Sashe 8
Arnan Daji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
tanayiba shigashi yana tsananin kaunarta Amma Bata saniba gata kyakykyawa me diri mtsww yaja tsaki sai da jeddah takare masa kallo ta tabbatar da yay mata ? Nan takada kai takama hanyar fita daga hall din taja hankalin maza dayawa saboda kyanta Amma batasu takeba tafuce waje tanemi waje tazauna tana jiran taga fitowarsa ayko kafin atashi taga ya fito da sauri shida wani abokinsa sun durfafo inda take Nan takara suma azaune saida sukazo gab da ita taga yabude motarsa da hanzari ta tashi ta isa gabansa Tace "sannufa" yay mata banza kamar badashi takeba, abokinsane yayi karfin halin cemata "sannu y'anmata ya kike? Ta washe baki tare da qara yauqi ta amsa da "lafiya lau" Nan suka hau zuba dama shine Wanda ya ganta tun a ciki ta tafi dashi shiko be auraba tunda yaga kamar Yar hannunce yad'ana Amma zefi san ya aureta, dataga wankin hula na shirin kaita dare saitace "abokinka baya maganane" yadan kalleshi a sace yaga yadda ya had'a rai ransa inyayi dubu ya baci sun barshi a cikin mota kamar bawansu, bayasan wargi Sam besan wanna shegen kwashe kwashen na faruk ya jiyo ya kalleta have "haka yake bikiga ya bude mota ya shigeba" "gsky yay mun" ya kalleta "Ni Kuma kinmun yaza ayi? " tai far da ido "naima kamar Yaya? " wani murmushi ya sakar mata irin nasu na 'yan duniya sannan yace "kinmun a matsayin matar aure" Dariyar ita ma Tayi sannan tace "kaban dariya wallahi ni gaskiya abokinka nake so shi yai mun shizan aura" ya'ke yayi don maganarta ta sosa masa rai amma ya dake yace "to ni a wane matsayin zaa ajiyeni?" "Abokina" ta fada da sauri sannan ta qara da "matsayinka kenan Kuma abokin mijina" Ya kalleta rai bace yace "To wannan da kike gani ansa masa rana Kuma bayasan babbar mace sannan baya kula mata". Ta dago ta kalleshi tace "wanne temako zakay mun yasoni ya kulani?" "Gaskiya babu" Ya bata amsa kai tsaye "zan dai baki card dinsa da number din wayarsa, Amma Ni mezaki ban?" Ya qarashe zancen da kashe ido irin na yan bariki, "hmmm me kake so ajikina kafada da kanka zan baka shi? " cike da murna yace "kinyi alkawari? " bata amsaba ya dora da "kawai so nake ki mallakamun kanki" Murmushi ta sakar masa na manyan bariki tace "dan dai wannan karka damu ka kwantar da hankalinka. "zanbaki complementary card dinshi, yadda zaki same shi a office da Kuma number din wayanshi shikenan ko? " cike da farinciki tace "shikenan ngde gaskiya" "to muje murage muki hanya". Tana tsaye taga kamar ya motsa da hanzari ta karasa kusa dashi tace "sannu kafarka? " saitaga ya bude idonsa Nan tacika da farinciki da gudu tafito waje cikin zumudi take kiran lamunde tana "Ya farka ya bude idonshi" lamunde ma cikin farin cikin tabiyota suka koma suka kamashi suka zaunar dashi sai binsu yake da ido ba umm ba ummun yakasa cewa komai kansa yakeji yay masa nauyi ya daure tam ya Kai hannu ya taba sai yaji a kulle yake ashe, yay shiru ya kasa magana Nan lamunde ta dakko masa maganinsa tabashi yasha shidai bece komaiba kawai binsu yake da ido, bai sansuba betaba ganin halitta irinsuba to Amma wayema shi meyake anan? beda amsar tambayarshi sannu suke ta doka masa yanata kallonsu kamar gumaka chan lamunde tace "begama hutawa be dawo hayyacinsaba mu kyaleshi ya sarara zuwa jimawa muje" suna fita Dan naci ta fakaici idon lamunde ta koma tasashi agaba tanata kallonsa tana murmushi. Tunaninta daya yaza ay tayi rayuwa dashi dama haka yake idanuwansama kawai abun kallone shine zetafi da ita inda yake ya aureta ko kuwa waye shima batasaniba tambayar dataketaywa kanta kenan tabbas inasan shi zan rayu dashi bazan taba gajiya da kallonsaba. Ja ene