Sashe 13
Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
matar Abdul tunda abokin mijinkine jihadi kikai murmushi tayi karka damu amma fa yayi fushi sosai Dan Allah kabashi hakuri Ya sheke da dariya kinganmu tare na warware masa komai dake faruwa yayi Allah wadai da halin jeddah kuma ya yarda ke macece ta gari kaddara ta hada zamanku da jeddah yanzu zanturo miki wani abokina zan bashi number din wayarki zezo hotel din da kuke kifito kiba shi zeturon su zuwa gobe nima insha Allah gobe zamuje nida maryama zamu tone komai data bunne sannan mu kwashe duk wasu abubuwa nasa muhimmai gaskiya kunyi kokari keda maryama Allah ya biyaku Ya kashe wayar ya kira abokinsa ya gaya masa hotel din dasuke ya temaka ya turo masa gobe muhimmun sako ne tunda shi Dan kasar ne yasan duk wasu cuku cuku dazeyi ya turo su tare sukai karatu a turkey cikin ikon Allah yana gab da wajen tuni ya karasa ya kira ta da hanzari ta fito komai tasa shi a envelope ta mika masa ya karba ko hira basi ba ta juya Dan kar Jeddah ta dawo ilai ko tana shiga dakin tana zama sai ga jeddah ta shigo cike da murna da manyan ledoji ga wata muguwar waya a hannunta iPhone 11 wayar ko Nigeria bata zoba ta rungume afra ki tayani murna nayi babban kamu kawata nasamu wani alhaji labaran shima Dan kano ne yace aurena zeyi Dan haka two weeks zami kawai mu koma kafin mu koma angama komai sai daurin aure Kuyi manage da wannan tofa jeddah masifa wakuma ta yayibo oho mata muje zuwa nice taku akoda yaushe *Feedyn bash* [10/23, 2:31 PM] Ummu Subai'a ARNAN DAJI *NA* *FAREEDA ABDULLAHI* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *ASSALAMUALAIKUM MASU YIMUN ADDU'OI NAGODE SOSAI DA KILAWARKU GASKIYA BAN TABA TUNANIN HAKA AKE KAUNAR ARNAN DAJI BA SAI YANZU GASKIYA INA GODIYA MASOYANA DA YAWAN COMMENT DINKU AGARENI BAZAN GAJI DA GODE MUKU BA INAJIN DADIN KULAWARKU GARENI AKARA HAKURI DAI DA RASHIN TYPING DINA AKAN LOKACI NAGODE MASOYANA* *BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DA SUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI TSIRARA DA AMINCI SU TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD SAW* *BOOK 2* 65-70 Waye alhaji labaran wani hamshakin me kudine Wanda baya bambaruwa kwata kwata yanada Mata biyu a yanzu uwar gidansa matar ladan nomar sa sai Kuma mabiyarta wadda suka hadu bayan yadan Fara samun kudi a hankali sunyi soyayya sannan sukai aure Yana auren Mata dayawa a karshe su rabu matan Nan guda biyu sune basa rabuwa Suma Kuma Basu da Yaya dayawa uwar gidansa nada Yaya biyar amaryar nada uku bayan su ba Wanda yake Kara haihuwa a gidan kansu a hade yake duk wadda ta shiga gidan izayarsu kadai ta isheta Banda wasu dabi'un na megidan Wanda su kansu matan Basu San dasuba dai su matan dayake aure Dan wasu sun Sha masu Kuma kwadayi sun jawowa kansu wannan kenan Hhhhhh alhaji duwai komai yayi Dadai nasamu yarinyar data amince da aurena farat daya zataci kudi cikin sati biyun da zami a Dubai shawara alhaji malamalai kayi kokari ka shiga jikinta tunda kace idonta a bude yake ka samu kafara saduwa da ita tun yanzu hakan shize Kara Bata dama ta saki jiki dakai ka siya Mata motoci masu zafi ka mallaka Mata gwala gwalai duk wani Jin Dadi ka Bata anan yadda zata kagara tana dawowa a daura auren Dan zatai tunanin a gidanma zata samu wannan jin dadin kasan dai halin matanka kuma kasan sati uku da kwana biyar ya rage Mana sa sani alhaji duwai Ina bukatar Kaya fa gashi kamun nisa shegen Kaya kana San wajen Nan baka gajiya hhhhhh sai na shigo garin Jeddah ce take birkita kayanta ta zazzage akwatin yafi so bakwai ihu ta zindima afra tashi wallahi sai kin fitomun da takadduna da ATM Dina wallahi kinyi kadan kimun sata duk yadda muke dake Zaki mun sata mtsww ta hambareta gefe nizaki kalawa sharrin sata da chan ban tabayi Miki satar ba sai yanzu ki dai tuna inda Kika saka wallahi a akwatina suke tasa ihu tana kuka wallahi afra kece Kika sacemun wallahi bazan yarda ba kinsan dai ke kadai ce a dakin nan ke kadai nabarwa kayana jikin afra ya Fara rawa asirin ta ya gama tonuwa meyasa Tai wannan sokancin cikin ikon Allah sai ta tuna kin manta a arrival mun barwa wani ajiyar jakan zamuje fitsari Kuma kin bude kin dakko passport dinmu a ciki Kuma yaga sanda Kika saka pin din Ihu tasaka wallahi shine nasan keba barauniya bace wallahi sai annemo mun shi a yau din Nan ki nutsu tunda two weeks zami sai mu koma a duba cct camera Amma kinsan fa shima Nan Dubai din ya taho Taya za'ai agane shi kawai idan min koma muje wajen boka musa yai Mana binckice akansa asa shi ya dawo da kayan kinsan aikin boka Sha yanzu magani yanzune take kama murna shiyasa nake sanki kawata