Sashe 15
Arnan Daji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*FAREEDA ABDULLAHI* *_?KAINUWA WRITERS?? ASSOCIATION_*?? ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *GAISUWA ME TARIN YAWA GA MASOYANA DAFATAN KOWA NA CIKIN KOSHIN LAFIYA INA BARAR ADDU ARKU INADA WATA BUKATA A WAJEN ALLAH DAN ALLAH KUTAYANI ADDU A ALLAH YABIYAMUN ITA NAGODE MASOYANA* WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA MAHAIFIYATA ALLAH YAJA KWANA *BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI* 65-70 Hankali tashe iyar Ja'e ta leka tace suje anji sun sani ay sukan su abun ya basu mamaki na ganin iyar Ja'e meya kawo ta oho ita da Sam Bata shiga wasu abubuwan dasuka shafi gidan sarautar koda yake ita dazata aurar da danta komeye namu ma oho suka wuce suna ta shelarsu hankalin su kwance cike da farinciki A guje Rama ta debo ruwa ta zuba Mata ta farfado kuce mafarki nake kar kuce a gaske naji wannan batu tabbas badu be chanchanta da zama abun bautaba tunda ya kasa temakona akan wannan hali kullum sai na Kai Masa kuka na amma be taba amsa mun ba kullum susuke nasara akan kowa da komai Tai shiru tana ta sheshsheka Aduke ta taso da kyar ta dafa ta karki damu Yar uwa kiyi hakuri ki aure shi kodan ki daukar Mana fansar abunda yai Mana bazan taba yafewa Ja'e ba kobayan Raina karku kyale shi ku daukar mun fansa keda rama iyar Ja'e ta dago fuska jage jage da hawaye dama shine shi yai Miki wannan abun Dana sameki cikin lalura meyai Miki tana girgizata kigaymun mana kuka kowa yake anrasa me magana a cikin su Tabbas nayarda akwai wani ubangiji bayan badu Wanda shike bamu ruwan sama Amma bamu San shi ba kullum addu ata haske yazo wannan gari inga Wanda ze kawo karshen mijina da Dana bana kaunarsu ko kadan basu kasance masu tausayin na kasa dasuba su kansu kawai suka sani basa tausayin kowa Banda burin dayafi Naga karshensu Tenkwai ta dago ido cike da tausayinta tabbas batai sa a ba a rayuwarta baga miji ba Baga da ba duk mugaye masu munanan dabi u azzalumai masu danne hakkin kowa nice zan kawo karshen Ja'e nizan auri Ja'e nayarda zan aure shi zan kawo karshen shi zan koya Masa darasi a wannan duniyar tamu Cike da mamaki lamunde ta kalleta kin amince zaki zauna da azzalumi bashi da imani sam kema kashemun ke zeyi shike Nan kema zan rasaki tamkar yadda na rasa Dan uwanki na rasa mahaifin ki sai kuka dama inada Dan uwa meyasa baki taba gayan ba yana Ina Ina ya shiga Lokaci na zuwa da zan baki tarihin rayuwar mu a wannan gari zakisan matsayin mu awannan gari na kuguru na Miki alkawari ranar bikin shekara na abun bauta badu zan sanar dake komai da duk abun da ya faru a Rana me kamar ta wannan zansanar dake koma wace ke a garin Nan Gaba daya lamunde tasa kowa a cikin rudani gashi duk Wanda yay magana a cikin su sai ta daga Masa hannu Bana bukatar tambayar kowa a yanzu Amma kamar yadda nai alkawari gaba dayanku ku taru ranar zan Baku tarihin mu Nan da wata biyu masu zuwa kowa yai shiru an rasa me magana Nayarda ki auri Ja'e Amma kamar yadda iyar sa ta fada Ina bukatar zamanki a sashen ta Dan nasan baza ta taba Bari ya cutar min dake ba kuta shi kuje kuduba Mara lafiya suka mike suka koma dakin da Mara lafiyar yake duk yana jin meke faruwa a waje ya Kura musu ido yana binsu da kallo daya bayan daya Iyar Ja'e ce ta shigo dakin mado kowa yay shiru ta karasa kusa da shi sunan ka mado kasamu rashin lafiya ne Amma Kai bawana ne a gidan sarki Ni matar sarki ce Babar dansa Ja'e magajin garin Nan a sashina kake Dan haka ka shirya komawa bakin aikin ka zan sanar wa da matarka da danka rashin lafiyar ka bansan inda kasamo wannan kayan ba ba irin namu bane Dan haka yadda kaga shigar mu take Kai ma taka zata koma haka kana da kyan jiki da wuri zaka warke Yai Mata shiru yana ta tunani tabbas yanada Mata da da Amma kamar ba a Nan suke ba ba irin wannan kayan suke sawaba Amma baze iya tunawa ba Tom shikenan Ina Mata ta da Dan nawa inaso zan gansu zan koma wajen su har na warke Inasan su zan zauna dasu Ranta kal tace suna gida kabari kaji kwari Nan da kwana biyu saika koma Amma zan dawo gobe na dubaka naga ya jikin naka yake sai na taho ma da kayan naka kasa a jikin ka muba ma amfani da wannan inda kasamu lalurar ne suka sama Amma mu da wannan mike amfani bana so kasanarwa da kowa kowa ya tambayeka kar kace komai Koda ko matar kace kar kace nice nasa aka Fara dubaka Gaba dayan su mutuwar zaune sukai jin wannan batu kamar almara me take nufi zata tafi dashi su cinye kenan hankali tashe