Sashe 18
Arnan Daji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
70-75 Jeddah ta dalawa afra duka tashi kawata yazo wallahi yana waje narasama wane irin kwalliya zanyi wane irin kaya zan sa Dan na burge shi na tafi da zuciyarsa gaba daya tabbas malam yayi gaskiya suhail yazama nawa Ni kadai Maza tashi ki shirya kina shegen zance sai ya tafi kinsan ba karamin mutum bane cewar umma data ke sawo Kai umma wanka zanyi ke banasan shashanci wankan ubanki zira Kaya ki gyara fuskar ki fita afra ko ta kasa magana kawai binsu take da ido ta rasa wannan San zuciya na umma da Jeddah ita dai Bata burin auren asiri tafi San na soyayyar gaskiya Dan shine ginshikin rayuwa Allah ya kyauta tafada a ranta Cikin hanzari tasa wani less me kalar ja da ratsin ash dinkin Riga da siket ya karbeta duk halittun ta ba inda be fito ba tayi kyau na mamaki batayi wata muguwar kwalliya ba ta daura Dan kwalinta ta fito tashiga dakin umma Nan da Nan jiki na rawa tahau bulbula Mata turaren ita kanta jitai yana hawa Mata Kai ya isa Dan Allah umma wannan turaren ba Dadi kamar na Yan bori Dan Allah barshi haka karya kadani To uwar kinibibi koma na meye shige ki tafi karki Mana asara ba malam ne yace yana shakar Saba sai dai wani bashi ba Kuma kinsan irin tsadar maganin nan maza ki wuce Yar albarka ki shigo dashi mu gaisa ta balla Mata harara ke kin cika rawar jiki wallahi daga zuwan farko zezo wani ki gaisa ko kunya bakya ji jibi fa yadda kike mtsww tayi ficewar ta Ai tana dosar wajen sa yai mutuwar tsaye wani masifar kyau yaga ta kara fiye da dazu tana zuwa kusa dashi wani kamshi ya dake shi ya dafe kansa yafi minti biyar be dago ba itama Bata tanka ba gabanta yanata faduwa kodai zaton ya yahau Masa Kai sai taga yadago idanunsa sunyi jajur ya kalleta tadan firgita ita kanta dataga yadda idanuwansa suka Sanja kala suka rune Nan da Nan Cike da kasala ya Fara magana Jeddah inasanki sai da tsigar jikin ta tashi Ina kaunarki zan aure ki a lokaci kankani Nan kusa zan aureki ki amince min zuciyata zata fashe bazan iya jurar kallon kiba batare da kinzama mallakina ba banasan auren mu ya wuce wata daya kiyi magana Dan Allah kar na mutu kirjina Kamar zata zuba ruwa a kasa Tasha Dan murna zuciyarta Kal bukatarta ta biya me Kuma zata nema a duniya yanzu ta Gama samun duniya amma sai ta basar aure suhail aure kace fa bayan kasan faruk ke sona Kuma cikin wata guda Ni marainiyace Banda mahaifi sai mahaifiya mu masu karamin karfine kafi karfina kanemi dai dai dakai kawai nasan iyayenka nazasu yarda ka auren ba Ambatar sunan faruk datai kamar ta watsa Masa ruwan dalma a zuciyarsa saboda masifar kishin daya yunkuro Masa Amma ya danne bakinsa har daci yake faruk ba aurene a gabansa ba yanzu ki bani dama na nuna Miki nafi kowa sanki a duniya zan aureki cikin lokaci kankani iyayena basu da matsa ba dukiya nakeso ba ke nakeso zaman lafiya nafi bukata sama da kudi wane irin kudine bamu mallaka ba daza a karbe duk abunda na mallaka abani ke nafi bukatar hakan akan komai ya wani marairaice Mata Itako dake tasan komai ta wani basar chan tayi shiru kamar bazata Kara maganaba shikenan suhail nizan koma ciki Amma kaje Kai shawara da iyayenka Nima zanyi danawa Amma kagaya musu mu bamu da komai talakawane mu masu rangwamen gata Banda mahaifi sai danginsa a adamawa ta shiga matsar kwallar farinciki shi Kuma yadauka tunawa da mahaifin tane ko Kuma talaucin dasuke ciki ya kudiri aniyar ciresu daga kangin talaucin Yakara narkewa a tausayin ta shike Nan zan gaya musu insha Allah cikin satin Nan za a Gama komai atsaida Rana kigayawa mamanku tasanar da danginku zan turo ga wannan ba yawa ya zaro rafar dubu dari ya Bata sai na dawo gobe ko kabar shi Dan Allah wallahi sai kin karba harda rantsuwa Tom nagode besan sutafi bukataba shikenan shiga gida dama sakon kenan yanata murmushi tashiga gida shi Kuma ya tada motar ya bar wajen Yana tafiya yana tunanin Anya ma ko shine tayaya za ace yaje wajen wata ba haleema ba harda maganar aure tabbas idan be auri jeddah ze iya mutuwa ita yakeso da ita ze rayu ahaka ya karasa gida ya shiga sashen hajiyarsa yai sallama ya shiga suna tarema da alhaji ko tsoro Babu bare fargaba aransa ya shiga falon Yauwa naji dadin ganin ku tare hajiya dama magana ce nakeso miyi daku daddy aure nakeso nayi cikin lokaci kankani cike da farinciki hajiya tace to candy Dinma bazaka barta tayi ba takarasa a dakinta saura shekara daya fa tagama kayi hakuri Mana suhail bansan ka da wutar ciki ba alhaji ma yai dariya kabari takarasa mana ko babban mutum ko dai kafara matsuwane ya fada cike da murmushi Yai shiru ya numfasa hajiya ba haleema