← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 37

Sashe 14

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Ni din dai ce taku mai son ku mamar Abdallah diya ga Aunty rabi*

😃😘😘😘😘😘😘😘😘😘
[1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣1⃣5⃣

Ya dunkule hannu ya kai ma wani icce duka. Taurin kan yarinyar nan yayi yawa.
Amma banga laifin ta ba nine na damu da kucaka *let me snub idiot* ya juya ya wuce.
Ka dauki tsanar duniya ka daura mun wannan jaraba har ina? Karar sa zan kai wallahi ya kuma takura mun. Dole in sanar da mamee idan bata dauki mataki ba zan hakura da aikin. Ta je gun hajiya cikin kudin ta takarbo dubu biyar takai ma goggo hansatu ta ce ga albashinta. Ta ware dubu ta bata ta boye dubu biyu, Ta ajiye biyun idan baban nasu yazo ta bashi.
Washe gari ma taki yarda su hadu, shima ya dan share abin na can cinsa a zuciya amma ya daure.
Kausar tunda akayi dan shagalin nan sai jinin ta ya hadu da umaimah taji kaunarta a zuciya gasu kusan sa'anni amma yanda komi ta ce umaimar tayi bata musantawa, ta shigo suka sha fira abin su umaimar ta ce don Allah idan ta sami lokaci tana so ta dan ringa koya mata boko don ta gane baki, tun a lokacin kuwa suka fara.
Sai dare suka dawo tare da mamee, jiyan bai sami zuwa ba sai yau. Tuni umaimah ta dade da tafiya gida.
Madaki sam yaki yarda ya kuma amince da cewar zuciyarsa ta kamu da kaunar umaimah ba tare da ta tsaya shawara da kwalwar sa ba, ya rasa inda zai sa ransa don kuna.
Ya kwanta ruf da ciki, ya runtse ido wallahi *So bai mun adalci ba* in rasa son da zan fada sai na wannan banzar yarinyar?.....kai ba so bane.
To meye? Haka ya dunga kai gauro da mari, kafin kace me ya sami attack na ulcer don zubewa yayi yana firowa sallar asubah.
Hankalin kowa ya tashi gidan masu kuka nayi masu kyarma nayi don bai taba irin haka ba. Akayi sama dashi likitanshi ya fara aune aune, nan da nan ya gano damuwa ce ta yado mishi ulcer. Mamee tayi ta jinjina abun a ranta damuwa? Ko dai don ta kawo mishi yaran nan? Nan da nan hankalin ta ya tashi.
Umaimah tun a gate ta fahimci kowa yayi zugum, saboda kullum kafin ta shigo sukan dan mata 'yar raha.
Ta iske mamee zaune idanu sunyi luhu luhu. Ta isa da gudu har ta kusa faduwa, mamah meya faru ko mai jikin ce?
Ta girgiza kai..... *madaki* ne...... Gabanta yayi wani mugun faduwa . ta zaro ido yayi me?
Baya lafiya.....ta saki ajiyar zuciya har mamin ta kalle ta, kai na firgita mamah , Allah ya raba mu da mugun ji, mugun gani da mugun aike shi kuma Allah ya bashi lafiya......ta mike . Aaammmeeenn uwani.
Ta danyi murmushi rashin lafiyar ne kika sha kuka haka? Ta Dalla mata harara. Ana kakkabe mishi file ne yayi kura ba inda zai tafi sai munga jikalle....... Bata San lokacin data kwashe da dariya ba. Tayi ciki itama tana dariyar ko kefa amma kinyi kicin kicin da rai ni duk kin kadan yan hanji.
Ta bita tana murmushi, barkwancin yarinyar yasa ta shiga ranta fiye da kima.
Abokansa lodi lodi , zandi zandi da ma'aikatan sa haka ake wuni zarya gaisheshi. Ta tabe baki, kodan kudin sa ai mutane sa soshi. Marassa zuciya biye ake....
Kwana biyu kowa ya hau yayi mishi sannu banda umaimah, yaga da gaske mutuwa fa zaiyi kawai ya yanke zuwa ya bata hakuri, a wuce wurin,
Ya sauko daddafe tana ta faman gyarawa mamee akaifa, basu ji saukowar sa ba, har sai da yazo daf dasu yace mamee....... Da dagowar kanta da faduwar gabanta duk suka wanzu lokaci guda. Idanun sa an kanta, suka hada ido tayi saurin maida kai kasa, *kai wallahi ya rame da yawa*
......bazakayi waya akawo ma abinda kake bukata ba ka sauko?
Idanun sa har lokacin na kan umaimah ya ce *Abinda nake bukata bai dauko ta waya mamee*..... Me?
Yayi firgigi to ina son dan mike kafa ta ne na gaji da kwanciya kamar ruwa ya karasa maganar yana dan murmushi yana duban mamin...... Umaimah ta mike zata bar wurin, ya ce, kowa ya je ya mun sannu yarinyar ki ta kasa zuwa saboda girman kai..... Ya salam, mutumin nan sai fita harka ta kuwa?
Subhanallah uwani, Saboda me? Zo nan amma baki kyauta ba..... Ta dan zukunna naje sau biyu yana barci.....karya kikeyi......kai jira, tsaya na ce. Koma dai menene ki gausheshi yanzu ina ji shi kenan ko?
