← Book details Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 26

Sashe 19

Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

makoki anyi Masa fa Kuma ai nayi takaba ko haleema dai kallonta take cike da mamaki ai kema kawai ki auranki Dan Kinga gaskiya da kyanki gwara ki Mori lokacin ki ki auren ki kema Shiru kawai Tai Mata tana ta nazari chan Jeddah tace haleema Baki da abinci ne Tai murmushi Yana cooler a flask naci nawa saura na Yara debo kici to tace ta nufi kitchen din maryama ta koma bangaren haleema dama tunda Jeddah tabar gidan Al ameen yai Mata korar Kare tunda ta shigo tana jinta tana bayan kitchen tana wanke wanke ta Gama Kuma Tai zamanta bataso su hadu Sam Dan tanajin tsanarta fiye da yadda haleema ke tsanarta ta shiga kitchen din harda cire mayafi haleema Bata kawo komai ba ta debo hadaddiyar jelop din shinkafa taji kayan lambu da nusashshen kifi ta zuba a plate maryama na hangota tana ta mamaki kodai da gaske ta sauta Ta bude freezer ta dakko drinks me sanyi ta duba ba kowa dake hangota ta warware zaninta ta kwanto maganin yaran ta barbada musu a ciki tana karkade hannunta maryama ta Kara lekowa Bata ga komai ba Amma jikinta ya Bata wani abun ta zuba ta dakko abincin ta dawo parlour tanata zurawa sunata hirarsu kamar gaske sai da taci Tai Kat Tai Mata sallama ta fito zata rakota ta hanata itako Maryama Sam hankalinta be kwanta da zuwan Jeddah gidan ba bataga dai me ta zuba ba Amma tabbas tayi wani abun tana Nan tana jiran ta tafi bacci me nauyi ya dauketa a wajen dama wajene me kyau Tana fita ta fito da maganin da akace idan dai halima ta shaki kamshin sa zata haukace ta fef fesa shi yadda ze shiga wajenta abun tsautsayi me wanki yazo kawo kayan wanki ya ganta tuni ya kunshe bakinsa ya juya Dan shi tsoronta yake ba ruwansa Haka ta ja motar ta Tai gaba cike da murna tana fita direba na sako hancin motar yaran suka fito ansar ya taho da gudu ya fada kan haleema momy abinci to Dan gidan momy autan momy bara na zubo ma ta mike taje ta zubo masa Nan ya Fara cin abincin magriba tayi Jin Ana kwalla Kiran sallah firgigit maryama ta tashi ta shigo gidan da gudu taga yaran duk suna parlour ansar na cin abinci da sauri ta karbe ya saka ihu Yana Kiran momy Lafiya waya taban autana cewar haleema ranki ya Dade nice banyarda da abincin bane Allah yasa ba Wanda yaci no ba Wanda yaci menene wato hajiya Ina taga Naga kamar maman asra tasa wani Abu a abincin to Kuma bacci ya daukeni kafin nazo na dauke na zubar ikon Allah wallahi dama sam banyar da da itaba maza jeki zubar shi Kuma insha Allah ba abunda ze same shi nasan dama Dan Ni da yayana tayi ba yayanta ba Dan ba yarda za ai taima yayanta Haka ko akai ta zubar ta Dora musu indomie suna ta Kiran abinci cikin 10 minutes ta kawo musu suka ci hankali kwance sunata hirarsu hankali kwance suna Al ajabin Hali irin na jeddah tunda duk cikinsu ba Wanda take bakon sa Jeddah ta cika da farinciki aikin ta yayi batasan yayanta suna hannun haleema batasan Dana nata yayan ba ta dauka suna gurin hajiya shiyasa idan zaka Gina Ramin mugunta Gina shi gajere Dan karya fada dakai Haka ta koma gidan hajiya hafsa tayi yadda boka yace Mata na zubawa a abinci duk ta ajiye na cushe cushe duk ta tusa tayi kyau kyan Dan miciji idan Kika ga Jeddah tamkar fure angama komai an na biki anfara biki anyi shagali iya shagli anyi lunch anyi party ya ake dinner a Bristol palace guri yayi guri Mata masu ji da kansu sun hadu maza sugar Daddy masu ji da kudi sun hallara matane manyan Mata matan aure wayanda suka gagari mazajensu da zawarawa wayanda suka gagari gidansu da yammata wayanda suka gagari iyayensu matan bariki manyan alhazawa ne ke ta faka manyan motocinsu Nan aka Fara dinner anci an Sha Anyi wadaka da nera amarya ta samu kyaututtuka daga hannun abokan ango ta samu kyautar gidaje da motoci da makudan kudade ita kanta abun ya daga Mata hankali soboda Bata taba ganin amaryar da akaiwa kyauta ranar bikinta ba kamar ta mahassada hassada ta cika musu ciki masu kaunarta kodan su rabe ta su dangwali arziki sunyi murna ance arziki kashi tofa Jeddah ta tako shi me shegen wari inji wasu kenan ba wani Abu daya daga hankalin jeddah ganin yadda taga maza na hugging din juna manya masu ji da kudi masu mataye da yayaye a gida amma sai Ta basar ba abunda yafi Bata mamaki irin yadda Taji Ana ambatar mijinta da malamalai na duwai kowa Haka yake cewa chan sai ga alhaji duwai ya bayyana hankalin ta be idda tashi ba sai da taga alhaji malamalai Yama manta da ita ya rungume duwai har dasu kiss Nan aka Fara sabuwar chashewa aka Fara budiri Nan taga Ana kawo