Sashe 16
Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bature itama Amma Ina haka yake dibanta kamar jaka duk ta saki ta bude gashi Sam baya Wasa duka yake shiga zuruf ta wahala Amma Sam Bata damu ba saboda kwadayin abun duniya satin si biyu suka dunguma sai airport suka shigo jirgi Dan dawowa Nigeria za'a daura aure Jeddah hara ta Sanja duk ta fada saboda bala'in naci irin na Alhaji malamalai haka suka biyo jirgi cike da shaukin so Afra ko tunda sukai haka da Jeddah ta Kira Al-ameen tagaya Masa komai yai tayi mata fada beso sukai rabuwar haka ba zeso su samu imformation akanta Koda tana Shirin aikata wani Abu haka saboda ya firgita da jeddah yace tanemi shiri da ita tunda ta kikkirata Bata daga ba Haka ko akai ta kirata Amma wayar a kashe taje dakin dasuka sauka wayam ba kowa a ciki ko tsinken ta Babu ta fitota duba ba alamun jeddah Haka ta hakura ta koma a abokin Al-ameen Yana zuwa ya dauke ta su zaga gari ya kaita kasuwa Tayo siyayya masu yawan gaske na kitchen da sauransu dai saboda bikinta ranar dazasu tafi dama jirginsu daya tayi ready din komai aka kaita airport a jirgi suka hadu da Jeddah Banza Tai Mata dama seat dinsu daya tunda Visa dinsu daya ta wata biyu ce Jeddah ta maidata ta sati biyu kiyi hakuri kawata nayi kuskure bazan karaba tabbas ke wani barice ma jikina abota ba Wasa ba nazubar da makamai na muna komawa za'a dauran aure da wanchan alhajin ta nuna Mata alhaji malamalai gabanta ne ya Fadi tabbas shine Wanda Ameer abokin Al ameen ya nuna Mata manyan Yan kungiyar luwadi subhahanallah wanchan Zaki aura eh kawata ya hadu ko umm kawai tace Dan Bata ga ta inda ya haduba fuska daskaka wata faskaka bakikkirin dakaganta kasan bakin zunubine idanunsa jajaye ko a Dubai ansan da zaman sa kungiyoyi ne dasu hmm kawai tace afra Zaki rakani wajen boka da wannan karon shikenan wani mugun kallo ya watsa Mata batasan yazo kusa da ita ba Wanda seda gudawa ta kamata Haleema anzama big madam angama karatu Yara sun yi wayo suna shekara ta bakwai gasu duk maza hankalin ta akwance tayi kiba abunta cikin nasara tayi masters dinta lafiya ta Gama ayaune take Shirin tafiya gida Hanan tayi kuka dukansu sunyi kukan rabuwa inda faruk yai musu alkawarin Hanan na haihuwa zasu dawo Nigeria Suma gaba daya Haka jirginsu ya dago zuwa Nigeria daga kasar Turkey cike da nasarorin data samu a rayuwarta ga yaranta abun Sha'awa tayo tsaraba sosai hatta mijinta Bata manta dashiba Kuma bata fushi dashi tasan asirine kawai yai tasiri akansa kodan darajar yayansu tayafemasa ta dauke Kar dake zuba a idonta An zuba komai a sashen haleema Wanda yaci uban nada komai sabo ga paint yaranma wajensu daban kowa dakinsa daban da toilet dinsa komai akwai harda kayan kallonsu gida yaci millions din kudade daga gefen side din haleema aka ginawa yaranta dakuna aka shigo dashi cikin gidan komai zam zam hajiya da alhaji da kansu suka shirya Al-ameen yajasu a katuwar Land cruiser Dan zuwa dakko su haleema dayaranta sauban safwan sudais Kai tsaye aminu kano international airport suka wuce gaba daya bakinsu yaki rufuwa saboda farinciki yau zasuga jikokinsu Dase dai a waya ko hoto