Ta dan kaikaita *Allah ya kara lafiya* kawai tabar falon tayi ciki. Ya bita da wani kallo...... Sai kawai ya maida bayansa ya kwantar tare da rufe ido.
Ya rasa ya zaiyi duk ta inda ya bullo sai umaimah ta zulle, kwatsam bayan kwana biyu mamee taje asibiti ya rutsa ta a daki, ta ganshi sarai sai ta basar,
*Ina son magana dake* kawai ya juya. Tabi bayan shi da harara *Ai sai ganina kam* taci gaba da aikinta.
Kusan mintuna biyar ya kara shigowa, *Da ke nake fa* ta dai yi shiru. Ya nufo ta a hasale, ta makure jikin gado sai kawai tasa mishi kuka.
Duk illahirin tsikar jikin sa ta tashi yaji wani *yarrr* ga wata kasala. Yafi mintuna uku yana tsaye yana kallon ta.
Ta dan sassauta kukan abinka dama da *sharbe*
Ya rasa ta in da zai fara. Motsa baki kawai yakeyi ya rasa me zai ce mata?
Ya dan kwantar da murya, banyi tunanin abin zai miki zafi haka ba, har ga Allah bana yi da mummunan manufa ba......ya danyi shiru.
Sautin kukanta ya tsaya chak!
Na rasa ta inda zan bullo miki ki fahimceni kin fiye taurin kai, na mini tsaraba kanki ki karba, albashin ki ma kin yafe, na kira waya kinyi rejecting. *You wrongly and negatively understood me* yanda duk kika daukeni ba haka nake ba.
Yayi shiru!!!!....... Ko zata ce wani abu amma motse taki motsawa,
Duk jikinta ya dauki wani sauti,ya zukunna gabanta *Umaimah*..... Saura kadan ta saki fitsari tsikar jikinta ta yi *yarrr* gabanta yayi wani irin faduwa da bata ta ba irin sa ba ta kara makurewa tana kyarma. Wani irin abu takeji da bata ta ba jinsa ba...... Ya ruko hannunta zo muje sama inyi magana dake a nutse bana son mamee tazo ta tarar dani nan ke kuma kina kuka......ta kankame jikinta, ya kura mata ido cikin tashin hankali kada fa yarinyar nan bacin kiyayyar da takeyi mun hada tsoro na ta fara.....? Tabbas yarinya ce karama kamar yanda mamee ke fadi, to wai nima wane rashin hankali ya shigeni na biyewa mitsitsiyar yarinya kamar wannan muna *Scandal*?
Ya kara sassauta murya yanzu ya kike so ayi?
.......ka tafi kaban wuri,
Ta fada tana shassheka,
Taurin kanki keja muna fitina, yaya ina lallashin ki kina dada rikicewa?
Ikon Allah ta ce a zuci,
To bazan tafi ba idan kin ga na tashi anan to kin biyoni zuwa sama.
Bata kara magana ba yayi yayi amma tayi shiru,
Ina son ki fada man abinda duk bakya so daga gareni na miki alkwarin zan daina kuma zan baki hakuri.....lokacin ta dago ido, fuskar duk tayi ja abinka ga farar mace,
Ina so ka fita hanya ta ka kyaleni bana son ........ Ke kina hauka ne? Ya daka mata tsawa sai kawai ta kara fashewa da kuka.
*Yau na shiga uku* bai San lokacin da yace haka ba.
Ya matsa hannuwanta murya kasa kasa *Umaimah ki dubi girman Allah kizo muje sama kada mamee ta shigo, kin San Allah yau sai mun gama maganar nan koda kuwa zaki kwana gidan nan...... Na gama magana dakai na hakura kayi wa Allah ka kyaleni haka.
Kamar zaiyi kuka kinfi so kullum muna fitina kamar kaji bakya so mu daidaita?
Tayi shiruuu!!!.... Idan ke abin baya damunki ni yana damuna ina so kiban lokaci muyi maganar nan.......mamee oyoyo yara suka fara ihu daga haraba. Ya zaro ido kawai sai ya mike ya sureta kamar jaririya yayi sama a guje......
Zatayi ihu ya hada fuskarta ta kirjinsa ya toshe da kyar take numfashi.
Ya dire ta a tsakar dakinsa ya maida kofa ya rufe da key, kana hauka ne zaka kasheni?
Da'allah yi mana shiru fanko, Ashe baki da nauyi kamar na dauko karmami ke 'Har abun nan kike ja da *madaki*.
Ke nake sauraro ki fada man abinda kike so da Wanda bakya so ko ma daidaita mu daina fada.......ina son yanzu ka bude in fita, sannan bana son ka kara Shiga sabga ta.
Dalili?
Ban sani ba...
Ki fada man dalili ni kuma daga yau zan kyaleki zan kuma baki hakuri,
Saboda na tsani inganka kusa dani. Ta fada a hasale,
Maganar ta daki zuciyar sa ya matso daf da ita , tayi saurin ja da baya yaci gaba da binta har ta kai ma bango, ta runtse ido tana jiran ya shako ta Lamar kullum ya sunkuyo daf da fuskar ta ...... *Am very sorry* kiyi hakuri. Jikin ta yayi tsammm!!!!!
Ya ja baya a hankali ya nuna mata kofa da hannu.........

*MAMAN ABDALLAH*

💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣1⃣6⃣
*KINA RAINA MARYAM ALIYU YAR ADUWA. M. ALI* 😘

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH
Chapter 14 · 0% Book details