← Book details Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 26

Sashe 10

Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ita acire Masa ita a kwakwalwarsa baze Kara tunata ba sai dai idan ya ganta Iyayen mijinki Kuma zasu zo Dan sun gani komai suzasu tafi da ita Amma zami musu rufin bakin daba zasu taba tunawa mijinki itaba duk abunda zasi miki karki damu lokaci yayi dazaki mallake shi ke kadai baze Kara kallon kowace mace ba duk wadda ya kalla ze kalleta ne a matsayin jaka hhhhhh nagama dake kuka take katitir Dan Allah katemakeni wallahi banasan ta haihu dashi na rokeka ka kashe ta kome kakeso zan baka Yaya uku maza Ni kima mace mezan tsira dashi na tabbatar kafin na kamota sun mallake dukiyar nagama magana ya daka Mata tsawa kisa a ranki basu aduniyar bazaku Kara ganin suba sai sannan hankalinta ya kwanta yauwa boka har naji Dadi million guda ta dire Masa shikansa yai mamaki Amma be nunaba sai kuma ke uwar banza danki kikeso ya shiryu baze taba shiryuwa ba ahaka ze mutu zan dai Baki layar sabani bashi ba kwalawa har ya mutu hahaha ya bawa jeddah nata magungunan yabawa ummanta layar ku tashi ku tafi nagama daku gafalallu ya daka musu tsawa da gudu suka fito Suka ja motarsu suka tafi gida sai wajen 1 suka shigo kano ta sauke ummanta ta wuce gidan a kofar shiga side dinsa ta Fara zuwa ta barbada maganin da aka Bata cike da murmushi ta koma bangaren ta ta Kara zuba wani daga Nan ta shige ciki tayi wanka ta fito ta koma bangaren suhail tana doka kofa cike da bala'i kufito munafukai hankalinsu yai masifar tashi su dukansu a bacci sukaji dukan kofar a zabure yace buya bara naje da sauri ya bude mata tana Ina wafa ba kowa ban waje ya tsaya ta fisgoshi Yana taka maganin yaji kansa na juyawa ciki ta shiga daga ita sai best da zani ta Fara finciko ta gashin ta ta damko har harabar gidan nizaki ciwa Amana dama cikine dake kike boyewa wannan cikin wayai Miki Dan bana mijina bane kinemo Masa uba suhail zo kokasan wannan girgiza Kai yayi ya dauke Kai bansan taba tace matar kace ita Wannan cikin nakane banawa bane bansanta ba tanemawa cikin Nan ubansa Ya shige ciki Yama manta dasu a wajen Nan ta Fara dukanta kamar Allah ya aikota dukanta take tana dukan cikinta sai ga alhaji da hajiya a waje sukai parking da kafa suka shigo ko motsinsu Bata jiba ta danne cikin sai ga jini ya Fara malala kamar an bude famfo ihu hajiya tasa tayo kanta ta duba haleema Bata numfashi sai jini take zubarwa ta kasanta kamar famfo hajiya naganin Haka Tai kan Jeddah kamar wata mahaukaci dukanta take ta ko Ina ta hada Mata jini da majina dakyar alhaji ya bambareta kamata mukai ta asibiti barta Haka suka kinkimeta sukasa a mota sai zubar da jini take. Cike da farinciki suhail yace da gaske zaku musulunta suka hada Baki eh zamu bi addinin ka Dan dama hanyar daxamu bar bautar badu muke nema mun rasa mafita bamu San yazami ba suhail yai farinciki yabasu kalmar shahada suka maimaita dakyar suke fada sai da suka maimaita so bakwai sannan suka haddace Nan ya koya musu wankan tsarki ya nuna musu yadda addini yake musamman su masu wata irin al'ada Abu na farko daza kuyi ku kurufe jikinku ku sitirta jikinku Amma tayaya