← Book details Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 37

Sashe 11

Auren Fari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

..... Yau ni naga bala'i ni umaimah, wannan jaraba har ina? Nikam na debo ruwan dafa kaina.
Kullum abu daya yaki ci yaki cinyewa, kai ina amfanin abinda baya wucewa a rayuwa?
Ikon Allah ashe ya san sunana tsabar wulaknci ne da gadara yasa yake kirana da *ke* ko *wannan yarinyar* Mi zanyi da wata jaka? Nasan menene a ciki? Duk girman jakar nan ya ce in dauka. Tabb da alamar tambaya. Bacin daukata sakarai da yayi ina jin hada rashin wayau ma duk babu yake tunani.
Allah gani gareka, Allah kadai yasan gobe me zan tarar ni umaimah. Ka hana kanka zaman lafiya ka hana kowa?
Ta tuna idan mamee ta aike ta gidan su kawu yanda take tarar dasu cikin nishadi da walwala amma idan suka shigo bangaren sa kowa jinin sa kan akaifa.
Tana son fita harabar gidan amma shaggun ma'aikatan nan zasu ringa mata dan kira suna *fine girl* masu jin hausan kuma *yar Fulani*...
Kiri kiri gida ya koma mani kamar wani sansani, kullum zan tafi ina zullumin me zan tarar ga madaki idan yana gari.
Wani lokacin kamar yana da tausayi amma wani lokacin ya zamo mugun karfi da yaji shin ko dai yana shaye shaye?
Amma kuma ai baya layi da magagin dasu yaya Abba keyi ko kuwa tasu kwayar ta masu kudi kwalwa kawai take tarwatsawa?. *NI KAM UMAIMAH NA SHIGA UKU*
Da gudu kowa ya fito masu aiki da mamee. Yayi tsaye yana faman kallon kofa.
Duk sukayi turus!
Kai lafiya? Mamee ta bukata,
Ya kalli yan aikin kuyi *clearing* ya haye sama.
Mi ke damun yaron nan ni jikar buzaye? Abinda madaki kullum kara hauhawa yakeyi fa.
Yarinyar nan ta maidani sakarai ko? Lallai bazan dauki iskanci ba. Wai tana nufin zanyi asara ne? Ya kalli jakar tabb...
Duk yau ya kasa cin abinci.
Wannan masifa da me tayi kama, yarinya karama ta hanani sukuni? Tunda Allah yasa yarinyar nan ta shigo rayuwata zuciyata ba kara samun sukuni ba.
Wai duk me ke haddasa mana wannan rashin fahimtar? Nida ita wake da laifi? Ya buga tsaki ita ce ,
Tana fama da rashin kunya ni kuma bana daukar raini.
Zan saisaita mata zama, ya tashi yayi alwala ya nufi masallaci nan cikin gidan sa.
Takwas da rabi ya shigo zaune take da baki bai ko kalli inda suke ba yayi hanyar sama.
Kai nake jira, mamee ta fada ,
Ya waigo cike da kulawa fuskar nan tashi murtuk, ta mike tayi ciki alamar ya biyota.
Yan mata ne su uku ya kara kawar dakai duk suka bishi da kallo.
*Yaro matashi mai tashen naira*. Kirarin sa kenan a gari. *madaki nada kyau* shi ba fari ne ba amma saboda hutu, kudi da kuma jin dadi yasa farat daya baka iya gane hakan. Irin kalar nan gareshi ta bakake mai kyau watan mai haske kamar chakuleti. Amma yana da sumar kai mai laushi da tsawo. Kullum tana kwance luf luf tana sheki da kamshi.
Dan gayu ne na karshe kuma miskili na kin karawa.
Ya kasa yin budurwa saboda mugun miskilancin sa ya ce babu macen da zai yi wa bauta ko ya bita yana lallashi bare uwa uba har ya mata laifi ya bata hakuri. Duk Wanda ke tare dashi yasan haka,
