← Book details Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 26

Sashe 2

Arnan Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

1-5 A guje lamunde ta debo ruwa ta zuba musu suka mike sunata kuka ba kuka zakuyi ba saurarata zakuyi suhail ne yace tayaya zan saurari wannan tatsuniyar taki ni musulmine cikakke kuko daga gani arnan daji ne Wanda gwamanati ta manta daku ana tunanin babu ku a duniya kuma akwai sauran irinku dayawa Meye sunanka dannan suna na suhail Dana suhel kai Dana nane tabbas saboda dan garin nan ne kawai me wannan zanen ko wane gida da irin nasu rama juya bayanki ya gani ba iri daya bane dana tenkwai Dan dai sunyi kama ne a zanen shiyasa zakaga haka amma ba iri daya bane tana juyawa radau irin nasa ba wani bambanci ga kamarsu nan tsantsa ganewa ne ba aiba Ashe Cike da kuka tenkwai tace ni su waye iyayena kenan lamunde dama bake kika haifeniba kinsan rama yar kice kika barta a hannun wani daban duk shirin mune tenkwai yanzu zakuji komai naji nayarda cewar suhail zan dai Ji labarinki amma ni bakece mahaigiyata ba tayaya ina birni kina daji ko sittira bakwa sawa bama kusanta ba sannan kice wai kece uwata Kuban ruwa zanyi sallah Suka fito yaga aduke a bakin daki HQ hangame kudaje sai bi suke ga kudansu narka narka ga tsutsotsi na fitowa kadan kadan subhahanallah ya salam Allah meye wannan mutum CE wannan kome kuna kallo zata rube kun barta haka Munrasa yazami da ita fyade akai mata ta samu wannan lalaurar fyade ya furta Allah ya sawake idan na koma gida zan aiko a dauketa a tafi da ita ai mata magani nayi alkawarin kawo cigaba a wannan garin da kudina da jikina duk da ban fita wajeba da kyar ya iya watsa ruwa yai wankan tsarki Dan be yarda da kansaba Ba soso ba sabulu kasa yadinga sawa yana rage daudar jikinsa gaba daya kyankyamin Kansa yake ya gama ya maida kayansa yanzu haka ze dinga fama da kaya daya saboda raunin Kansa amma dole ze bar garinnan yau ko gobe hankalinsa a tashe yai alwala yai sallah kawai kallonsa suke meye wannan dungure dunguren dayake oho masa ya Dade yana sallah yana addu oi sannan ya gama mekake haka cewar rama Ku bari ba lokacin tambaya bane yanzu Idan nagama Baku Baku labarin keda shi da tenkwai sai ya bamu nashi Kuna saurarata eh sukace gaba dayansu harda aduke a dakin tafara bada labarin kakanku me suna rana shine ya haifi mahaifinku me suna tabo nice babarku lamunde rama da kai suhel kakanku ya kasance adalin sarki a wanchan lokacin yayin da da kakan jae shine waziri bashi da imani ko kadan tun zamanin iyaye da kakakanni ake bautar gunki badu ake cin naman mutane A yadda aka bamu labari da badu baya magana kuma duk sanda kaso zakaje kaganshi da bukatarka ze biyama akwai masu kula dashi kimanin mutum talatin maza da mata suna masa wanka da kwalliya rana daya aka wayi gari badu ya kashe su dukansu bebar ko gudaba ana zuwa aka tarar da gawarwakinsu Daga nan yasa dokar hana zuwa sai karshen shekara ko kuma sarki idan anshiga wani hali zeje yayi bauta sannan Suyi magana yasa dokar yanka maza biyar duk shekara hakan shiya hana kowa ratsowa ta dajin dajin ya zamana se mukadai yan garine muke rayuwa a cikinsa saboda mutannen da ake kamawa aka bawa gunki jininsu kwanci tashi aka rasa na kamawa sai aka koma kan mazan dasuke zaune a gari ana kamasu ana bawa gunki badu jininsu hakan yasa muka kara Shiga matsi Haka akaita tafiya har akazo zamanin kakanku yanemi badu ya janye wannan batu na yanka mutane maza biyar maza sun fara karanci a garin sai mata kuma lallai sai Wanda ya haura shekara ashirin badu keshan jini sunyi muhawara inda badu yace yaje yagani tunda yaja dashi zega meze faru shiko ya tsaya kaida fata sarki rana a wannan lokacin ganin yadagene aka wayi gari duk wani ahalin sarki ankashesu saura shi lokacin be auri kakarkuba yanada tarin mata a lokacin Haka yaita kuka yaje wajen badu yanemi gafarar sa akan ya janye Dan badu yace Somin tabine sai yaga bayan duka yan garin haka gari kowa hankalinsa ya tashi ganin wannan mutuwar ko da daya ba abar masaba kuma yace bashi ba kara haihuwa haka aka cigaba da wannan dabi ar dama akwai dabi ar cin jarirai agarin indai ka haifi da haihuwar fari za a cinyeshi tas ai romonsa Sam kakanku sai ya denacin naman jariran saboda bakin ciki ga ba damar daukar fansa haka suka hadu da kakarku ya aureta a lokacin Jeddah bakin ciki yai mata yawa Allah cikin ikonsa saiga afra nan suka Shiga daki itada afra ta fashe mata da kuka ta debo mata result din tana kuka mtsww meye abun damuwa ina Ahmad na layinku kije kidinga nemansa ki saki ranki kibi hakan kya samu kema ya yarda dake iyayensa kuma ki kamasu a hannu nasanki da San abun duniya kwanciyar mage zaki me daukar rai shima koyazo kice yayi hakuri sai nan da