bakuda wasu kaya sai ganye abunda za ayi anemi manyan fatu ai musu dinki Wanda ze rufe musu ko Ina Ja'e yace za'ai haka Nan ya dinga koya musu duk wani Abu da musulunci ya koyar suhail yace yansan tafiya garinsu bayaso ranar bikin shekara ta ruske shi ba'a kau da wannan dabi'ar ba an ceci bayin Allah daga fadawa halaka Ja'e Kai zaka tsara komai shiru yayi tabbas Kam da kaina zan dauki fansar kashe mahifinka suhail Dan kaho baze taba shiryuwa ba Da ka barshi Amma Sam yace hakan baze yiwu ba Dan Dole sai ya mutu Yana mutuwa muguwar dabi'a ta mutu a garin Nan Amma kasheshi ba karamin Abu bane kasan cewa Yana mutuwa nizan gaji sarautar Amma zan maidoma da kayar ka Dan banaso na tsani sarauta a'a Ja'e karmi Haka dakai wallahi saika karba sukai dariya ya kamat dukanku nasanja muku suna ke lamunde Babar mu kin koma Aisha ke kuma Rama kanwata kin koma Ramatu ke Kuma tenkwai mayar Ja'e ta sunkuyar dakai Dan kunyarsa takeji sungama hauka akansa ita da yar'uwarta Ramatu Ashe yayansune murmushi Tai Nasa Miki suna fadila ke Kuma Aduke yai Mata wani kallo me tattare da ma'anoni dayawa sunanki subai'a suna dayazo Masa kenan sunan Yana burgeshi besan meyasa ya tsinci kansa da sa mata wannan suna tunda yafara ganinta yake tausaya Mata Dole idan ze koma da ita ze koma yanema Mata lafiya mikewa tayi cike da kunya cikin tsautsayi ta zame ta Fadi Tim ta kwalla Kara kafin kowa yaje kanta suhail yai tsallen badakere yake kanta. _To fans sainaji ra'ayoyinku ace a group inada member sama da 200 a kowane group Amma comment bana samun guda ashirin cikakke a kowane groups Allah ya kyauta duk hukuncin Dana zartar karkuga lefina dama na muku bayani tun a baya nice taku har kullum_ *Feedyn bash* [10/23, 2:31 PM] Ummu Subai'a ARNAN DAJI *NA* *FAREEDA ABDULLAHI* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DA SUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI* *WANNAN PAGE DIN NAKUNE ARNAN DAJI FANS GROUP 3 NAGODE MASU COMMENT DA KOKARI ALLAH YASAKA INAJIN DADIN COMMENT DINKU ALLAH YA BIYAKU DA GIDAN ALJANNA INAJIN DADIN YADDA KUKEMUN ADDU'OI ALLAH YA AMSA NAGODE FANS *Book 2* 50-55 Jini ne ya tsinke Mata kafin kace meye wannan hankalinsu ya tashi inda ramatu ta tafi dakko kayan aiki kafin ta dakko har cikin jikinta ya Fadi da sauri ta dawo ta Bata taimakon gaggawa ta dawo dai dai Amma tanata zubar da jini Nan da Nan sukai Mata kunzugu da fata ran suhail ya baci ga Ja'e a wajen duk da yasan komai game da abunda yai Mata Amma ransa ya baci yaji Bala'in kishi ya kamashi Nan da nan yaja Ja'e waje baze yiwuba suhail kafita a Haka bara nasa a dinkama fata yanzu wadda zata sitircema ko Ina Nima zansa adinka Mana harda Suma matan suhail yaji Dadi hankalinsa ya kwanta zasu samu su sitirce jikinsu kafin ya samu ya fita daga garin ya kawo musu Kaya MASU kyau Ja'e ne ya tabo suhail daya tafi tunani inaso nasanja suna duk da na fulanine kamar yadda kafada sunan manzon Allah nakeso Muhammad nakeso kadinga kirana kafin musamu addinin ya karbu a garin Nan alfarmar danake roko guda dayace kadawon da fadila ta Wallahi itace rayuwata tun tana jaririyar ta nake santa sanda kowa ya tsaneta base yanzu da kirar ta tafitoba Kai