← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 37

Sashe 26

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*Good morning all*

*Maman Abdallah*😘😘😘

https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH

💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣2⃣6⃣

........... Ya waiga bai ga umaimah ba , ya fito da sauri ko tsayawa tayi , babu ita... Ya kira security din sa da suka zo tare yana tambayar sa yayi damama ya fara dube dube ya daka mishi tsawa *Are you mad*???
....... Hankalin kowa ya dawo wurin duk aka mimmike tsaye, billahil azim idan baka nemo mun ita ba a bakin aikin ka ya yi hanyar waje duk aka rufa mishi baya.
Ina yarinyar nan ta tafi?
Ya kwadawa securities din bakin gate kira suka kwaso a guje yarinya ta fita yanzu?...…. Eh yallabai ta hau mashin....... *What????* Kuna hauka ne *Don ubanku*
Ya dauko waya yayi kiran duniya taki dagawa.
Ya kira mamee kamar yayi hauka,
Mamee yarinyar nan ta dawo gida?
Lafiya, Menene?
Ta dawo?
A'a me ya.... Kit ya kashe
To wai ubanwa yasa kuka bari ta fita.... Ya zaro ido ohh my God *Anya ba ganin samira yasa ta gudu ba?*
Kaiii kishi umaimah ke gareta sosai??
Tawa ta sameni ya kara kiran nameee...
Ta ce ka ganta? Tana daga wayar.
Ina ne kika aiketa?
Gidan hajiya bara'atu tal'udu.....kit, ya kashe.
Ya kalli driver *Maza dauko mota*.....
Kadan kadan yayi tsoki, rigimar yarinyar nan tayi yawa.
Daga nesa ya hangota hannuwanta rike da manya manyan ledoji suna rinjayar ta, tana shirin hawan adai daita, ya daka mishi tsawa *Kada ka bari ta shiga*
Kawai taga mota gaban ta, tayi saurin fadawa adaidaita ya sauko da sauri... *ke kina hauka ne?* mai adaidaita ya zaro ido ganin *Umar madaki*
Ta kalleshi a wulakance daga turu na fito malam muje..... Wallahi ka tayar da mashin din nan zakayi asarar ta.
Yasa hannu zai fizgota ta ingijeshi na rantse da Allah ka taba ni zan tara ma jama'a, ta daka wa mai adaidaitan tsawa *Malam na ce muje ko?*
Sai kawai ya fado ciki muje malam..... Ta yi saurin fita ta dayar kofar ta barshi ciki kafin ya fito ta haye dan mashin......
Ransa yayi mugun baci, suka bi bayanta. Hon sukeyi amma ta ce wa mai mashin din ko juyawa kada yayi.
Ana sauketa bakin gate shima ya fito, umaimah.... Umaimah tayi banza dashi ba halin ya ruga ya rikota duk saurin sa ya kasa cin mata,
Falo ta tarar da mamee tana ganinta ta taso uwani me ya faru ne ina kika tafi?...... *Ke kin raina ni ko?* ya shigo kamar an ingizoshi.
Ta ajiye ledojin gashi mamee ta ce wadancen lesukan basu iso ba.
Tayi ciki abinta ya daka mata tsawa.....amma ko saurarenshi batayi ba tana jin ya biyota koda ta shiga dakin sai tasa makulli.
Ya yi bugun duniya taki budewa.....
Mamee na jin su tayi zaman ta falo tana fada, *Yara kamar kaji* kullum cikin masifa mtseww.
Ya dawo kamar zautacce mamee zan batawa yarinyar nan rai bana son raini, kinga yanda ta wulakanta ni bakin titi tabarni cikin adaidaita, mun shigo ina magana ta mayar dani sakarai, a gaban ki kuma yanzu kinga ta rufe kofa fa....
Me kayi mata??
Ya buga tsoki kawai kishin banza ne na rashin dalili, Samira sardauna ce na tarar office daga gaisuwa ta gudu.
Au samirar tazo kasar ne?
Nima ganinta kawai nayi.
Ya zauna bisa kujera *Gaskiya mamee ki fadawa yarinyar nan*
Ta kalleshi me?
Tasa ma ranta hakuri saboda yanayin harkokina da ya kunshi kowa jiya fa *Uche* ta kirani a waya wallahi yarinyar nan ta nemi birkicewa. Me ta dauke ni ne? Mtsew...
Ni zan fada ma uwanin haka? Tabb lallai kana da sauran aiki.