ga asra da ansar gaba dayansu suka tafi a motar Yana chan Yana neman mota tuni sun dure subai'a a gefe sun hau kan kwalta sunata tsalle da murna sunga abun mamaki gawasu abubuwa dasuke ta gudu akansa har tsugunawa suke suna shafawa fadeela harda lasa wani mahaukacin burki suhail yaji Anja Yana juyawa yaga fadeela da ramatu a tsakiyar titi suna tsalle ihu ya zindima yai kansu gadan gadan shiko me motar Banda dariya ba abunda yake wayannan daga Ina Mata har Mata Amma daga gani kauyawane sai tsalle gashi ba sittirar kirki sai fata suhail ya matsa ya daka musu tsawa sukai gefe ya karasa gun me motar abun mamaki kawunsane kanin hajiyarsu zaro ido yai suhai na'am uncle alhamdulillah daga Ina ba lokacin magana bane muje mayi maganar a gida ku shiga muje yace musu Ya juyo dakko subai'a dansi sauri Nan suka Fara kici kici gwarama fadeela Tai kokari data zura kanta ta taga tana kokarin shiga Amma ta kasa sabanin ramatu da karkashin motar takesan shiga dataga ba haza sai ta dare saman motar Tai zamanta tanata zaro ido uncle dariya yake ya kasa magana cikinsa har ya kulle shi Kuma suhail ya Kai subai'a fitsari besan wainar da ake toyawa ba fadeela chatake Kai jawoni ciki tuni ya fito Yana kallon ikon Allah Ramatu asaman mota har faduwa ya kusayi sai ga suhail da gudu ku ya ficiko fadeela ya sakko da Ramatu ya sasu a motar dukansu Suma suka shiga take suka Fara jiyo ihu daga hanyar da suka biyo da gudun mutane dukansu sai da suka tsure Banda Uncle dake Shan dariya a waje da gudu suhail ya tukuda shi ka tashe ta mutafi akwai matsala Amma mota ta cije Taki tashi ga ihun Yana Kara tunkaro inda suke *To my fans ko yazata Kaya gashi arnan daji sun biyo sahun su suhail ko garin Yaya Haka ta faru ku biyoni dajin cigaba Kuyi manage da wannan wallahi dakyar nayi Amma Kuyi hakuri idan kunjini gobe Tom idan kunji shiru kuyimun uzuri wallahi Banda lafiya sosai Ina barar addu'oin ku idan kunyi sallah sainaji ruwan comment daga gareku nice taku a kullum akoda yaushe masoyiyarku ta har abada* *Feedyn bash* [10/23, 2:33 PM] Ummu Subai'a ARNAN DAJI *NA* *FAREEDA ABDULLAHI* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Assalamualaikum wannan page din sadaukarwane ga aminiyar kwarai hafscy smart or idon birni kawata ta Amana ina fatan Allah ya Kara Mana dankon zuminci ya saukeki lafiya mu kwaso shoky muci rengem allah yabarmu tare sister Amana sai Dan Amana ta gidana inasanki fiye da yadda kike Sona ki huta kiji Dadi kiyi yadda kikeso da wannan page din nakine yayar Ja'e *Bismillahir rahmanur Raheem da sunan Allah me rahma me Jin kai* *Book 2* 80-85 Cikin ikon Allah Yana Kara muza key din ya Bata wuta sai ta tashi Aiko suka zunduma ihu suna kokarin fita ta taga da hanzari ya rufe tagogin takaici ya ishi suhail suna yin gaba saiga tawagar sarki ta fito basuga komai ba sai sawunsu wani ihu sarki ya saki Yana gurnani kamar Zaki da hanzari suka koma hanyar dasuka fito dan bama yaso wani yaga titin sosai bare yai Sha'awar sa ransa a matukar bace suka juya gida gudu suke ekamar zasu tashi sama Ana iface iface da alkawarin ganin bayan su gaba daya idan ya kamasu huci kawai