Mamee ta kalleshi cikin ido. Gaban sa yayi mugun faduwa yasan doka ce zata saka mishi ko umarni ko kuma wani gargadi mai amfani.
Kaga yara falo? Kaje ciki ka ga wacce tayi ma duk na san halin ko wace ciki da mahaifanta, tunda ka ce baka son auren zumunci. Sannan na baka dama har kishi uku kana *failing*
Ya kalleta namee ....wallahi bazan kuma sauraron ka ba, kaje kayi abinda nace kada ka hadu da fushi na. Haba madaki ya zaka maidani sakarai kana nufin baka aure ko me? Ko kuwa matan banza kake bi namiji cikakke kamar ka bai yiwuwa ace har yau bakaji son ko wace mace ba........ai kinyi sauri ne mamee.
Ta daka mishi tsawa nayi saurin don iyayenka, kaje kayi abinda na umarceka kada ranka ya 6aci.......
Ba kince kin san halin ko wace ba? Kije duk wacce tayi miki cikin su shi kenan......yasa kai ya fice kamar ya kurma ihu don takaici.
Tayi kasaké...!!! Wannan taurin kai na madaki ya zanyi dashi?
Ransa ya gama kara jagulewa, tayi wayar duniya ya sauko yaci abinci yace ya koshi. Haka ya kwanta ga azababben tunani ta ko'ina ga yunwa.
Haka ya kwanta har safe ga cook din sa baya nan yayi tafiya,
Karfe takwas ta iso, mamee tayi kiran duniya yazo ya yi kalaci amma yaki daga waya,
Duk tunanin ta fushi yakeyi, har karfe goma bai sauko ba,
Ta kwala ma umaimah kira, tazo.
Hau sama ki kira man umar.
Hmmm kawai ta fada ta juya. Don bata san me zata fadawa namee ba.
Shin ai duk masifar sa bazai dauki raina ba ko? Wata rana sai labari. Ita kadai ke sabbatu, tana tafiya, gabanta na dada faduwa.
Ta kwankwasa har kusan sau shida ba ayi magana ba. Tayi tsaye tana tunani kada ta shiga a kara yar gidan jiya, har zata juya sai taji wani irin kakari daga ciki. Ta saurara da kunne tabbas shine. To lafiya? kakarin amai taji ta Murza kofar taji ta a datse, ta sauka da gudu ta nufi dakin mamee tana kwala mata kira mamah! Mamah!! Mansura ta tareta ta zagaya baya fa.
Tana jin haka ta yi hanzarin zuwa ta dauko mukulli ta kara hawa saman da gudu.
Kwance yake saman kafet cikin amai ko in ce kumallo, gashi yana fama da ulcer. Ya duke yana ta murkususu ya dafe cikinsa.
Ta doka salati ta nufi inda yake ta dago shi *baka lafiya?* da kyar ya daga kai *Bani wani abu in ci please*
Ta sakeshi da sauri ta kara yin kasa, duk an shirya kalaci a table ta hado tea da madara ta zubo farfesun koda ta hanzarta.
Yana inda ta barshi. Ta ajiye kayan ta kamashi zaka iya tashi? Ya girgiza kai alamar a'a. Ya hakuri ka daure bana iya dagaka ta yaya zakaci abinci cikin amai?
Ya daddage ya dafata zai mike ta durkushe duk suka fadi gefe. Ta ce wash!
Ungo sha tea din. Ya kasa motsawa. Ta lura tabbas ya gama galabaita sai kawai ta ringa diba tana bashi.
Yaushe rabon da ya sha tea da madara?
Ta dunga dura mishi da spoon yana sha yaji dadin da ya rabu da ji a rayuwar sa.
Tana bashi tana faman sannu.