akwai bada shawara me kyau hakane tace banza sakarai ke kawai boka shima insha Allah karshen sane yazo daga ke har shi har mahaifiyar ki cikin tashin hankali ta Kira alhaji labaran kana Ina ne yagaya Mata kawai fita tayi Al ameen ne gaban hajiya yanai Mata bayanin komai ranta kal tana ta sa Masa albarka yanzu zanje zamu tone komai na gidan nida maryama zamu dakko takaddun gidajensa da companies dinsa da komai daya dangance shi kafin ta dawo hakan yayi Dan albarka tun kafin su tallasar Masa da dukiyar dan wannan jeddah sai ta wulakanta tun a duniya abunda tadinga aikata Mana raba da mahaifi ba Wasa ba ta rabashi da yayansa da matarsa mesansa baiwar Allah komai na bangarenta ta sace Kuma munyi waya saura sati daya su dawo Kuma insha Allah gidanta zata koma kamun bayyanar suhail Dan Dana be mutu ba duk inda mukaje Cha ake Yana Raye cikin koshin lafiya Dan haka kasa ai Mata order din komai a zuba asashen ta to momy bara naje sai na dawo haka yaje gidan suka Fara aikin cirewa shida maryama suna daga gadonta sukaga wasu manyan gunki manne da juna suka fasa shi sunga abubuwan mamaki dayawa hankalinsu yai masifar tashi duk dauriya irin ta Al ameen sai da yai kuka ganin irin yadda akai wa yayansa ga sunansa Nan andaure shi katamau bashi da wani yunkurin motsi haka suka hada komai waje guda aka sai ga me gadi ai akwai wasu kawunan jaki Dana bakin Kare Dana bakar akuya Dana bunsuru danaga tasa wanchan security din ya binne Dama Al ameen tunda ya Fara ganinsa be yadda dashi ba Dan bema yadda ma aikaci bane tuni ya Fara kwalla Masa Kira da gudu yazo ya damkeshi yana duka sai ya nuna gaya masa me Jeddah tasa shi ya aikata Nan ya Fara bayani kamar yadda me gadi ya fada sannan ya Dora da fadin ya binne layu a makabarta ya binne bunsuru da ransa abubuwa kala kala Nan aka Tisa keyarsa sai da ya kaisu suka Ciro komai aka lakada Masa duka sannan ya kore shi daga gidan abubuwa ba kyan gani sai wari wasuma sun rube sun Zama kwarangwal Haka aka zuba musu fetur aka kone Ihu da Kara ke tashi a wajen wasu irin maganganu wuta na tashi Nan sukaga wani haske ya fice ta cikin wutar sai da tacinye kurmus akasa direba yaje kogi me gudu ya zuba Dan ba asan illar taba itama Dan irin ihun da aka dingayi da rugugi da ana konawa suka bude sashen haleema yaga yadda akai Mata dashi ya Kira wani company yai musu bayanin komai sukazo suka duba komai suka koma da zummar gobe zasu siyi komai ya dauki komai na suhail ya bar gidan ransa a jagule ya firgita da Mata tsonsu yake bashi ba aure sai yayi binkice me zurfi Yana tafe Yana share kwallar tausayin yayansa Suhail ne wani karti yazo Masa ya Mike ya bangaje sarkin daje ya fisgi takobinsa yanata addu'oi ya tofa Mata sai tasaka wan ihu Nan da Nan ya sakar Mata Sara gaba daya dajin yadau wata Kara me barazanar fasa kunne duk Wanda ya sume sai da yafarfado suna kallon ikon Allah kawai gani sukai ta Kama da wuta tana ihu tana komai tana magana atemaketa bazata Kara cin mutum ba ta tuba kowa mamaki yake haka ta kone kurmus sannan dajin yadena cin wuta Nan da Nan gari yai wani irin haske wata irin iska take ratsa duk Wanda ke cikin dajin abun mamaki sai ga tsuntsaye sun fara shawagi a saman dajin da babusu Sam duk wata hallita me motsi Bata iya fitowa Nan da sarkin daji yai kan Ramatu data Fara sandarewa take ya fito da magungunan hucin nata ya Fara shafa Mata Amma ko gezau suhail ne yai kanta cike da addu'oi Yana yofa Mata a kafar chan ta saki ajiyar zuciya tuni sarkin daji yake ya sawa Mohd magani wajen ya tsaya ya Dena zubar jini mafarauta sai zare idanuwa suke suna mamaki wannan Abu Wai yai ba kububuwa an hallakata su goma Sha biyar ne suka matso wajen suhail Kai ko wane irin tsafi ne dakai Haka munji Kanata wasu kalamai Daba musan dasuba yayi murmushi ba tsafi bane addu'a nake Ina gayawa ubangijin dayayi wannan aljanar yayi mu daya kawar da ita Kuma ya amsa Dan ta kone har abada Nan da Nan sarkin daji yayo kansa tabbas Kaine jikan sarki Rana a binkicena zakazo Kai zakai Mana maganin wannan kububuwa ka kuma kawo haske a wannan garin ka kauda zalincin sarki kaho ta sanadinka za a Dena bautar badu Dan Haka na yarda da ubangijin ka inaso na koma bautarsa Nan dukansu sukace Suma sun amince farin ciki ya cika zu iyar kowanne daga cikinsu Mohd Rama fadeela Mohd yai caraf yace munaso hakan yazama sirri a tsakainin mu suka amince da sharadin nan suhail ya basu kalmar shahada ya koya musu wankan shiga musulunci a dajin suka wuni Yana koya musu kana Nan Abubuwa na musulunci harda sallah yai musu alkawarin zeje gida ya dawo da manyan malaman dazasu koya musu komai sukai sallama fadeela ta Kama Rama datake dingisa kafarta