← Book details Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 26

Sashe 21

Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na datse miki hannu yanzu Tayi murmushi koda zaka kasheni nadena numfashi allah yana tare dani alhamdulillah nasan shahada nayi kuma yayana bazasu barka ba zasu daukar mun fansa ko yanzu burina ya cika dana ya dawo kasarsa ze sauke ka ya kawar da zaluncin ka ya kasheka kamar yadda babanka ya kashe kakanninsa kai kuma ka kashe mahaifinsa wata muguwar kara ya saki yada takobi ya sare tsintsiyar hannunta tasa ihu ta fadi a sume rikicif ganin gaka iya ta kara fashewa da kuka saura ke zan fada zan fada tana kuka ta bashi labari tundaga zuwan suhail har tafiyarsa Shakota yai yadinga dukanta munafika na tsaneki dama ashe bakya kaunata kika ajiyemun bako a gidana da kyar fadawan sa suka karbeta badu ya temake ka kace badu zakaiwa kyautar jininsu dan haka karka kashe su kuma tun yanzu wata ajiyar zuciya yake yana wani jan numfashi ku maidasu haka aka kwashe su kamar wanki aka maidasu inda suke adinga basu abinci so daya ruwa so biyu saura kwana biyar bikin shekara yau dan haka a tsananta tsaro a garin nan Haka aka zuba fadawa ta ko ina a garin harda mata bayi tundaga farkon daji har cikin gari anan suke kwana saboda tsananin tsaron da aka sa a garin zuciyar kaho kamar zata fashe ya gama sanin sirrin garinsa gashi ya gudu da yammatan dan angaya masa da Rama kadai ze samu haihuwa a yanzu amma dole ya nemeta saboda idan ya kashe su ja'e ta haifa masa magaji gaba daya garin kuguru yana cikin mugun tsaro hankalin kowa a tashe yake sun dauka yaki za'ai duk wajen bokan da kaho zeje a garin sai ace da Rama kadai ze iya haihuwa gashi badu yace ranar bikin shekara yazo da budurwar datai masa gaba daya yana cikin tashin hankali Su suhail sun huta matar uncle dakanta taja su fadeela tayi musu wanka kamar jarirai har amai tai saboda datti ga wani hamami dasuke ta Kara yi musu wankan tsarki tazo kan subai'a kuka tasaka ganin yadda gabanta ya jagale Nan ta hada ruwan Dumi tasa gishiri da Dettol ta cika ruwa a baf tasa ta take tasaki wani ihu sai da Tai suman hucin gadi tafi Rabin awa a ruwan sannan ta cireta Tai Mata wanka taji dadin jikinta sosai dakanta ta fito daga bandakin Nan tasamusu dogayen riguna sunyi kyau abunsu ba abunda suka iya a duniya kamar jarirai sabuwar haihuwa tausayinsune ya lullubeta dama akwai irin wayannan a duniya wallahi ta dauka sai a TV wayannan bazasu taba wayewa duka ba saboda fadar annabine Dan kauye sai ya shekara arba'in a birni yake wayewa Aiko sai dai addu'a wayannan Suhail ya nemi izinin tafiya gida Nan uncle yace shize Kai su Amma matarsa fafur tace a bar Mata su fadeela beso ba Amma ya roki alfarmar su tafi su gaida su daddy sai dawo ta yarda da hakan dakyar suka yarda suka fito Tsoron mutanen garin suke da tarin gine ginen dasuka gani ya daga musu hankali tayi saudat sunan matar uncle tayi alkawarin nuna musu yadda zasu dinga kula da jikinsu Dan gabansu har wari yake dukansu da wani yauki saboda rashin kula gashi ko kamar zaka kitsa kansuma abun kallone ga gashi Amma Duk kwarkwata inbame dauriya ba baze iya zaman minti biyar dasu ba Tayi mamaki da suhail ya iya tahowa dasu duk da Taji