Ya shanye duka, ta dauko naman shima ta fara bashi, ganin ya fara farfadowa ta kalleshi kamar hada yunwa ma ciwon.
Ita ce ma ba ( kamar ). Jiya banci komai ba gashi ina da ulcer.....ulcer? Ai wannan wauta ce ta fara bambami, gashi ka garkame daki ai da kayi mussai yau.
Ya kalleta sai ta bashi dariya, yayi murmushi kawai.
Wai me ma ya kawo ki dakina?
Ta dalla mishi harara nazo *ceton ka* ya dan tureta zai tashi yayi luuuu ta taroshi da sauri ya fizge ta bishi da kallo. Me ya kawoki dakina?
Mamee ke kiranka.... Kada ki fada mata abinda ya faru.
Naji ta fada tare da mikewa. Ya tashi da kyar ya dauko magani yasha.
Ta tafi ta mayar da kayan . ya sauko ya nufi dakin mamee yaji kiran.
Umaimah kuwa tana kai kayan ta koma saman ta goge aman ta gyara mishi dakin tasanya mishi freshener ta canza mishi bedsheet sannan ta shiga kewaye ta wanke mishi.
Tana gamawa ta tabe baki. Allah yasa yau ya zame mishi ishara ya rage zafin rai.
Tana sauka shi kuma yana hawowa, ya kalleta sama da kasa, ina kuma kika je? Me kike mun a sama.
Ta kalleshi ci ke da takaici, abar hali aci me? Gama rasa me zata ce mishi kawai ta raba shi ya fincikota ya hada da bango.
Bana hanaki ina magana ki gudu ba?
Ta kalleshi kai wane irin mutum ne?
Irin ki ne.
Ta girgiza kai ni ba haka nake ba........ Ke bakinki bai mutuwa ko?
Ikon Allah, ta fada.
Saboda bana son maganar zan tafi ka dawo dani shin me kake so?
Jiya kin mayar dani sakarai kin pretending na shiga ciki kin gudu ko?
Kin gwammace in rike albashin naki da ki dauki jakar can ko?
Kwarai kuwa na hakura da albashin. Don haka bani wuri in wuce.... Ta ingijeshi ya daki karfen bene ta baya.
Tana yin step daya ya murdo hannunta ya maidota da karfi jikin sa ya maida hannuwan sa duka bayanta.
Wani takaici ya diran mata sai kawai ta dora kanta a kirjinsa tana kuka.
Jikin sa yayi mugun sanyi, yayi shiru!!!... Tayi mai isarta tukun, ta dago, yayi saurin sakin ta, ta kalleshi idanu jawur, na rasa yanda zanyi da masifar ka, munzo na baka hakuri na daina shiga sha'anin ka, kullum da abinda kake tokalowa.
Bana son hadaka da mahaifiyar ka amma ka kasa ganewa. Kwallah suka shatato mata.
Na gaji na gaji. Wallahi zakayi dana sanin wulakancin da kayi man yanzu. Bani kwadayin kudin ku. Ina yiwa mutuncin mahaifiyar ka ne.... Kuka yaci karfinta da gudu ta sauka. Ya bita da kallo kaman ya kamota ya bata hakuri amma baya iyawa.
A sanyaye ya hau sama, turus yayi ganin yanda dakin ya koma, ya zaro ido innalillahi yarinyar nan ashe gyarawa tazo tayi. Ya dafe kai *ohhhh my God* jikin sa ya kara yin sanyi,
Umaimah kuwa tana baya ta lafe tana ruzgar kuka, tayi mai isarta, sannan ta goge fuska, *In shaa Allah bazai kara ganina ba* ko mamah ta aikeni zan San dabara amma wallahi bazan yarda ya kara sanya ni a ido ba. Kuma na rantse da Allah sai ya bani hakuri akan wannan wulakancin.............. Turkashi.

*MAMAN ABDALLAH*

MU KWAN LAFIYA😘😘😘
[1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣1⃣2⃣
Chapter 11 · 0% Book details