tenkwai ta bude baki zata Fara magana ta daga Mata hannu muje Inasan magana daku ta fice suka bi bayanta suka shiga dakin lamunde har da aduke data ke takawa da kyar ta dinga basu hakuri su rufa Mata asiri su rufe wannan sirrin ta zayyane musu duk Shirin ta jikin su yai sanyi da wannan tunani nata tabbas suna Kama da mado ba me ganewa idan aka turashi tunda Suma wasu na tirin baza a ganeba Kuma wannan ce kawai hanya daza a tseratar da rayuwarsa Rama tace iyar Ja'e na Miki alkawarin zan tira shi kafin ranar daze koma wajen ki nayi alkawarin kula da lafiyarsa har ya warke kafin tunanin sa ya dawo bazan janye ba ki dauke Ni matsayin me kula dashi yadda matar mado bazata zargi wani Abu ba bare har asirin ki ya tonu Cike da farinciki iyar Ja'e tace tabbas kinyi gaskiya naji Dadi da kuka fahimceni kinga kema baze Miki nisa ba ta dubi tenkwai duk San da kike son ganin sa zaki gan shi tunda bayina Ni a bangarena suke banasan siyi nisa dani a Daren yau mado Dole ze bar gari duk da hatsarin dake tattare da tafiyar say Amma Dole yase da ransa bamu San me wannan mutum yazo dashi ba bamusan alherin dake tare dashi ba sai ya warke Cike da farinciki ta baro gidan tana zuwa kofar shiga gidan wazata gani sarki kaho fuskar Nan a tamke daga Ina kike munafika kinje wargaza auren gudan jinina ko to baki isaba in Banda kece mahaifiyar sa da tuni nasa anbatar dake Dan nasan bakya kaunar mu nida shi zan iya kashe ki akan Ja'e Ta sheke da dariya kaho kenan da bakin ka kace nice mahaifiyar sa Dan haka baka Isa Kai min shamaki da Dana ba ba tsoron kasa a kasheni nake ba zan dai gayama ne kawai Dan ra ayina shawo kan yarinyar naje yi abun da ka kasa sai nuna Isa da iko akan Wanda ba danka ba ko danka baka iya tankwara shi bare Dan wani kuma sai gashi Ni makiyarsa na Samo Masa farinciki sabanin Kai masoyinsa daka kasa yarinya ta amince saboda Ni zata auri Dana Dan haka kaga karshen kiyayya kenan Gashi dai magana tagaya Masa Amma kamar ta sashi a aljanna Dan farin ciki tabbas ta bashi farinciki be taba tunanin zata iya nemar wa Ja'e aure ba sai gashi ta fada karya ba dabi arta bace balle yace ita tayi ransa Kal ya kalleta In dai ko hakane ki Fadi duk abunda kikeso zan Miki bansan kina San gudan jinina ba sai yau me kike bukata ai miki kinyi abunda mu muka kasayi Dole kema a faran ta Miki Bana bukatar komai sai yarinyar ta zauna a sashena Dan haka take da bukata Ni Kuma farinciki shine namu Dan ta Mana halacci yarinyar Hhhhhh in dai wannan ne an Miki Ankara muku bayi Mata guda goma sannan anhada muku da kyautar shanaye guda goma hhhhhh kin kyauta muna godiya masoyi yata a shirya yau a bangaren ki zan kwana Tai tsaki a ranta base kazo ba badu yaja da ranka shanu Kuma mu bazami komai dasu ba gwara bayi kodan ita amarya Dan haka kabar shi karya kike Dole dake zan kwana yau Kuma baki ISA nayi kyauta ki dawon da itaba Har zatai magana ya juya ya tafi fadawan sa suka rufa masa baya wata zuciyar tace karshema tun nakune suke ta albarka ki karba kici gaba da kula dasu harsuyi yawa kidawo da yawan shanunku ta share kwallar data zubo Mata saboda tunawa da iyayenta tabbas sai ta dau fansa akan sarki kaho ta juya ta nufi sashen ta Ummata albishirin ki bukata fa ta biya suka rungume juna sunata ta murna umma harda guda afra Bata San wainar da suke toyawa ba batasan akan me ake maganar ba tace wai farin cikin me kuke ne abani Nima Nasha adara Dani ba a barni abaya ba Yar uwa Cike da farinciki tace wallahi sis nayi babban kamu wannan dakika ganmu tare suhail ne Dan gidan alhaji ibrahim gadon kudi shine ze aure Ni Nan bada dadewa ba sai ki Fara shiri daga yau Ido waje aure Jeddah aure yanzu kinsan a tsarinmu ba aure yanzu yaushema har kukai maganar aure dashi baki gayan ba a Ina kuka hadu baki taba gayan ba dama bazaman Amana kike Dani ba Ni bana iya boye Miki sirrina kece ke boyen naki Mtsww kina da matsala wlh jiya muka hadu Kuma yace yana San aurena sai anjima zezo zami tsaida magana kinsan ba Wanda ze Fara ji sama dake Kece zaki gayawa wasu ma kece fa Babar kawa sai yadda Kika yi Sai abunda kikace a wajen bikin Nan Hmmm shikenan yanzu naji zance Amma aranta Bata so ba Bata so Jeddah zatai aure ta barta ba tafiso siyi ta gantalinsu tare Dan Jeddah ita tabude Mata ido sosai gashi zata tafi tabar ta gaskiya bata ji dadin hakan ba ita kuma gsky yanzu karatu ma takeso ta koma Dan gayen jiya yy Mata alkawarin daukar nauyin ta Cike da murmushi tace Tom kawata Allah yasan ya alkhairi yakaimu ranar Amma fa