Ta mike ka fidda ni cikin wannan maganar ma can Ku ta shafa.
Mamee.... Kawai ta yi ciki.
Kiran sa kawai akeyi a waya ya kasa dagawa, banda sakonni. Mamee ta ce bude uwani nice,
Mamee na shiga ta nemi maidawa ta rufe ta kalleta tana yar dariya keni tsaya fita ma zanyi kayan da kika dankwarar man dasu falo na kawo. Ta ja baya ta kasa ko murmushi, dadi kamar mamee ta goya ta ganin kishin madaki haikan a wurin ta.
Cikin zuciya ta ce lallai uwani kin cika *Diya* zaki gyara man shi da alama.
Don zanga inda za Anyi *So* da zafin rai. Har karo yakeyi da namee zata fita yana kokarin shigowa, ta kalleshi kamar ta kyalkyace da dariya amma ta basar, ja'iri hada alhakina don iyayenka, nan na dunga kawo maka yara kana gwasaleni, ta fada a zuci ta wuce ,
Umaimah na ganin sa ta zauna bakin gado ya karaso zai kamata tayi saurin wawuro wata flower ta glass dake bakin gadon mamee, *Na rantse da Allah ka kuskura ka taba ni zan maka rauni*
Ya yi turus, ta kalleshi a wulakance, kallo da yafi tsana a rayuwar sa fiye da duk wata kalmar ta muni da zata furta,
Wai kana mun daukar sakarai? Ko kuwa kana mun daukar makwadaiciya wacce zata bika saboda dukiyar ka?...... What are you talking about?
Ya daka mata tsawa....ita ma ta hayayyako mishi.
Bani son ka wallahi yau na tsaneka bana kaunar ko ganin ka a rayuwata.
Mtsewww haba no wander ba da aiki sai ka kai hannun ka jikina ashe halin ka ne ko wace yar iska tabawa ........ *Ke* .....ya daka mata tsawa ..... Ita ma ta tace .. *Enough* tare da mikewa tsaye ko ka fita harka ta ko kuma na bar gidan nan bari na har abada, kasan dai na isa shari'a ko?
Yaga da gasken gaske yake sai ya fara rokon ta *Umaimah please let me explain*...... *Explain what?* ta katse shi.
Maharramar ka ce? Ni kaina na fada maka bana so kana taba ni ko kuwa ya hallita?
Zai yi magana ta daga mishi hannu *Wallahi idan baka fita kaban wuri ba zan bar ma gidan gaba daya*
Dole ya fita,
Ta buga tsaki, duk ya fita ranta, bata kaunar ko ganin sa.
Samira child hood friend din sa ce, sun shaku matuka, yana bala'in shiri da ita yarinya ce natsattsiya a kasar London tayi aure can kuma take da zama mijinta ya rassu amma bata dawo Nigeria ba saboda aiki da takeyi, yaranta biyar, babu wani abu tsakanin su, duk Wanda yasan madaki yasan samira.
Mamee bata san fitar shi ba, yana zuwa office ya tarar samira ta bar mishi note na wulakanci saboda ta kira ta kira bai dauka ba kuma ta tura text ba replay.
Ya rasa abinda ke mishi dadi a rayuwar sa, komai ya jagule mishi duk Wanda ya tunkare shi sai bala'i.
Washe gari aka tashi da azumi.
Abu kamar wasa sun kwashe kusan kwana hudu umaimah tayi wuri ta kyaleshi, bata daukar wayar sa bata zama duk inda tasan yana nan.
Yana kwance sama ya kira taki dauka, ya ce wannan yarinya da bakin kishi take, tama ki saurara ta taji uzuri na. Mamee taki tasa baki nayi rokon duniya ta ce kar na kuma yi mata maganar ma.
Ya runtse ido kawai dabara ta fado mishi ya tura mata text.
*I know that there is no forgiveness for the kind of mistakes I do. But if you can forget my mistakes and give me a chance, I'll make everything as good as new. I'd start everything all over again and make you happy.* Tana ganin message din ta kashe wayar ta ya kara tura mata wani yaga pending.. Yana kiran wayar yaji ta kashe,
Ta harari wayar *Wallahi sai ka gane kuren ka* kai taba jikin mace baka dauke shi bakin komai ba?
Ban iya wannan iskancin.
