← Book details Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 26

Sashe 25

Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daya sukazo kano direct asibiti akai dasu Dan abasu kulawa *To fans sai naji comment dinku wallahi comment yai sanyi fa yai kasa fans insha Allah gobe zan Gama muku arnan daji inaso kowa ya gayamun darasin daya dauka a ciki nice taku a kullum a Koda yaushe* *Feedyn bash* [10/23, 2:33 PM] Ummu Subai'a ARNAN DAJI *NA* *FAREEDA ABDULLAHI* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation _*Assalamualaikum wannan novel din sadaukarwane ga mahaifiyata inafatan addu'oin da akai Mana nida ke da zuri'a ta Allah ya amsa Mana nagode nagode masoyana Allah ya bar kauna ta har abada*_ _*Alhamdulillah Allah na godema da baiwar dakai mun Allah nagodema da basirar daka bani Allah ya karawa annabi tsira da aminci su tabbata agare shi alhamdulillah masoyan dasuka bibiyi littafina tun daga farko har zuwa karshe da wayanda suke mun comment naji Dadi nagode sosai Allah ya Kara Mana kaunar Juna Allah yasa kun anfana da abunda yake a cikin wannan novel nawa Allah yasa ku kaunaci novel Dina nagaba fiye da wannan arnan daji sai mun hadu a sabon novel Dina me suna fachalata *BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DA SUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI INA GODIYA MASOYANA* *BOOK 2* *END END END* 125-130 Take suhail ya Kira anty saudat yace Duk sutaho dasu ramatu asibitin aminu Kano suka shirya suka tafi ya Kira haleema suzo duka da Yara tana kuka take Gaya Masa ansar ba lafiya sai sankamewa yake dama asibitin zamu zo kuyi sauri ki kawo shi Dan Allah tana kuka bazata iya driving ba sai driver ne ya daukesu sai asibitin aminu Kano abun na ansar sai gaba yake yaran duka kuka suke yaro yayi Kore Shar hankalin haleema ya gama tashi Duk addu'oin da suka zo bakin ta today Masa take a haka suka karasa asibitin suna da gudu suka dauke shi sai emergency Duk sun chan dama a chan aka kwantar dasu anata samu su ruwa Ana Shirin shiga da Indo Aisha theater hannunta Nan suka karasa aka karbi ansar Nan aka Fara kiciniyar dubashi Ana lamunde taga jikokin ta yayan suhail taji Dadi tayi farin ciki burin ta ya cika ta cika burin mijinta yayanta sun rayu cikin aminci anan kafin ashiga da ita tabawa yayanta ahaji Ibrahim labarin Duk abunda ya faru bayan rabuwarsu shima yabata labarin shi ya Kuma Bata labarin dukiyarsu a yanzu haka shanunsu Ana yin youghourt fresh milk da man shanu komai nata yana Nan Taji Dadi ta godewa yayanta sun jinjina hukuncin Allah shiyasa akeso mutum yakasance me temako gashi ya raini dansa jininsa cikin aminci daya azabtar dashi dayaiwa kansa Nan tadingaiwa hajiya godiya yayana naji labarin kaje nemana eh tabbas naje a lokacin Dana shiga garin sarki yasa aka kaini kurkuku nazama daya daga cikin wayanda za'a yanka inata addu'ar Allah ya kawon dauki ya kubutar Dani A wata ranar laraba ne Allah yaban sa'a me gadina yasha burkutu ya bugu dama ya manta ya budeni yaban abinci shine na salallaba na gudo nayanki daji naita gudu cikin ikon Allah na billo wani gari beguwa kwana na uku agarin duk da Suma arna ne Amma basuda mugun