kwalabe ta tabbatar giyace su kuma matan aka dinga hadasu da shamfen anci ansha anyi shagali Ba a tashina sai karfe daya anan aka Kama dakuna Mata ganin yadda akaiwa jeddah Nan suka Fara sake salon iskancin Taku ko wacce da kalar nata upwayanda ke neman Mata suka Fara kamu masu neman junansu ko suka shige daki Dan wasu sun maku a cikinsu Haka ko akai alhaji labaran ya lallabata suka shiga daki da sauran kawayen su da basi kasuwa wasu da dama sun gane Dan homo zata aura Amma ba halin fada Haka suka shiga dakin sunata Hira suna Tai Mata famfo Akan karta yarda ta zauna da kishiyoyi Dan ta Zama hamshakiyar hajiya yanzu shiko alhaji malamalai nachan da alhaji duwai sunata buga Masha'arsu Dan an Dade ba'a haduba tun kafin ya tafi Dubai Basu bar Juna ba sai gab da asuba ragowar ma Haka suka dinga barzar junansu Jeddah tana complain din yadda suke rungume rungume sai kawayenta suka nuna Mata tsabar wayewace da zaman turai suma ba Haka sukewa junansu ba ta yarda a Haka hankalinta ya kwanta Asubar fari Ta mike ta Fara shiri ko ta kansu Bata bi ba ta fice Dan Shirin daurin aure taje gidan hajiya hafsa karfe takwas ta tafi kwalliya goma dot ta dawo tayi kyau kamar Yar tsana tamakar fure an daura auren alhaji labaran da hajiya hafsa sadakinta dubu dari biyar lakadan Ba ajalan ba andanyi chasu a green park sunci sun Sha karfe shida aka kawo motocin Kai amarya kowa ya samu Yan gulma da Yan bani na iya Kai tsaye sashenta aka kainta Yan ganin gida sun Gama gani dama ba dnginta ko guda hajiya hafsa ce ta tarasu tace Yar yarta ce wasuma sun dauka budurwace Dan jikinta me kyaune bakace Tama taba haihuwa ba Bayan kowa ya tafi ta mike ta zagaye sashen nata tsaf bala'i gida yayi gida Bata iya ganin sashen nata ba ta koma ta rufe fuska koma zata rufe oho taci kwalliya tayi kyau chan Taji hayaniya ta dauka abokan angone harda gyara Zama Nan aka Fara nocking Tai shiru tana jiran ya shigo da karfi Taji an hankado kofar Ana zage zage ke Dan uwarki kinaji muna bugu Baki bude ba dayar ce ta janye mayafin eh lallai wannan kyau haka ga kwalliya duk a gidan Nan to daga yau Zaki dau darasi Dan uwarki matane manya su biyu da yammata uku ko wacce rike da zabga zabgan bulalai keba kwadayi Yasa Kika aurar Mana Miji ba wallahi na lahira sai ya fiki Jin Dadi zakisan kin shigo gonarmu suwaye ku cewar Jeddah Bata rufe Baki Taji an waska Mata Mari tana dagowa aka Kara Mata ta saki wani ihu momy ta matso ta daki bakinta sai da ta cire Mata hakori ihu ta saki na azaba Ku daketa kuyi Mata dukan mutuwa tamu sannu da zuwar kenan tunda Baki da mutuncin daza a kawoki ki gaishemu Nan suka zage balaga sukai Mata lilis Tana ihu tana komai Amma ba Wanda ya daga Mata kafa sai da ta daku sukaga da kyar take motsi suka fice suka barta a yashe face face cikin jini cikin kukan ma ta gagara yinsa Nan da Nan fuska Tai him ko Ina jikinta ciwo yake jitai anturo kofar da karfi bakaramin firgita Tai ba _To fans Bari mu kwana anan sai zuwa gobe insha Allah koya Labarin su ja'e sai gobe zamu leka musulman daji muga halin dasuke ciki akara hakuri dani yanayin jikina ne sai a slow nice taku har kullum a Koda yaushe_ *Feedyn bash* [10/23, 2:33 PM] Ummu Subai'a ARNAN DAJI *NA* *FAREEDA ABDULLAHI* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_~Assalamualaikum masoyana bazan gaji da godiya agareku ba fans musamman feedyn bash real fans da kainuwa fans da komai mukaddarine fans da matan aljanna Ina Jin dadin yadda kuke nuna min kauna bakina baze iya furta adadin kaunata agareku ba hannuna baze iya rubuta sakon godiya a gareku ba Sai dai nace Allah ya biyaku da gidan aljanna nagode da addu'oin ku agareni nagode nagode nice taku kullum a Koda yaushe maman yan.......kundai gane beauty *Bismillahir rahmanir Raheem da sunan Allah me rahma me Jin Kai* *Book 2* 100-105 Alhaji labaran ne ransa a mutukar bace ya bude kofar da karfi Yana zuwa ya dauke Jeddah da mari Wanda sai da taga wuta Dan ubanki su hajiya sa anninkine daza a kawo ki baza a kaimusu ke ki gaishesu ba suna gaba dake to wallahi idan kinasan kanki da arziki ki musu biyayya yi nayi bari na Bari Dan dasu Zaki zauna a gidan Ni idan nasa kaima sai kin ganni ba'a wulakanta mun iyalai na bazan dauka ba fada yake kamar xe Ari Baki Jeddah da take kuka kamar ranta ze fita na shiga uku Ni Jeddah yau Kuma gidan danazo Kenan Ni za'a yiwa duka a Daren aurena zancen da take Kenan a zuciyarta tana ta kuka mtsww dadine yai Miki yawa Ni Zaki tasa agaba kinawa kuka ubanme akai Miki Dan wannan Marin danai Miki ai shafar Mai ne dago fuskarta Tai jage jage da jini da majina ga
Chapter 19 · 0% Book details