Ko aure na ya yi wannan wata rana ya tabo jikin wata yaji tabshi lokacin nawa ya taurare banza zan zama.
Kishin yarinyar nan yayi yawa, daga *Hugging?*...... Kai na gamu da gamona ni madaki, problem din ta gama gane na mutu kanta,
Ya tashi zaune, kaii..... Lallai , in ba umaimah ba wace yar iskar yarinya zan ringa bi tana mun wannan wulakancin, wai ni madaki nake ba mace hakuri tana mun tsawa a kai.
Mtseww *I hate this condition* ya dafe kansa.
Ta tsaneni ko ganina bata son yi? Ga mamee na sane ta zuba ido?
Ya kara tsoki, wallahi zuwa zanyi ayita ta Kare na gaji, ita bata da tausayi ne?
Ya sauko sai kawai ya hangota ashe mamee ta aiko ta,
Tana hangoshi ta juya zata koma ya karaso da gudu ya tari gabanta, ki dubi girman Allah ki saurareni umaimah .....zatayi magana ya katseta, ,,... *Girman Allah na ce*
Tayi shiru. Haba umaimah wannan kiyayya haka ko lokacin da muke tsahin hankalin ma bakiyi mun haka ba ballatana yanzu da muke son juna kawai dan kuskure ne da za a iya gyarawa..... Ta kalleshi *Dan kuskure*
Yayi saurin daga hannu sama, *Babbar matsala* ce afuwan.
Wallahi samira babu wani abu tsakanina da ita, kinji na miki rantsuwa ...... Ni na ga haka tunda ka mance dani ka mamuke ta,... Kamar zaiyi dariya ya dai tsuke, shin ai don na hugging din ta ko?
To wallahi bazan kara ba, yanzu haka na rantse da Allah ko clerks dina tsoransu nakeyi.
Tayi mishi banza, ya nuna mata kujera don tsoron tabata yakeyi ki zauna ba don ni ba don Allah...... Ta zauna kanta gefe tasha mur,
Ya ce kut, cikin rai.
Ya fiddo waya duba ki gani text din da tayi mun ko a ranar sannan tabar mun note office hada zagi na rantse da Allah baki bina bashin rantsuwa umaimah ban kulata ba har yau.
Ko kirana akayi yanzu naji muryar mace gabana faduwa yakeyi . ya kamata ki sassauta man saboda akwai huldodin da dole dasu nakeyi........ Na fika sanin haka, don yanda ka saba taba jikin mace bazaka iya ko wace hulda bata ba........
Innalillahi sharrin da zakiyi man kenan? ..... Ni na gani da ido na.
Ta taba wayar gari nan gidan baka dankeni ba?
Haka idan kaje office ka dunga rungumar mata sannan ka dawo nan ka dosa dani ...ta kalleshi na maka kama da *Yar iska?*
Ya zaro ido umaimah ki fahimceni.....wallahi ban fahimtar ka, ni bakai man ba.
Ta mike tsaye ina rokon ka ka ajiye maganar so mu ringa mutunta juna. Wallahi bani iya auren namiji mai hali irin na ka....... Ya tari gabanta idan na taba rike wata diya mace bayan ke Allah ya tsine mun, sai kuwa samira tun yarinta idan mun hadu zamu........ Zaku kadaddabe juna.
Ya langabar da kai, *Kiyi hakuri* in shaa Allah na miki alkawari hakan bazai kara faruwa ba.
Zatayi magana ya hada hannuwa *Na tuba* kiyi hakuri na kai karshe wallahi na horu, ba zan kuma na please........
Ta kawar da kai *Ya wuce*... Ya saki wata sanyayyar ajiyar zuciya har sai da ta waigo ta kalleshi ya sakar mata murmushi...ta kara tsuke fuska.
Ya zauna taimaka ki kawo mun ko tea ne inyi buda baki, ta kalleshi da sauri......
Kina mamakine?
Wallahi bana sahur bana buda baki kullum daga dabino sai madara nake sha.
Ya langwabe ai na ga *Bone* kwanakin nan..... Ta wuce shi kawai.
Shiru shiru mamee ta fita taga lafiya kawai taji maganar su falo sai kawai ta sadada ta koma,
Ta zubo mishi farfesun kaji da fruits salad nan da nan soyayya ta tashi, da ya kawo hannu zai kamota sai ya tuna ya basar .......
Ana tsoron mu nida iya, inji diyar mayya......😃😃😃😃
Suna nan sai dai kawai sukaji liman ya kwala kiran sallah....Allahu akhbar....
Chapter 26 · 0% Book details