bace wata ce daban wannan mun hadu da ita a wajen bikin abokina Inasan ta sosai Amma talakawane shine nake Kara tausaya Mata so nake Nan da wata daya ai auren nan da sati daya nakeso agama komai sai asa bikin sati biyu kitemakamun Dan Allah yai rau rau kamar ze kuka Hajiya jin abun take tamkar mafarki Kai suhail baka da hankali ko kafara shaye shayen zamani karka maida mu kananan mutane Mana ita haleeman kayi Yaya da ita ko Kuma so kake ka yaudarar musu yarinya wannan wane iskancine haka kaji yaro Dan Allah alhaji ya daga Mata hannu Ya isa hajiya namiji mijin mace hudu ne Dan haka indai tanada tarbiyya zan aura Masa ita Amma da sharadin idan haleema ta karasa karatun ta ze aure ta wannan Dole ne hankali kwance yace na amince ko a rana days nema a daura hajiya kamar zatai bindiga yanzu suhail ko mahaifinka be zauna da Mata biyu ba sai Kai kana yaron ka dakai me kake nema haka indai wajen Nan ne kake kwadayi wlh saika gaji dayi mtsww Ya isa hajiya cewar alhaji halitta halitta ce Kika sani ko yanada karfin daze iya jurewa Mata hudu ma Dan haka inbazaki Fadi alheri akan wannan lamarin ba kiyi shiru fatana ya kasance adali karna Kara jin bakin ki indai ba albarka zakisa ba tashi kaje zansa ayi binkice akanta Dan haka karka damu zan sanarwa iyayen haleema kaima kuma kagaya Mata to daddy ya Mike ya fita ransa Kal yanaso ya Kira ta beda number dinta ya manta be karba ba Tana shiga tafara rawa a tsakar gida Nan uwar ta tayata afra ta fito ya akai ta kwashe komai tasanar musu dan haka kafin dare ma yayi zomu koma wajen malamin Nan afra tunda nagane ki zamanki bama sekinje ba umma wa wallahi Dole muje tare Banga ta zamaba haka suka dauki hanya sai gidan malam suka zayyane Masa komai yai dariya tabashi ragowar kudinsa takara Masa dubu ashirin yai Mata daurin baki saboda ko anzo bincike kowa yakasa aibata ta dama Kuma tana Dan musu ihsani duk da haka dai akara rufe baki saboda wayanda Bata sani ba afra ma tasa akama Mata gayen ta a hannu me suna Jameel yace ba matsala suka dawo gida suka shirya ita ta tafi nata wajen afra tabi Jameel wannan kenan A ranar da iyar Ja'e ta koma tasa mado ya bar gari adaren ranar washe gari matarsa ta fito tana ta nemansa be kwana a daki ba Dan besaba irin wannan ba iyar Ja'e tace ta kwantar da hankalin ta zatasa ane Moshi labari yazagaye gidan ba aga mado ba hankalin kowa ya tashi Dan mado yanada kirki mutum ne na mutane Rama ce take cirewa suhail Kaya Tai masa tik haihuwar uwarsa gaskiya wannan sura Tai Mata ga banana Masha Allah tagama kwadai Tuwa Amma Ina tasan ba fuska gaka ta tire Masa jikinsa tsaf fatar sai Tai duhu ya koma sak mado gaskiya tana sansa Amma yaza tayi tariga ta hakura tabarwa tenkwai duk da aure zatai Amma tasan na daukar fansa ne zata dawo wajen abun sonta Sai ga aike daga iyar Ja'e nakayan sa irin nasu Tenkwai ta karba ta mikawa Rama Dan ita kunya takeji bazata iya shigaba shi kansa kunya yakeji Amma yazeyi baya iya control din kansa saboda har yanzu jikinsa be Gama murmurewa ba a hankali tasa Masa ya koma sak arnan daji yazama mado ta kara sa Masa magani tagyara Masa kan tanade shi ya fito waje yana binsu da kallo lamunde ta kalle shi cike da murmushi a ranta tace kamar dama chan Dan garin Nan ne Rana Bata karya sai dai uwar diya Taji kunya ayaune ranar bikin cin jarirai ta garin kuguru ayaune Kuma ranar daurin auren Ja'e da Tenkwai idonta ya bushe ba alamun kuka da kanta Bata jira an aiko tafiya da itaba tacewa su lamunde taje gidan sarki da kanta su kwantar da hankalinsu suci gaba da kula da aduke ita kuma zata kula da bakonsu tana shiga gidan sashen mahaifiyar Ja'e tayi Nan aka dinga murna Ana sowa ga amarya tazo da kanta lallai tabada Kai hankali kwance akadinga Mata ado irin nasu na aljanu to aljanu Mana dan kamar aljana haka ta koma saboda ado ga shirgi da ake ta Tula Mata Ja'e ya samu labarin amarya tazo dakanta kamar ze hauka Dan Dadi da gudu ya garzaya fada yaiwa kaho albishir cike da farinciki suka rungume juna nagayama tana sanka tana kaunarka Baga shiba tazo dakanta yanzu zata fito fada ai tunda angama dafawa yanzu za afara ci a a kar afara ci afara daura auren tukun to shikenan afito da ita Kowa ya fice ya tafi fada andauki amarya ankai ta fada itama fada ta cika makil yarage saura iyar Ja'e datace tana zuwa yanzu akwai abunda zata yi Sai wata baiwa data aika ta gidansu Tenkwai tace agayawa Rama ta shirya ita take jira da hanzari taje ta isar da sakon Dan karta rasa naman Wuri yayi wuri fada ta cika makil inda akayi shelar kowa yayi shiru za a daura auren Ja'e da Tenkwai kowa yai tsit Nan me daurin aure ya Fara aka Kira Ja'e aka