yake Wai harda dansa na cikinsa a wannan abun Ina baze yiwuba tabbas matarsa ta cuce shi Dan wannan abun dasa hannunta Bari mu waiwayi su ja'e lokacin daya juya lafiya kalau ya karasa gidansa ya tattara matansa duka a wannan Daren dama bashi da yawan Yaya su ashirin da hudu ne matan nasa Yara Tara yayi musu bayanin musulunci sosai sun ji Dadi sun yarda sun gamsu da wannan addini yai musu bayanin yadda ze rabu dasu dukansu baze bar ko daya ba dukansu sunyi murna Banda tawargaji ita kadai ce Bata yadda ba Tai bakin ciki kamar me akanme ze rabasu da addininsu tun na iyaye da kakanni Nan ya Basu kalmar shahada suka karba gaba dayansu beyi nisa shima a addinin ba Dan Haka abunda ya sawwaka ya koya musu Amma yace su boye karsu bayyana sai angama komai Ya shiga dakinsa ya kwanta abunsa Yana shiga ta wargaji ta fice sai gidan sarki tana zuwa sashensa aka sanar da ita yana sashen iya ga dare ya tsala Nan da Nan ko tace magana ce muhimmiya idan aka Bari gari ya waye akwai matsala duk ta kwashe komai ta gayawa masu tsaron fada harda guduwar su Tenkwai ai da gudu sukayi sashen iya kaho na gab da fadawa rijiya iya ko kamar ta mutu Dan bakin ciki Banda wari ba abunda yakeyi ga shegen datti sai Jin Kiran Gaggawa yayi daga bakin kofa da sauri ya Mike Rai bace Dan an Gama katse Masa Jin Dadi itako godiya Tai ga sabon ubangijinta daya temaketa kaho be Kama nacinsa akanta ba Yana fita aka isar Masa da labari be jira komai ba yasa aje gidan a kamo Masa kowa azo dashi fada zeje gurin badu yanzu Ya dau hanya sai gurin badu Yana zuwa yai Masa kirari sai ya Fara wani ihu bazan saurareka ba kaho kunci amanar mu sai da aka Gama Barna sannan zakazo Kuma harda danka na cikinka me Shirin Zama sarki sun kashe mun kububuwa ta tabbas bazan kyalesu ba maza ku bisu sunbi ta barauniyar hanya idan kukai azama zaku taddasu Dan ba wani Abu dazan Bari ya daukesu nine ubangijinku Ni kadai zaku bautawa hahahaha ya saki wata dariya dukansu saina Sha jininsu harda danka Kai Kuma zan barka bazan kasheka ba Kai ta mulki har na Kara baka wani Dan daga amaryar dazakai a anan gaba anemi yarinya azo da ita zan aurama godiya nake ubangijina Ina godiya maza ku bisu ku kamonsu a dauresu agana musu azaba da matarka da danka da matar Dan tsohon sarki da yayayensu da wannan Bakon shine yaron Dana gayama hhhhhhhh dif yaji shiru Jikinsa har rawa yake yazo gari sai lamunde kawai aka tarar nan da Nan yasa akamo Masa ja'e da iya yasa dukansu akaisu kurkuku aita gana musu azaba yaja zuga suka bi barauniyar hanya badu ya rage musu nisan zangon tafiyar Dan Haka nan da Nan suka karasa suna zuwa sukaga tashin su a mota shine suka juyo su gayawa badu ko akwai matakin dauka gaba daya garin ya hargitse gashi saura kwana hudu bikin shekara Dole su Kara tsaro da shiri Cikin ikon Allah suka sauka lafiya da gudu yaran suka rungume kakanninsu Dan sun sansu a hoto ita ko haleema asra da ansar ta rungume cike da tausayin su wace wannan granny momy dinku ce wajenta zaku koma ga Yan uwanku suka dinga murna suna tsalle suka rungume juna suna hugging din juna suka shigo mota bayan ansa musu kayansu duka sukayo gida