labarinsu Amma tayaya suhail yazama Dan wannan garin zata so taji suka rankaya gidan su suhail sukai horn me gadi ya bude musu sukai parking sai rike hannayensu take haka suka shiga gidan hankali kwance ma aikatan gidan gudu suke gani suke suhail fatalwane suka shiga parlour din sukai sallama alhaji da hajiya na zaune inalillahi wainna ilaihirrji'un muryar wanake ji kamar ta suhail nine mom da sauri ta juyo Da gudu ya karasa shigewa jikinta mom sai kuka dad ko mutuwar zaune yai Yana kallonsu ya sake ta ya rungume daddy hamdala kawai yake dad mom da Baki fa nake Uncle yai murmushi kugama murnar sa shigo saudat ku shigo Mana cikin murmushi ta sawo Kai yammatan suka biyo bayanta a firgice daa ya Mike Suma suka mike gaba dayansu kawai gani sukai ya yanke jiki ya Fadi yanata nuna wani guri hankalinsu ya gama tashi gaba dayansu tofa fans meke faruwane dad yayi hamo _To fans bari indakata anan inajin dadin comment dinku fans Ina kaunarku har raina muna tare iya wuya I love you Lodi Lodi masoyana *FEEDYN BASH* [10/23, 2:33 PM] Ummu Subai'a ARNAN DAJI *NA* *FAREEDA ABDULLAHI* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Dr rahmatullah s nepa Maman asmeey Ummou shureim Princess maisar Nahdy Ummu khalifa Princess deejah Maman Amma Maman hamra Mmn auwal Maman humaira Nerner Aysha Humaira K'sdq Mrs aminullah Zeenatu Khadija Ummy labo Jamsam Nahdy Queen _*Kai wallahi kunada yawa bazaku lissafu ba masoyana na feedyn bash fans Ina godiya Wanda beji sunansa ba Dan Allah karyai fushi koyaji Haushi Kuma Kuna Nan tafe masoyana wannan page din nakune kuyi yadda kikeso dashi ina Jin dadin comment dinku masu comment karkuyi fushi musamman masu comment Dan Banda marasa comment nagode masoyana na Amana*_ *BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Book 2* 110-115 Da hanzari mom ta debo ruwa Duk sun rude sai kuka suke suko su ramatu sai buya suke suna tunanin ko tsoronsu sukeji Duk da a dogayen riguna suke Amma ganinsu suke wasu daban kuka kawai suke a gefe sai da ta zuba Masa ruwan yai wata ajiyar zuciya ya matso jikin ramatu ya kamota itako a tsorace take ta saki wani irin ihu wallahi Indo ce wannan sak ba mis iko sai Allah Indo Amma wannan nasan ba Indo na bace kamace kawai sai kuka Nan suhail ya zubawa daddy ido daddy meke faruwane wallahi kamarsu daya da kanwata danake baka labari kullum jikinsu yai sanyi tunda sunsan labarin su Amma shi betaba bashi wannan labarin ba yadai ce iyayensa sun mutu da kanwarsa hatsarin mota tofa wata sabuwa cewar suhail Nan aka zazzauna aka dinga gaishe gaishe Nan suhail ya basu labarin komai be boyeba harda yadda lamunde ta tubure dantane tofa gaba dayansu zufa suke ketawa mom ko hawaye take wallahi karya take meya hadaka da arnan daji muguwa kawai shiru dakin yayi Alhaji yai gyaran murya hajiya bansan rashin gaskiya Mana kinsan dai cewa maganar gaskiya bamu muka haifi suhail ba wani ihu suhail yai yai kan daddy Amma kafin ya karasa ya sume akadinga zuba Masa ruwa ko gezau hajiya kuka take wallahi idan ka kashe mun shi bazan yarda bazan yarda ba Dana ne nono na yasha wallahi sai nai shari'a dakai suhail ya mutu sai lallashin ta saudat takeyi Banda kuka ba abunda take suko mamaki suke yadda har maganar