← Book details Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 26

Sashe 14

Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ko maganin ba adeba sarkin daji yai musu alkawarin Kai musu da kansa ze debo Suka karasa gida suka gayawa lamunde abunda ya faru tayi farinciki Dan Haka Ja'e yace ze tafi gida Nan da kwana uku zesa suhail a hanya adaren ze kashe kaho suna Tai Masa fatan nasara da samun cigaba a rayuwarsa waiko ya matar mado inji fadeela hhhhhhh ya sheke da dariya kai tanasan mado kuma Kai madon take so Wai meye sirrin ne Kai kasani inji suhail ta tashi hankalinta rashin ganinka to shine iya taga be kamata a tsaya boye Mata ba gashi ka dawo hayyacinka Dan haka Tai Mata bayanin komai tayi kuka kamar ranta ze fita Amma ya ta iya Haka ta hakura Dan yanzu Haka ma a yau din Nan tare zasu da daddare su musulunta (Allah Akbar gaba dai gaba dai addinin musulunci)murna tacika suhail tuni ya zube ya Fara godiya ga ubangiji murna ta cika su dukansu Niko ga shawara meze Hana ku tafi gaba dayanku dasu fadeela da Ramatu saboda kulawa da subai'a ya dallawa Ja'e harara ni ban Isa kula da itaba ba Haka bane Dan dai kawai zata fi Jin dadine nasan farin cikin ta kake so koba haka ba ya Kai Masa duka lamunde ta shigo abunda ke Raina kenan katafi dasu gaba daya hankalina zefi kwanciya Dan in sarki ya samu Labarin wannan bakon addini wallahi kashin mu ya bushe Allah Yana Nan umma kidena damuwa to shike Nan tace shikenan diyoyin albarka bara naje na kwanta Kuma ku tashi muje ta Kama Ramatu datake dingi shi fadeela ta karbeta a a kyaleta dama subai'a na dakin lamunde suna fita Ja'e ya matsa kusa da fadeela Suhail ne yai tsaki kaifa baka da kunya agaban yayanta kake nanukarta ko rungumeta zakai ayi hakuri yayanmu ya fada Yana murmushi mikewa yai ya bar musu dakin tuni ya kamota ya Fara rungumarta kissing dinta yake Kota Ina ita kanta daurewa take chan dataji ze wuce gona da iri ta ture shi kamanta a addininmu na musulunci bakyau Haka sai anyi aure hmmm na manta kece kullum tafiya kike da imanina Amma ba komai kin amince a Kara daura Mana aure murmushi tayi ta mike Tai hanyar waje hankalinsa ya tashi sai ji yai tace na amince Mohd dama bakai nake kiba halinka nake ki dama chan Inasan ka bazan taba samun masoyin gaskiya kamarka ba a wannan duniyar ta fice da gudu yai hamdala yai murmushi ya fice sukai sallama da suhail ya tafi gida Da daddare sai ga iya da matar mado suna zuwa suka Fara zuwa wajen suhail ya musuluntar dasu suka dawo dakin Aisha lamunde kenan suka zauna sunta hirar musulunci da yadda akai suhail yazama danta da irin zaluncin da kaho yai musu da mahaifinsa suka aikata musu Taji dadin bayyanar suhail cikin garin ta bawa Ja'e goyon bayan kashe kaho har turakarsa sun dade suna Hira sai ganin mutane sukai tsaye akansu hankalinsu inyayi dubu ya tashi me sukayi suwaye wayannan ga dare addu'oi suka Fara Wanda suhail ya koya musu gani sukai an bude hanya suman zaune sukai dukansu Dan tsoro addu'a kawai suke _~To fans Dina masoyana na gaskiya masoyana na Amana iya wuya iya dadi muna tare daku anan zan dakata sai naji ruwan comment dinku Dan wallahi ba karya saboda ruwan comment dinku nake typing jinjina agareku masoyana nice taku a kullum akoda yaushe~_ *Feedyn bash* [10/23, 2:33 PM] Ummu Subai'a ARNAN DAJI *NA* *FAREEDA ABDULLAHI* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Assalamualaikum wanna n page din sadaukarwane agareki maman asra da ansar Allah ya rayamun Yara na ya Kara musu basira da hazaka da kokari Amma fa feedyn bash fans kuyiwa maman asra zanga zanga Dan ita ke hanani typing ta daukeni da Hira sai na buya nake muki typing Yasin Kuyi Mata zanga zanga ba ruwana *BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DA SUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI* *Book 2* 70-75 Sarki kaho ne ya danno kansa Yana zabgawa iya harara jikinta sai kyarma yake dukansu sun gama tsurewa ya daka musu tsawa me kuke aikatawa me kuke shiryawa ko angaya muku bansan abunda kuke aikatawa ba meke tsakaninki da wayannan kinsan cewa cikakkun makiyan mune Koko kunsan cewa nema suke suga bayana musamman ma wannan mummunar danafi tsana badu ya temakeka tuba nake naxowa shalele bikon matarsa ne saboda yadda kullum yake min kuka ya hanani kwanciyar hankali shine nazo biko hade da dubiya yasanar dani sun kashe kububuwa shida su Tenkwai din da Rama A firgice ya juyo sun kashe kububuwa karyane kububuwar da tun iyaya da kakanni take duk Wanda ze taso haka ze shude ya barta karya ne daya daga cikin bawansa yace badu ya temakeka Ni kaina naji wannan batu dake ta yawo a garin Nan Amma ance angansu da wani kyakykyawan saurayi me Kama da mado Amma ance wannan farine