Hali daga ranar bansake komawa ba a garin na samu labarin ai duk bako kashe shi ake shine nasa araina kema kin mutu Ashe Allah yayi kina Raye Tai murmushi Ina Raye Yaya Amma nakusa mutuwa yasalam ya fada ya toshe bakinta karki Kara fadar haka insha Allah muna Raye Nan da Nan aka shiga theater da ita tana ta daga murmushi Chan sai iya ta farfado Nan suka koma kanta suna hada ido da hajiya suka saki ihu habi tabita da kallo kawai Dan ita iya Bata santa ba wannan habi ce Yar gidan kawuna da suke zaune kauyen fata ya tafi cirani da shi da matarsa shekara kusan talatin Kenan tun muna Yara ba'a Kara ganinsu ba ko Wanda yaji labarinsu ba'a samu ba Nan suka fashe da kuka dukansu tabbas nice nice suka rungume juna Allah nagode ma Dana hadu da ahalina ban mutu ba Dana Mohd ga danginka wannan Yar uwatace Nan suka kacame kamar gidan biki sai da aka koresu tukun daga dakin dukansu Nan da Nan hajiya tafara Kiran waya tana sanarwa yau taga habi Yar gidan madibbo murna danginsu Nan da Nan sukace zasu zo Kano gobe gidanta sugana da Yar uwarsu shekara kusan talatin Suna zaune a waje haleema kawai kuka take tana tunanin ansar yaron sun shaku kullum Yana manne da ita kawai taga amwuce da wata kamar Jeddah Nan da Nan ta mike tabi bayansu zuwa dakin sai da ta kura Mata ido ta ganeta mutumin sai hawaye yake likitane shima Ina sauri anmun waya Ina da emergency patient bantanta ba kawai kwashe ta nai nadauka ta mutu Ashe da ranta buguwa Tai ta Suma Bata ji ciwo ba kanta ne kawai ya fashe Amma abun da yaban mamaki anyanke Mata nonuwa toshe bakinta tayi kawai ta boye kukanta ta Kara matsawa itace Wallahi ihu tasa Yar uwata ce kishiyata ce wallahi nan da Nan suka juyo kanta kinsan tane eh nasanta kishiya tace alhamdulillah dama Yan uwanta nake nema Nan ajiyar zuciya sukaji ta sauke haleema ta matsa kusa da ita ta bude idonta fes akan ta Da gudu ta rikota tana gunjin ihu haleema ki yafemun ki yafemun Ina hajiya nina kashe suhail da hannuna ninasa kanina ya kashe shi kuka haleema take tana tausauya wa Jeddah mace har mace bakyan Hali dubi duk ta haukace haleema na tsaye aka turo gawar ansan likitan yace kece maman wannan yaron ko ta gyada Masa Kai Allah yai masa cikawa inalillahi wainna ilaihirraji'un abunda ta iya fada Kenan ta karasa ta dakko gawarsa tana kuka ta ajiye shi a gefen Jeddah kin kashe danki da kanki tun randa Kika zo gidana yaron nan be Kara lafiya ba Kuma shi kadai yaci abincin Nan me kikai sa ihu tasa ta rungume shi ansar ka tashi karka mutu Dana inasanka ku kadaine kukai ragowa a ahalina baka mutu ba wallahi ka da kaina saiga suhail ya shigo Yana neman haleema yaganta a tsaye gaban wata mata ya Fara kiranta my dear kizo su mom zasu tafi gida kafin afito da ummata daga theater cike da kuka ta juyo karaso kaga abun mamaki Yana zuwa yaga wata Mata a yankwane Kai da kirji nade da bandage nonon ma Babu ya hango gawar dansa da gudu ya dakko ta likitoci duk sunyi cirko cirko suna kallonsu harda masu vedio a waya Suma ne kawa Jeddah batai ba suhail ta ambata sai yanzu ya ganeta a firgice ya kalleta Jeddah kece haka lallai muguwa azzaluma dama karshen maha'inci kenan kin rabani da iyayena