← Book details Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 26

Sashe 22

Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

zan tafi daki zuwa garin Jos inda iyalina suke suna shagari quarters Dan haka zansan yadda za'ai da kudin kayi karatune eh nayi secondary a kauyenmu to Masha Allah zaka koma makaranta daga Nan sai asan yadda za'ai nai Masa godiya yace Dame gari ze tafi Dani ga amanar shanun Nan tunda sunfi dari ya kula dasu adinga kiwo dasu kudin nonon da Mai adinga sallamar masu kula dasu yai megari yaji dadin haka muka wuce barrack dinsu ta falgore daga da sassafe mukaiwa Jos tsinke Nan ya bude account yasa kudin akayimun takaddun sakandire kunsan yanayin kasar nan Agurguje a hannunsa nasa mu komai na rayuwa harda matata yarsa ce shekarata ta farko a makaranta ya auran ita na samu buk a Kano Nan muka dawo tare yasiya mun gida da kudina ya siyamun company guda biyu ya bude mun manyan super market da manyan shaguna inda na zabi sunan mu na gado alhaji Ibrahim gadon kudi a kowane Abu Dana mallaka shekarar mu biyar da aure shiru ba batun haihuwa nagama karatuna lafiya ba Kama kasa na waye baza kuce wannan iro na kauyen burji bane wata ran munje duba baban hajiya ba lafiya mundawo dai dai wani daji motar mu ta tsaya ruwa ya Kare gashi ba gari kusa hakan yasa na tafi neman ruwa cikin dajin dake safiya ce Haka na kutsa daji sai Naga ruwa me mugun girma cikin farinciki na karasa nasa jarka na debo ruwan sainaji kukan jariri abun ya ban tsoro na saki robar zan zura da gudu sainaji kukan yai yawa dana matsa chan saina hango wani Abu kamar Dan karamin kwale kwale Amma na ice nayi addu'oi na karasa sainaga jariri fari Sol dashi a cikin wanna abun ga ganyaye sun rufe shi da hanzari nasa kafata cikin ruwan na janyo shi ba komai a jikinsa ga ruwan ya Fara tabashi ko cibi be Fadi daga gani sabuwar haihuwane da hanzari na cire rigata nasashi na dakko abin dayake ciki na maida shi ciki na debo ruwana na ajiye shi a gefe na juya zan tafi ya Kara tsandarewa da kuka tausayinsa yasa banyi shawara ba na dakko shi hajiya harta gaji tafara biyi hanya muka hadu na Mika Mata jaririn Tai mamaki nai Mata bayanin komai tai hamdala a ranta Dane daga sama Allah ya bani muka daukeshi bako tsoro mun tsinci da a daji cikin ruwa muka dawo Kano lafiya muka kaishi asibi lafiyarsa kalau sai nemonea data kamashi Haka muka dinga rainonsa har ya girma mun sanarwa da iyayen ta sun amince Amma munce a gidan marayu muka dakko shi Cikin ikon Allah kamanninsa daya Dani kamar Nina haifeshi tunda mutan unguwa sun dauka danmune tunda a gra muke ba ruwan wani da wani sanadinsa ne ma muke mu'amala da Yan unguwar shekarar sa uku Allah maji rokon bawa ya bata ciki ta haifi Al ameen gashinan daga Nan sai dai Bari Bata Kara haihuwa ba suhail ya taso da nasibi da kokari inda muke jinsa fiye da Al ameen yayi karatunsa ya gama yayi kudi sosai na Basu company da gidaje Amma shima tashi daya yai fice a Nigeria yaro da kudi Kenan yai murmushi wannan shine tarihin ka suhail kowa kuka yake a parlour din a ransa me magana
Chapter 22 · 0% Book details