← Book details Arnan Daji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 31

Sashe 11

Arnan Daji Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

parking rai bace faruk meye sunan abokinka naga baya magana faruk yay dariya suhail kenan ai miskiline baya magana sosai ran suhail in yai dubu ya baci dan Allah jibi yadda yadda yake ta washe mata baki mtsww ya ja tsaki yadau waya yakira budurwarsa haleema cike da shauki yake maganar ran gimbiyata yadade nasan nayi lefi tuba nake kiyimun rai karki fushi kinsan kece rayuwata gaba daya Ai jeddah jitai gaba daya ta muzanta ya gama da ita agabanta yake cewa wata itace rayuwarsa a fusace ta bude motar ta fita faruk yai maza ya bita gimbiya ta yazaki tafi bamu gama magana ba kaina ne yake ciwo zanje gida mayi magana wata rana baki ban no dinki ba cewar faruk ka kyaleni Dan Allah bazan bakaba suhail ko ya gama wayar yana jinsu meko zeyi inba dariya dariya yake kamar cikinsa ze kulle maganinka kenan na mamajo kowa kagani kana so Jeddah tasa Kai ta shige gida ranta a kuntace ko sallama Bata iya yiba dama ba damun ta tai ba da chokareren takalminta ta shiga dakin ta tana zuwa ta zube a katifar ta luntsumemiya ranta a kun tace tana ta saka da warwara Haka suka kwana zuciyoyinsu a jagule gari be gama wayewa ba sukaji kakarin mutum yanata ruwa ruwa ay da gudu suka Mike suna Yar rige rige saboda duk cikin su ba Wanda yai bacci kawai juyi suke cike da damuwa suka dai suka San abunda ke damun zuciyoyinsu gasu suba musulmai b bare suyi sallah Kai musulunci yayi Allah ka kara Mana tsoronka da biyayya agaremu ka kashe mu cikin bautar ka A guje tenkwai tadebo masa ruwa Rama Kuma tai dakin tana zuwa ta tallafo shi sannu sannu basu ya baka lafiya ya zuba Mata ido yana kallonta waye Kuma badu besan shiba tenkwai ta shigo da ruwa jikinta har rawa yake kamar mazari Rama ta karba ta bashi Nan ya kafa Kai sai da ta janye Dan karya kulle shi cikin sa ba komi yadinga binsu da kallo suwaye ku Ina ne nan wanene ni cike da tausayinsa tenkwai ta ce tsintarka mukayi a ruwa waye Kai Ina ne garin ku kayi bayani musaka a hanya idan suka ganka zasu kashe ka Amma Ni zan bika cewar tenkwai ya kara kallonta kawai yakasa tuna komai na rayuwarsa bana iya tuna komai iya abunda yace kenan Amma Nan ba iri na bane ku tabbas katuna Mana cewar rama shiru yay be kara cewa komai ba Rama ce ta mike zoki ji tenkwai ta mike ta bita tana ta waiwayensa wai shine ya tashi har yake ta magana haka ranta kal burinta ya kusa cika Rama taja tenkwai gefe akwai damuwa saboda ya samu cutar mantau sai kuka tabbas Rama bataso haka ba Amma tunda tagan shi tasan sai anyi haka saboda ciwon dake kansa ya taba kwakwalwarsa gwarama mantau din Ana dawowa akan ace hauka yake jagwab tenkwai ta zube tana ta kuka abubuwa sun musu yawa wannan gari babu adalci cikin sa bazata bar shi ya rayu a ciki ba zata San yadda zatayi Rama jaruma ta durkusa ta gogewa tenkwai hawayen ta nasan yadda kike ji a ranki game da soyayyar wannan mutum wannan itace damar dazaki amfani da ita ki mallake shi tunda yana cikin mantau baze iya tuna komai ba ze soki ya kaunace ki a hakan da muke a cikin jeji saboda beda wani zabi a yanzu (gaskiya Rama kina burgeni jaruma ce ke kujifa wata sadaukarwa duk da San da take masa kawance na gaskiya kenan)ta rungumeta kin kawo shawara me kyau Amma Dole sai bayan na auri Ja'e na kashe shi sannan wannan alkawari ne saina cika shi sannan tawa duniyar zatai mun Dadi um um kibi a hankali duk yadda kike tunanin Ja'e ya wuce Nan karki fara kibi komai a hankali yanzu tashi muje muga aduke bekamata mu yasar da itaba tun jiya bamuje mun Kara ganin taba gaskiya fa hakane bamu kyauta ba muje maza nasan tana jin jiki gashi ba asa Mata maganin ba muje muganta sai mu wuce daji mudebo Mata maganin Amma bazan je wanchan ba banaso naga gawar babana sai hawaye suka zubo mata muje na chan gaba da gari hanyar beguwa Suka fito suna tafe Rama tana ta hawaye saboda tunawa da abun da Ja'e yay wa mahaifinta Yanzu fa shikenan ya cinye shi Kuma kashe shi yayi gwara ace mutuwa yayi taga gawarsa data ga wannan bakin lamarin Amma yazatayi ba Wanda ya damu da damuwar wani a wannan garin kowa ta kansa yake kanayin Abu kadan za a kashe bakin ciki yai wa mutan wannan dajin yawa dame zasuji tana musu fatan su Sami chanji a rayuwarsu Koda bayan ta gushe ne a duniya Dan tabbas zata kashe kanta rayuwarta Bata da amfani
Chapter 11 · 0% Book details