Sashe 18
Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wallahi bazasu ciba ihu suke suna kuka taikaici ya gama cikamasa ciki ya daka musu tsawa baku da hankali ne angaya muku Nan ma daji ne dazakuyi mun hauka KE fadeela kinfi kowa iskanci ku shiga hankalinku fa haba kamar ya Kara tunzurasu ihu fadeela ta saka ka dakkomu zaka kashe mu wallahi bazamu ci wannan ba cikin ikon Allah sai ga me doya da miyar alayyahu dama suna noman doya cike da murna sukace zasuci aka sauke musu sukaci suka Sha ruwa sukai nak mutane Banda dariya ba abunda suke musu wannan Abu Haka tashin hanakali fada Dame gari ranar sallah Nan suka dau hanya zuwa Kano Direct gidan kawu suka wuce Wanda tuni yabawa suhail kan motar saboda tsabar haukan dasuke da kauyanci duk abunda suka gani sai sunyi ihu ko dariya gaba daya sunzama kamar mahaukata Rama ce ta fashe da kuka gaskiya yaya suhail ka cucemu dama Haka ake rayuwa a duniya kaki kazo kadauke mu tuntuni to da tuni muna chan muna Shirin dibgar Roman shekara shi dai kawu dariya kawai yakeyi sai bayan sun shiga Kano suka nufi gidansa dake sharada Nan suka yada zango dakyar suka shiga gidan Dan Basu taba ganin gini irin saba danma suhail yayi musu bayanin yadda garin yake a hanya Gidanta suka je lokacin karfe takwas na dare suna zuwa tayi parking ta kamo Jeddah sukai bangaren ta ko Ina a gyare ta kwantar da ita chan sai ga Al ameen Yana zuwa ya doka Mata harara to Yar iska kingama yawon tazubar din naki wallahi yau sai kinbar gidannan tunda bana ubanki bane ba sisin ki a ginin gidannan azafafe ta mike ya isheka Al ameen a yanzu ko zanbar gidannan tuni ta Fara hada kayanta ta dakko duk wani abunda zata bukata kozaka ban wuri murmushi yai Mata Amma na mugunta Yana fita ta Fara daga katifa abun mamaki duk wani abubuwa nata na asiri Babu su ihu ta dinga zindimawa kamar mahaukaciya Afra dariyace ta subuce Mata na shiga uku afra kidena dariya Ina neman kayan asirina ne da boka yaban mutum mutumin zan maida zuciyarsa ga alhaji labaran hmm lallai Jeddah har yanzu Baki saduda ba wallahi tun da Naga yadda gawar boka ta wulakanta na Kara tsorata da lamarin rayuwa ki hakura kibi Allah mtsww dallah chan gafara zan tuba NE Amma ba yanzu ba saina tatike alhaji labaran Haka suka fito ranta a bace harda envelope dinta ta takaddun gidan suhail da duk wata kadara tashi Bata San ansaja ba ansa Mata na bogi suka wuce tana hararar Al ameen Dan shi take zargi Bata San komai na asirin ta ankwakule ba shashasha Allah ya shirya Haka suka koma gidansu tana shiga gidan wani gululun bakin ciki ya tokareta saboda wani Baki da gidan yai ga wani mugun wari suna shiga sukaga ummanta a kwance gabanta duk ya rube sai tsutsotsi yake rufe hancinsu sukai gaba dayansu hankalinsu ya tashi lafiya umma meya sameki cewar afra data karasa gareta Amma jeddah tsaki taja ta koma waje gaskiya bazata iya zama a wannan gidan ba tasan me zatai zata nemi hotel ta Kama na two weeks tanemi iyaye na bogi su daura Mata aure a hada Mata na karya a karbi lefe abunda ta tsara kenan aranta Bata bi ta kansu ba ta fita taja motar ta Tai gaba afra kitemakeni Banda lafiya tun Ina zuwa asibiti Abu yaci tura inata boyewa ne Amma na kamu da cutar daji wadda kukewa lakabi da cancer yanzu Haka tanga ne ya kaini asibiti akace kudin aiki dubu 700 Kuma nasan Yana da ita Amma yace be da ita ya kawoni Nan ya yasar har yau ban Kara ganinsa ba kitemakeni afra cike da tausayi tace Ni Banda kudi a yanzu Dan bikina saura sati daya Amma bara na Kira jeddah tana fita taga wayam ta duba dakinta Bata Nan bandaki ba kowa ta leka waje wayam ba motar ta ta gudu kenan itada uwarta bare ni tuni itama ta karawa kafarta burki ta tafi gida itama tana Allah wadai dasu jeddah insha Allah alakarsu ta yanke tana tafiya sai ga text dinta ya shigo idan kingaji Kya tafi ki kyaleta kwashe kwashen ta na masifa taje wani yai Mata cin dayafi karfinta ya rubata Dan Haka ki kyaleta Naga uban daze Kara cinta a Haka tunda ita batasan ta girma ba Tofa lallai wayannan Basu da mutunci cewar afra tuni tasa number dinta a divert Jeddah Bata zame ko Ina ba sai gidan wata dillaliya a Yan lemo Tai Mata bayanin komai ta amince akan kudi dubu dari biyu sunyanke maza za'a nema su karbi lefe su daura aure Baki alaikum haka ko akai ansamu wasu dattijan biri zauna gari banza aka tsadance su uku ta Kira alhaji labaran ta Gaya Masa komai dariya kawai yai ba matsala gobe karfe goma na safe zasuzo su kawo Haka ko akai washe gari ta Kama asabar aka kawo kayan lefe akwati Sha biyu sai kace wata budurwa budurwar ma ta yayan gata da sadaki dubu dari biyu da kudin gaisuwar iyaye dubu dari uku gaba daya dari