tsaye yake ta bala'I "kuka Bari ta kubce muku tafiku gudune ko Yaya wannan yarinyar itace zata tonan asiri wajen tenkwai tabbas idan tasamu wannan labarin bazata aurenba Ni Kuma itace rayuwata ita nakeso" cike da bacin rai damusa yace "haba sarki me jiran gado duk tarin kyawawan matanka Amma kace lallai sai wannan mummunar? " A fusace yasa wuka ya tsarge wuyansa sai jini ya Fadi Tim kasa matacce "duk Wanda ze aibaya tenkwai hukuncinsa kenan kodako kahone kyau bashine maceba diri shine mace Dan haka ita nakeji tamun soyyarta har cikin bargona take" can yay wani tunani sannan yace "tabbas dole aduke ta bakunci lahira a yau din nan da ita da rama bazan barsu surayuba saboda idan suna raye tenkwai zata dinga tunawa da abunda ya faru Amma idan na kashesu nasan zata kara tsoronna takara yarda dani ta Mika kanta gareni kawai Koda ba a daura aurenba" "bashari"ya Kira yaransa "yau tsakar dare tunda duhu ya fara zamuje mu kashe aduke suka sannan muje har gida mu cinye rama Dan zatai maiko" (yafara tandar baki ya tsohon maye Koda yake meye maraba yadama mayen ne) suka hau murna,ya wurgowa musu harara "kufara shiri so nake akashe aduke abar gawarta amma ita nasanja shawara ba yauba saboda gobene bikin cin jarirai Dan haka a barta sai ankwana biyu adai kashe aduke yau" Nan suka hau ihu suna murna. Mahaifiyar ja'e ko abun duniya ya isheta tabbas sunada bukatar sanjin rayuwa jikinta nabata wannan bakon shize kawo musu sanji tayaya take wani tunani yazo mata ze zama daya daga cikin bayin bangarenta su goma ne Amma akwai wani tabbas kamarsu guda da wanchan sai dai shi be cika haskeba Amma ay akwai dabara akwai abunda suke sawa me rinar da fata shizatasa masa ta sallami wanchan ya gudu Amma sai ya warke. Take tasa aka kirawo mata darzan yana zuwa ya zube "angaisheda uwar tausayi uwa agun yariman masarautar kuguru" "magana nakeso miyi dakai kasaurareni sosai idan ka kuskure hukuncin kisane akanka inaso nanda Dan wani lokaci zan umarceka dakabar garin nan zansaka a hanya kafita kabar garin nan ka koma beguwa tunda su naji anacewa suna dai bautar gunki Amma basa cin mutum Kuma suna karbar bako yafi kusa da garin Nan idan Kuma zaka iya ka karawa gabama to ka kara" nan yace "ranki ya dade inada mata da d'a" "kabarsu kaje idan komai ya nutsa kadawo garesu" cike da murna yay godiya Amma kasan ransa yana jimanta yadda ze rabu da matar sa da d'ansa "karka kuskura ka nuna musu zaka bar wannan gari nasan yadda zanyi dasu kawai". Dare na tsalawa suka dauki hanya suka shiga gidansu aduke suka sadada dakin suna shiga sukaga mutum a kwance kawai suka Burma mata wuka tasaki ihu suka kara mata suka daddatsata cikin Daren Nan ga gari da duhu suka sa kai suka fito suna fitowa suka hau sowa da murna saura daya burin ubangidansu ya cika ya mallaki abar sansa duka da anmasa alkawarin aurenta amma yafiso ta amince masa yayi wannan alkawarin saita soshi baze taba sa mata karfiba kamar yadda yakeyi soyake tabashi hadin Kai yaji Dadi ya morewa wannan jikin nata me masifar laushi cike da farin ciki yashiga turakarsa ya kwanta. Ahankali take takawa saboda ba isashshiyar lafiya tana shiga taji tana taka abu tana dubawa taga jini mezatay tasaki wata kara anan tafadi tasume. (tofa muje zuwa akara hakuri dai fans ??????????bana samun damar typing me yawa abubuwan sunmun yawa kuyi hakurin biyoni kudai yanzu labarin yasoma) *feedyn bash* [9/11, 22:29] +234 810 679 5647: *?ARNAN DAJI?* *NA* *FAREEDA ABDULLAHI* *_?KAINUWA WRITERS?? ASSOCIATION_*?? ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation GAISUWA DA JINJINA AGAREKU MASOYANA INAJIN DADIN YADDA KUKE COMMENT DINKU AKAN ARNAN DAJI NAGODE SOSAI