lamunde ta tabbata tunaninsu wannan mutumin shine yayan lamunde chab chakwakiya aka Debi suhail sai asibiti nan aka Kira haleema aka sanar mata ko takalmi Babu akafarta Tama rasa meke Mata Dadi hankalinta yagama tashi daga wayannan sambala sambalan yammatan Kuma tare suke Duk da akwai kauyanci a tare dasu da kazanta da rashin wayewa faduwa tazo daidai da Zama anan aka kwantar da subai'a akayi Mata dinki agabanta aka Bata gado na sati biyu saboda tetenus yaso shiga wajen saboda kazanta da rashin kulawa su fadeela sun koma gidan anty saudat asibitin dama ba'a zaman jiyya haka suke zuwa suna dubasu Suhail sai da ruwa leda yasha biyar Dan akwai karancin ruwa ajikinsa gaba daya shikansa beda lafiya saboda sauyin rayuwar daya samu kusan shekara guda satin sa daya sannan aka sallamosu Duk ya rame hankalinsa Duk a tashe yake wannan wane irin mutane ne masu yakanah haka Dame ze saka musu wannan alkahirin dasukai Masa beda bakin godiya agaresu gaba daya yanzu kunyarsu yakeji Sam ya kasa sakin jiki dasu mom ko gaba daya itama ta rame tare suke jiyyar Haleema ko Ina aljanna ta shiga Amma abunda ke damunta dayane motsi kadan yace y jikin subai'a wacece itane gaba daya ta tsare gida ta kankane tana tare da shi har aka sallamo shi gaba daya sun hallara kwansu da kwarkwatarsu Banda subai'a dake gadon asibiti kowa ka kalla fuskarsa ba walwala Dan sun San wannan zaman bana lafiya bane alhaji ne yai gyaran murya suhail ka fahimceni zan fayyace maka wani boyayyen sirri Duk da mahaifiyar ka ta rokeni akan boye wannan Sirrin Amma bazan bi San zuciyarmu mu cutar da mahaifiyar ka tunda Allah ya nuna Mata Dan ta Duk da bamu da yakinin haka Amma idan har ba mahaifiyar ka bace ba abunda zesa harta furta haka tsakanin d`a da mahaifi sai Allah jini ba karya ba ya gyara Zama Bayan na rasa ahalina gaba daya Wanda wannan wani sirrina ne Wanda ko matata Duk tsawon shekarun mu batasan takamai mai labarin ahalina ba Amma ta Soni a haka ta kaunaceni Banda abunda zan saka Mata anan gidan duniya bayan mun rabu da ahalina na fito titi a wannan lokacin ne narasa yadda zanyi Ina hawaye Ina komai ga tarin shanu da kudade dankar a tare Dani gashi hanyar Nan akwai yan fashi musamman dajin falgore gaba daya a tsorace nake cikin ikon Allah sai ga wata mota ta fyallo da gudu Nan na hau titi na dinga daga Masa hannu dakyar ya tsaya dayaga ze kadeni cike da tsoro ya dakan tsawa Kai Dan fashi ne ko ya zaro bindiga ya saita Ni na durkusa nasamasa kuka Ina cewa yatemaka min Banda kowa a garinnan hanya tabiyo damu an kashe iyayena da kanwata a cikin Daji ya tausaya min to Kai gaka da shanu yazanyi dakai da wayannan shanun Allah Kuma ya temakeka muna gab da gari Nan da Nan Naga yayi waya cikin minti talatin saiga wasu mutane da kakin sojoji yace maza su kada shanun zuwa garin falgore gidan Mai gari Ni kuma yadaukeni mukaje falgoren gidan me garin yai Masa bayani aka saukeni haka kawai naji hankali na yafi kwanciya da wannan mutumin Ashe sojane babba me mukamin general Nan nace Inasan magana dashi muka kebe na nuna Masa tarin kudina shikansa ya tsorata dayaga wayannan kudaden yadauka kayana ne a buhun Ashe kudine tabbas kayi hankali meye sunan kane yace Ibrahim
Chapter 21 · 0% Book details