wata ukun kawai kije kibawa hanan hakuri ki Shiga jikinta yadda zataje gidan tai ta zuzuta kirkinki kinga kece da riba Shi kuma Ahmad karki yadda Ku hadu a nan gidan danke ba hankaline dakeba kudinga zuwa hotel wanda yake da tsaro zamu shirya muje gun bokan Dana gaya miki ni yanzu zan koma dama wayarki na kawo miki nagode afra tabbas nasan kina kaunata yanzu gobe da wuri zanyi dabara naje mu hadu da Ahmad ya deben wannan muguwar sha awar suka fito ta rakata ta tafi gida ita kuma ta dawo hanan tagani a parlour tanata kada kafa tana jiran ta tanka mata Cike da murmushi ta karasa kusa da ita kiyi hakuri kanwarmu da abunda ya faru jiya tai mata banza nayi kuskure ki yafemun kinsan ciwon ya mace na ya macene inasan suhail sosai kiyi hakuri nasan kuna fushi banje nagaida mom ba amma yanzu ki tamabayar mana suhail sai mije ki kaimu mudawo cike da murna ta kalleta haba anty jeddah har naji dadi kinga zami rayuwa me dadi dake kafin na koma da nayi niyyar komawa sashen anty sadiga amma nafasa yanzu bara naje taje ta sameshi yanata lele da uwargida rangida tagaya masa yabasu izini yaji dadi har ransa Suka fito hanan tajasu sai da sukaje supermarket me kyau tayi siyayya kamar hauka suka je gidan baki duk sun ragu saura na nesa suka gaisa hanan tanuna musu ita a matsayin amaryar suhail hajiya taji dadi kowa yanata yaba mata da sa mata albarka sai sunkuyar dakai take irin na masu kunya aranta ko kira take zakuci ubanku dukanku dani kuke zancen saina raba tsakanin uwa da danta *Anan zan dakata sai naji comments dinku fans nagode da yadda kuke kaunar arnan daji haka* *Feedyn bash* [10/23, 2:18 PM] Ummu Subai'a ARNAN DAJI *NA* *FAREEDA ABDULLAHI* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Assalamu alaikum inawa kowa da kowa fatan alkhairi Allah yasakawa kowa da alkahairi ya biya bukatunku na alkhairi gaskiya bansan haka kuke sona ba haka nake aranku ba sai jiya nayi murna da farin ciki da addu oin gareni da comments dinku Allah ya bar kauna* *Bissmillahir rahmanir rahim da sunan Allah me rahama me jin kai godiya ta tabbata ga Allah ubangijin hallittu tabbata ga annabi Muhammad (saw)Allah yasa mu amfana da darasin fake cikin wannan book din akuma dinga tunawa maguzawan daji ana kai musu tallafi Dan har yanzu akwaisu duk dajin dazaka wuce akwai halittu masu rayuwa a cikin sa* *Arnan daji book sadaukarwane ga mahaifiyata Allah yakara lafiya da Nisan kwana ya raya zuri a* 5-10 Haka aka dinga nan nan da jeddah zuciyar hajiya tadanyi sanyi sai yamma suka koma suhail yazo wajenta yana bata hakuri ta wani kwantar dakai ta rungumeshi ka kwantar da hankalinka ba damuwa duk daya Mike nida ita nan yaso tabashi hadin kai amma ta kiya hanan na labe naji sai hnkln ta ya kwanta ashe yadda ake zato ba haka takeba sharrin shedanne jiki ba kwari suhail ya fito Jeddah faduwa tai tasa kuka ga bikin zuwa ba zanin daurawa tuni jataba ta ciyota tai masa text ummanta ba lafiya suna asibiti bata jira reply dinsa ba ta fice ta kira Ahmad tagaya masa inda zasu hadu ta kashe wayar gaba daya danma karya kirata tana ganin text taki budewa kafin ta karasa ya karasa samir guess palace sukai wa tsinke nan sukaci karensu ba babbaka suka kwana suka hantse Ahmad dai shine ango Dan shi akaiwa gyara Ya gigice ya fita hayyacinsa Dan ta kashe kudi wajen dibgar magani da kyar ya kyaleta dama itama jarababbiya Ahmad dine dai dai ita dan yana masifar gamsar da ita duk da bashi da kudi ita take bashi amma fa akwai kayan aiki haka suka kwana sai da safe taiwa gidansu tsinke gabanta na gaduwa cikin ikon Allah sai kaninta kawai ta samu a gidan Wanda rabon data ganshi har ta manta Shame shame ta same shi ansassara shi an kawoshi anyasar a gidan yafi shekara baya gidan wai yana Lagos daga baya ya dawo abuja a yadda suke samun labari amma yanaiwa uwarsa aike idan yasamu dama yazama tantirin Dan iska haka ta dauke shi ta kira makocinsu ya temaka mata ta kaishi asibiti ita ko ummansu iwar gantali ko ina tayi Allah masani dakayar suka karbeshi duk da private ne ya jigata ya zubar da jini ko magana baya iya yi Haka ta kunna wayarta sai ga text din mijinta yafi guda goma hankalinsa a tashe yanata kiranta baya samun ta yai mata text ba amsa yaje gidansu a rufe ba kowa kamar jira yake saiga kiransa ina kika shiga meya samu umman taki amma baki kyauta ba kin yafi ba Neman izinina kefa amaryace me kwana daya a gidan ta amma ki fice ta fashe da kuka ba umma bace ba lafiya kaninane gamu a asibiti tagaya masa hatsari yai ni kuma na dauka umma akace Cike da tausayawa yace gashi nan zuwa yanzu da sauri tadinga Neman layin umman cikin sa a ta shiga ta zayyane mata komai minti goma sha biyar sai gata a fujajan kamar dama tana kusa
Chapter 2 · 0% Book details