biyar suka kawo murna kamar jeddah ta zuba ruwa a kasa Tasha daya tambayeta meyasa aka kawo Nan bayan da tace a dangwauro take sai ta waske kawai Ai chan din babanta dama ya mutu mamanta Kuma Bata garin sunyi waya tace azo Nan gidan kanwarta Haka suka bar maganar bayan sati daya akai bikin afra aka kaita me Dile batai party ko daya ba sai dinner da ango yai bayan daurin aure an kaita gidanta suka Sha dinner dinsu tadai yi walima agidansu anyi biki lafiya angama lafiya duk wata kawa datasan ta barikice Bata gayyaceta ba iya Yan unguwar sune da Yan uwanta matar babanta bataso Tai wannan auren ba bakin ciki kamar tayime gashi ta samu mijin marainiya akwati takwas yai Mata komai Masha Allah sai muce amarya Allah ya bada zaman lafiya Haka jeddah tadinga shirye shiryen ta tsaf dangane da nata bikin tasha gyaran jiki tayi kyau dama jikinta me kyau ne sai ta dawo tamkar wata fure Dan kyau tayi fes abunta gwanin Sha'awa biki ya rage saura kwana uku duk wasu fitinannun kawayenta ta gayyacesu Dan party suka shirya har kala biyar zasu watsu su lalace ya bude Mata bakin aljihu sai bindim bindim take a ciki gashi komai ya sauke mata na daki tasan ita me sa'a ce a rayuwarta bazata taba auren wahala ba wata kawarta ta hadata da wani hatsabihin boka megani har hanji yagama shiryata yadda zata tunkari gidan alhaji labaran Tofa maji magani jeddah koza a Kara dacewa _*To fans sai naji comment dinku gaskiya na yanke shawarar Dena posting kowane book nawa a wasu groups din sai nawa Dan bakwa mun comment wahar dakaina kawai nake iya fans Dina kemun comment wallahi indai Banga sanji ba daga yau nadena posting din book Dina a kowane group nice taku a kullum a Koda yaushe*_ *Feedyn bash* [10/23, 2:33 PM] Ummu Subai'a ARNAN DAJI *NA* *FAREEDA ABDULLAHI* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Assalamu alaikum my fans inafatan Kuna lafiya Dan Allah kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu hakan ya farune sakamakon rashin lafiyar danake fama da ita kuyi hakuri kumin uziri ba kullum zan dinga muku typing ba Dan Allah kudinga kokari Kuna posting zuwa wasu groups din wallahi bazan iyaba abun dayawa nagode my fans nagode da kaunarku a gareni da tarin addu'oi in da kuke mun suke Kara bani karfin gwiywar faran ta muku kamar yadda bakwa gajiya dayimun addua akara hakuri dai dani 95-100 Jeddah duk wani shirye shirye ta Gama tayi gyara na tashin hankali ko budurwa albarka har wani yalo yalo take wankan inji akai Mata jikin ta yayi smooth ga alhaji labaran ya sakar Mata bakin aljihu facaka kawai take da kudi ta tattaro ta dawo gidan hafsa dillaliya hankalinsu kwance suke shirye shiryen biki wadda hafsa ta Zama uwar amarya ga wayanda aka debo haya a matsayin iyayen ta maza tunda dama mahaifinta ya mutu a matsayin abokans da Dan uwansa suke Tayo gayya ta manyan Mata matan dasuka amsa sunansu Mata wasu zawarawa ne wasu matan aure wayanda suka gagari mazajensu wayanda suke haduwa a shargallensu yammata ma ba'a barsu a baya ba bikine ta shirya shi nakece raini anshirya karya a bikin ko dayake da abun ai Kawarta ce ta rakata gun boka sangamu ya Bata lakanunnuka da magungunan dazata mallake mijin ita kadai ta juyashi San ranta sannan ya Bata Wanda zata haukata haleema saboda bala'in haushin dukan datai Mata ya Bata Amma sai yai wata wata daya yake Fara aiki sannnan ya Bata Wanda zata kashe yayan Amma da sharadin indai aka kuskure wani ya ganta sanda take aikin ita zata haukace Kuma a haukan zata mutu ba magani ta yarda da hakan gears yaran su mutu nata su tsira ai ko tana tafiya Bata zame ko Ina ba sai gidansu ita da haleema ta Gama shirya duk wa ni plan ita da kwayenta ta ajiye su a hanya ta danna horn megadi ya bude Mata direct part din haleema tayi Tana shiga ta tayi nocking aka bude Mata sannan ta zauna haleema ta hade fuska tan jiran Taji taima ta wani haukan na daban ko zancen banza Amma sai taga ta durkusa kasa tana hawaye kiyi hkr Yar uwata da duk abunda nai Miki ki ya femun nazo neman gafararki dama bikina za ai na kawo Miki iv nazo na Gaya Miki na nemi gafararki gaban haleema yai wani irin faduwa ta ringa addu'oi a ranta tana rokon Allah ya kareta daga sharrin Jeddah idan da wani mugun abun tazo Allah ya maida Mata da kayanta kanta ba komai na yafe Miki jeddah cike da farin ciki sai washe Baki take nagode sosai Yar uwata Nan suka dinga kwasar Hira Amma Jeddah Anya ko Baki garajan daura aure ba baku da tabbacin mutuwar suhail fa dariya tayi haba sadiya inbanda abinki suhail ai ya Dade da mutuwa shekara kusan daya ba amo ba labari ai Dole mu fidda Rai Kuma anga takalmansa a wajen da hularsa to shi Yana Ina har zaman