yayane a wajenta nasan zataji maganar ka kazama namiji Mana Mohd cewar suhail itama tanasanka Naga tsagwaron sanka a kwayar idonta muna Nan halayenka ta tsana yanzu Kuma daka gyara dakanta zata janyoka jikinta Kawai shawarar da zan baka anan itace karabu da ita dakanta zata nemeka ka shareta sannan kayi kokari ka fahimtar da mahaifiyar ka mu samu itama ta musulunta kaga mun Kara yawa karka damu Amma inzaka je garinku zan bika a'a Ja'e ya dalla Masa harara au namanta mohd kayi hakuri nida subai'a kawai zamuje itama Dan lafiyarta Nan Mohd ya Kama kuka Yana nacuci baiwar Allah na cuce ta Nan ya dinga lallashin sa kayi hakuri Haka kaddarar ta take na tabbatar da cewa da Kuna cikin hasken musulunci Wallahi bazaka aikataba zuciyarka me kyauce babanka ne ya kashe maka zuciya kayi shiru Haka Tabbas musulunci shine addinin gaskiya Ina kaunar wannan addini kallifa yadda mukai haske harwani kyau fadeela ta take duk wannan bakin munin ya kau tunda mukai wanka mukai sallah akwai wankan dazaku dingayi na kullum da soso Nan baku da sabulu Amma nasan bazaku rasa bishiya me fito da soso ba tabbas akwai koba wanchan din ruwan koginmu Yana kumfa sai mudigayi bakiji har nadena wannan Karin warin da hamami ba suka sheke da dariya gaba daya katemakeni Mohd kasamar mun hanya mu gudu nida subai'a ta habawa dariya Mohd yake Nina gane take takenka cewa santa kake Kai dai Bari Ina Santa Ina Tsoron matata jeddah caraf a kunnen ramatu tazo fitowa Yana Tsoron matar sa Chab namiji kamar yayanta Yana Tsoron matar sa ba haka ta barshiba Dole zata laluba indai har tayi Masa wani abun wallahi saita warware tayi silar tonuwar asirinta fasa fitowa Tai ta koma gida yauwa suhail maza koma ciki Kar mutane suganka da wasu Kaya daban Dan dai dama suna hidimar bikin shekara ne suna chan bazaka ga kowa yanzu ba Nima Dan kaho yasan Banda lafiya ne nake Nan azatonsa Ina wajen iya Dan ita Bata zuwa wayannan shirmen koma ciki maza yanzu za'a dinka kayan zuwa dare zan dawo sukai musabiha ya koma ciki shi Kuma ya nufi gida cike da tsantsar farinciki. A guje suka shiga da ita asibitin da hanzari likitoci suka taresu Kai tsaye aka wuce da ita ICU Banda addu'a ba abunda suke hajiya ta tsani Jeddah bazata Kara yarda da ita ba Dan tagama Mata da suhail Amma shima wallahi dai ya gane kuskuren sa bashi ba haleema bazata taba yi Masa maganar taba fatanta ta samu lafiya tunda Bata mutu ba Banda alhaji ko waje yanema yazauna yanata lazimi wannan masifa har Ina Ashe Haka wannan yarinyar take da mugun Hali tayi musu lumbu lumbu ta cikasu da alkhairan ta Ashe duk kissa ce irin ta Mata tana chan tana gasa wadda ta kasance kishiya agareta Yar'uwa awajenta idan ta riketa tsakani da Allah gidansu gidan tarbiyya ne Amma Ina gashi ta cutar da ita cutarwa me yawa Abunda ke bashi mamaki meyasa Mata suka dau kishi hauka basa koyi da kishi irin na matan annabawa irin na mutanen da susai dai kawai hauka sunsa San zuciya da San Rai a zukatansu Kuma duk Akan namiji namiji dai namiji dai Kuma ba'akan komai ba sai wannan jijiyar mtsww yaja tsaki sune bin boka malamai duk Dan jijiya da abun duniya inbanda hauka duka duniyar nawa take
Chapter 10 · 0% Book details