuwa koda yaga tashin su sai kawai ya koma gida don fara shirye shirye saboda hatta hotel din da zasu sauka madina titi kawai ya raba shi da masallaci daga dakin su idan an kira sallah ma suna ji.
Haka garin makka,
Ko motoci akwai wadanda zasuyi jigila dasu inda duk zasuje.
Cikin kwana uku yasa aka fidda kayan gidan daman yayi order wasu daga *Italy*
Sai da aka fente gidan kaf sannan ya mayar da kayan gaba daya tsarin gidan ya canza. Su kawu keta shige da fice da matayen su tare da sauran yan aiki.
Aka kara ma gidan securities, Ga kayan da yayi order na lefe daga kasashe daban daban nata zuwa.
A saudiyya kuwa, mamee ta zama yar gata, bata taba umara mai dadin wannan ba saboda ko abinci umaimah kamar ta bata a baki. Ga ibada tunda ta gane hanya kullum masallaci karfe ukun dare ta ke tafiya sai asubah sannan mamee ta isketa , haka da suka makka.
Duk abinda mamee ta tambayeta me zata siya sai tace turare, ko a madina katuwar jaka tayo. Musamman da mamee ta fada mata cewar ba za a yi masu awo ba. Ta saki jiki duk abinda takeso ta siya.
Har sai da ta kare tayi mata magana a wani babban shago dake *Shahara mansir* uwani wai duk shagon da muka je sai kin siyi turare? Anan fa duk Inda kikayi siyayya kina karawa gaba zaki ga mafiyin sa ko wanka zaki ringa yi da turarukan nan sun isheki hakanan jakuna biyu? Haba.
Ta kaita wani shago na inner wears sai mameen ta dan fita ta bata wuri tare da ajiye mata makudan kudi nan ne ma ta yi ma kanta siyayya amma duk turarukan nan madaki take kwasar mawa tsaraba.
Domin ta rike da turarukan sa wani ko ta mance sunan tana ganin kwalbar zata tuna.
Yaya tazo daga Kaduna ta tarar da gida yanda ya koma hatta fitulu an canza su. Ta buga ma jamila waya hankali tashe kinga gida?
Wallahi abu sukeyi daga ita sai danta babu shawara don ta daukemu sakarkaru.
Haka sukayi mahada suka bude babin tsinewa mamee suna mata mugun alkaba'ai sannan sukayi alkawarin ko kwandalar su gudummuwa kuma bikin ba wani abinda za ayi dasu zasu zuba mata ido.
Madaki kuwa bai tsaya gidan shi kadai ba hada gidan malam bawa a lokacin ne su goggo suka san wa umaimah zata aura.
Gyara abinda ka gyara yayi masu ko wace ya canza mata kayan daki ga abincin hidima ga kudade azumin nan fa su basa jin sa ko kadan.
Jakunkuna set shidda yayi mata ko wane set guda Biyar ne.
Kamar lesussuka da shaddoji *Marley* ya bada aka dinko mata, atamfofin ne ya bayar *Ghana* shima wata manager sa ke fada mishi.
Bani iya lissafa lefen umaimah kawai a kiyasta ga tunani. ( don kun san wurin akwai wulakanci da rai ).
Ya bugo kati, ya fara rabawa iyaye kuma sunje kai kudi dukkan su suka dawo da son barka.
Abokan sa ko wa yaji burin sa ya san wacece wannan?
Musamman yanda sukaga madakin na rawar kafa kowa sai abin ya daure mishi kai. Tambayar daya ce *Wacece wannan lucky girl?*
Kowa kagare yake yaga umaimah.
Mamee kuwa ba ita kadai ba mutanen da suke hulda dasu a can babu Wanda baya sanya ma umaimah albarka yanda take kula da mamee wata mata har cewa tayi mamin ta bata ita danta ya aura tace ai itama surukarta ce.
Babu Wanda baiyi mamaki ba wurin saboda duk daukar su mahaifiyata ce.
Wannan ya kara sa mamee taji ta kaunaceta fiye da baya.
Waya kuwa a rana suna iya wayar fin dubu ashirin ita da madaki saboda a can akwai tsadar kira kwarai da gaske ko shi ya kirata sai an debi kudin ta haka itama . sunfi yawan waya bayan azahar da kuma la'asar sauran lokutan baya samunta tana masallaci.
Yayi yayi ta tura mishi hotuna takiya, shi kuma yana son amfani dasu ne a bubbugo abubuwa.
A kasansu tayi kawa wata barabiya sunan ta *Fatimah* kullum umaimah na gunta bayan isha'i tana koya mata yanda suke yafa gyalen jallabiya a fuska yayi kyau. Ta koya mata kuwa kala kala.
Ranar da zasu dawo baiyi barci ba.
Da kanshi yaje daukosu airport, jirgin na tsayawa motocin na karawa.
Yana ta dube dube, Bai gane umaimah ba tasha wani katon glass baki da wata matsiyaciyar jallabiya ta yane fuskar ta da gyalen tayi nadin larabawa, ya dan kawar da kai yana kara kallon kofa sai kawai mamee ta fito yaga umaimah ta mika hannu ta rikota ya zaro ido tare da hayewa matattakalar........
.

*Maman Abdallah*
😘😘😘😘😘😘😘
[1/27, 7:43 AM] ‪+234 806 091 7227‬: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣3⃣0⃣
Chapter 30 · 0% Book details