tas bako a garina tabbas akwai abun da kuke boyewa Dole naje nagana da badu akwai matsala a wannan garin kuduban gidan Nan gaba dayansa indan kun ganshi ku kawon shi nan suka firfita sunata neman sa sun duba ko Ina basu ganshi ba sai Kaya na fata a daya dakin irin Wanda ja'e ya koma sawa suka zo dashi Suka durkushe a gabansa kan kowa a kasa badu yaja zamaninka badu yatemake ka ba kowa a gidan Nan ba Kuma komai sai wannan kayan na tabbatar Kuma na ja'e ne charaf dayan yace bana ja'e bane nadayan ne mekama da mado tabbas nagansu dazu zasu fita ran sarki ya gama baci narantse da badu duk sai na halaka ku ya fice ransa a bace yayinda iya jikinta Banda rawa ba abunda yake kayarda Dani bansan komai ba bansan kowa ba sai Kai sanadin San da Dana ke musu nazo kayarda Dani ta mike da gudu ta rungume shi ta baya duk a cikin kissa ne Ya juyo da ita nayarda dake Dan haka fito mu tafi yai gaba fadawansa suka rufa Masa baya iya ta koma ku kwantar da hankalinku Amma a Daren yau zansa Ja'e ya sasu a hanya saboda akwai matsala bazan bar sarki yaje gun badu ba idan ba Haka ba ze Gaya Masa komai nagode iya kin temakemu dayawa da hanzari suka fice suna fita suka tarar sarki najiransu Taji dadin hakan suka tafi hankalinta a tashe tana ta tunani chan dabara ta fado Mata dama sarki yanaso ta bashi hadin Kai indai tanaso ta dauke hankalin sa daga zuwa me wajen badu to tabbas sai ta bashi hadin Kai ta bashi kanta zatayi hakan Koda hakan na nufin mutuwarta gwara ta ceci su suhail Ina suhail ya shiga Ina yake hankalinsu ya gama tashi sai ganinsa sukai sun hauro daga katanga shida Ja'e kuyi maza ku kamo subai'a bamu da lokaci maza kuzo mu wuce Aisha na kuka yayanta nayi suka rike subai'a su matan suka sasu a gaba suka haure ta katanga Dan sarki yabar masu tsaron gidan haka suka dinga gudu suna yankar daji sai da suka kusa fita daga jejin sukai sallama suna kuka Mohd na kuka kozaku dawo ku sameni ko kuma bazamu sake ganawa ba fadeela ki gafarceni nasan har yanzu Baki dena Jin haushina ba ramatu subai'a nafi kwarar rayuwar ki kuyafemun kuka suma kukan suke na rabuwa da garinsu Basu taba barin dajin ba sai yau ko iyayensu ba Wanda ya taba barin garin hanayar da sukabi hanya ce ta sirri Wanda ba Wanda yasan da ita sai sarki kaho da Ja'e Idan kace zaka bi hanyar barin dajin zaka kwana uku baka fita ba Amma ita wannan befi Kai awa biyar ba Kuma zata sada ka da kwalta Haka suka dinga kuka fadeela ta rungume Mohd tana kuka munyafema masoyi Yan uwana duk sun yafema zan dawo gareka Banda Miji sai Kai a duniya ka kulamun da kanka karka Bari wani Abu ya sameka dakyar suhail ya fisgeta suka dagawa Ja'e hannu yanata kuka a wajen ya juya ya koma garin sukuma suka Kara gudu suhail daukan subai'a yai Dan sufi sauri suka dinga gudu sai da asuba suka kawo titi har anyi sallah motoci sai wuce wa suke dai hankalinsu ya tashi rashin mota kusan awa guda sai juyawa suke suna duba bayansu suko farinciki suke yau gasu a wani waje Basu san sunan motar ba bare titin kawai kallo suke shiko hankalinsa baya jikinsa Tana fita ta tafi wajen alhaji labaran tana kuka take Gaya Masa satar da akai Mata Kuma mallakinta ne murmushi yayi Dan yasan karya take yaga komai akanta Dan ya duba sosai zakici ubanki yace a ransa to naji kwantar da hankalin ki wannan ba abun damuwa bane ya Mike ya dakko takaddun company guda biyu manya manya ya Bata wannan anan kera jaka da takalmi wannan na kayan kwalliyane murna kamar ta suma ta rukunkume shi da gaske alhajina gaskiya naji Dadi ka biyani duk Ni kadai wow kwarai ko asan da nake Miki kadan Kika gani bakiga komai bama Allah ko yanzu muje ki ga motocin da'a kawo Miki guda uku duk nakine suna fita taga motoco kirar huwei daya marcedes daya kirar Land Rover kuka tasa yanzu alhaji na wannan duk nawane dariya yayi nakine ga sheda ma takardun ya Bata da sunayenta da mukullan kuka take kashirban Dariya yake aransa kukan farinciki kike yanzu gaba Kuma na bakin ciki Zaki sai kinyi nadamar sanina a rayuwarki shegiya makwadaici ya ta share kwallar yanzu alhaji mukoma ciki mi magana suka koma ciki tana nane a jikinsa alhaji so nake wannan company din ai Masa takaddu da suna na saboda halin rayuwa murmushi yai wato saboda halin rayuwa so take shima ya mutu taci gado ko ta kashe shi kenan lallai wannan jaka ce ya fada a ransa yanzu ko take ya Kira lawyer minti goma sai gashi ya Gaya Masa yadda za'ai ya Mike ya tafi murna ta cika ta alhajina bara naje nanunawa afra motocina tasan cewa niba mutuniyar banza bace Dan ansacen kadara a ranar nai wasu ya washe Baki wannan gaskiyane gimbiya ta Nan ta mike ta Fara kada malamalai tuni ta tafi da zuciyarsa Dan ba abunda yake bukata sama
Chapter 14 · 0% Book details