da yayana da matata kinsa na aureki ta asiri karshe Kika nemi kasheni Allah ya Isa tsakanina dake haleema ta toshe Masa Baki ka yafe Mata kaddarar ka Kenan karka manta da Bata nemi Kashe ka ba bazaka hadu da ahalinka ba nan ta Fara bashi hakuri sai haleema ta tafi da sauri ta Kira alhaji da hajiya danya kekashe kasa akan baze yafe Mata ba Nan sukazo suka ga ikon Allah Nan ta Fara basu labarin auren datai sun girgiza da wahalar data Sha matan sai kuka suke hardasu ramatu dama gata gwanar kuka Kowa ya tausaya Mata Nan daddy yasa Kowa ya yafe mata Kuma sunyi alkawarin neman alhaji malamalai da kungiya su insha Allah za'a bi Mata hakkin ta Nan tabawa suhail number din account number dinta da komai Tai Masa kwatancen gidan hajiya hafsa Dan komai nata Yana chan da takardun gidajen ta yai Mata alkawarin karbowa Ana haka likitoci sukace abasu gawar ansar zasu kaita dakin daza'a ajiye shi kafin ai cike cike Nan ta rukunkume Dan Wallahi karya ne Yana da Rai dakyar aka kawace shi tana gunjin kuka Kowa kuka yake Dan tausaya Mata asra ce tazo ta rungumeta momy Kara rungume ta kiyafemun yata na mallaka Miki duk abunda na mallaka Amma na halal Banda na Haram kuka take sosai chan Kuma sai ta Fara dariya a'a sai suhail ya kwace asra tuni ta diro daga gadon kamar ba Mara lafiya ba Ta Fara yage kayanta tana tonawa kanta asiri asibiti yazam gidan biki Kowa sai kallonta ake Ana Allah wadarai Dame Hali irin nata Nan ta Fara tsigar gashin gabanta tanaci hauka tuburan Nan da Nan ma"aikatan asibitin suka kamata a ka Sanja Mata daki aka kulleta tamau Nan da Nan akai refer dinta zuwa dawanau kome akasa Mata sai ta yage shi Allah yasa mi kyakykyawan karshe ba irin nasu Jeddah ba kuka Kowa yake a wajen harda yarta data Fara wayo kunya kawai takeji idan akace ga yarta Datai saura sai ta fashe da kuka tace haleema ce mamanta ganin haka mazan sukace duk akai matan gida shikansa suhail dauriya kawai yake kodan darajar yayansa data Haifa Masa karshen Jeddah haka yazo chab dijan Allah yasa mudace suna tsaitsaye aka fito da Indo Aisha Amma Anja zani anrufe Mata fuska daddy na ganin haka ya fara kwalla yasan Babu Aka ajiyeta gabansu likitan ya girgiza musu Kai sumewa suhail yai a wajen nan Kai maza aka Fara bashi temakon gaggawa uncle da daddy ne suka yi duk wani cike cike aka Basu gawar Aisha data Ansar Nan sai ga suhail da kafarsa ya fito be warware ba Amma haka ya fito suka taho gida akai musu sallah aka kaisu gidan su na gaskiya Ramatu fadeela subai'a kuka kamar ransu ze fita har ririkesu ake to yaza'ai kullu nafsin za'ikatul maut haka suka hakura suka dangana Basu da kowa yanzu sai suhail da ja'e da iyar ja'e to gasu daddy haka aka share makoki bayan arba'in daddy ya Kira malamalai aka Raba dukiyarsa kamar yadda Allah yace shi kaso biyu ita uku aka rabawa ramatu da suhail Suma sukaiwa Yan uwansu alheri dan ba karamar dukiya suka samuba bayan wata uku aka shirya gagarumin biki Dangin hajiya sunzo sunga Yar uwarsu da danta sunyi murna sun tafi da ita da Ja'e Ja'e taga dangi ta Ja'e farinciki kamar me yaga danginsa Dan duk sunfito daga kauyen fata sun koma garin Jos a chan
Chapter 25 · 0% Book details