← Book details Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 25

Sashe 7

Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*11(K)*
*KAINUWA WRITERS
ASSOCIATION*
daya bayan daya sukaringa cire kayannasu suna sakawa acikin ruwan omo wannan yazame musu jiki dake tana rigasu dawowa takan dawo gida daya saura sukuma sai daya da kusan rabin suke dawowa,
tana shigowa gida take zazzaga omo cikin roba ta zuba ruwa duk Wanda yadawo takanyimar tinin cire Kaya yasa aciki ita Kuma nana tana dawowa before sutafi Islamiyya saita wankesu ta shanya.
Bayan sungama cin abincine sukayi sallah sai ta dan dimama musu ruwa domin yin wanka dan garin iska na kadawa haka takamasu daya bayani daya tayi musu tayi musu ita Kuma nana tana shafa musu Mai tare da saka musu kayan islamiyya basu Shari awa daya da dawowaba har sun kammala shirinsu yaran gwanin Sha,awa dukkaninsu suna tsaye domin tafiya Nana ce bata fitoba suke jiranta ganin batada niyyar fitowane yasa karimatun takwalla Mata Kira amsawa tayi batare da ta fito ba,
Girgiza Kai tayi tareda mikewa domin binta cikin dakin tana lura da ita tinda ta dawo batada walwala bakuma yarasa nasaba da zancen ko na makaranta ne ,
Sanda tashiga dakin tana tsugune tana lalube cikin Jakarta kudi take hadawa Yan goma gomane birjik da Yan biyar da Yan ashirin agabanta tanayi tana goge hawaye dasike tarar mata
Nana kifuto kutafi kinasawa suna makara shiru tayi sanda taga tana goge hawaye tare da goge majinar hancinta.
Wani abin nayi Miki dakika shigo daki kina kuka ?
Niba kuka nakeba .
To meye kike kenan ko wani abin akayi miki
naga tinda Kikashigo kike fushi kigayamin abinda Yake faruwa , wannan kudin Kuma dasuke gabanki nawaye ?
Shiru tayi batare da tace komaiba ita kanta dan bayar da zata yine tana tausayawa umman tasu dawainiyarta tana yin yawa amma dole sai Dole shiyasa ma takan jure horon da ake Mata narashin biyan kudin term Akan lokaci.
Magana nake Miki inkuma bani da muhimmanci Kan lamarin ki sai inkyaleki.
Dama Kan kudin term ne kullum sai ance inkawo kowa ya biya Ni kadai ce ajinmu ban biya ba yauma koroni akayi to Dana futo titi nayita tsayiwa bansami abin hawaba shine wani malami yazo wucewa ya ganni atsaye sai yasani gaba yamayar dani yace gobe inkawo inba hakaba kar nazo,
Gauron numfashi taja tare da furzarwa tayi murmushin Yake tace auke wannan ne yasa ki fushi kina mace har Dan wannan abin zaisa ki karaya ai ita mace kullum da dauriya akasanta yazamana duk inda Kika juya Zaki jure Amma dan Dan wannan har kike fushi tashi kutafi gobe in Allah ya kaimu babanku zaije sai ya basu abinda yasamu inkuma Basu samu ba sai ya basu hakuri insha Allah duk za,abayar har na kannanki ending this month insha Allah.
Goge fuskar tayi ta amsa da Amin .
Af wannan kudinfa nawane nagansu tirmis a gabanki?
Kudina ne nake tarawa na makaranta Wanda nace miki zamuyi yayin mauludi.
To mezakayi dasu kike ebowa keda Zaki tafi makaranta kinbar Yan uwanki atsaye sai kinsa anyi musu bulalar makara saboda Allah.
Jiyane akayi musu bulala amakaranta sabida basuje da kudin wataba shine damuka taho hanya nace musu zanbasu yau sukai inada kudi agida kirgawa zanyi nagani inzasu Kai sai nabasu inbasu kaiba Kuma ko mutum biyu sai na bawa .
Ido ta zuba Mata tarasa ta inda zata fara komai nema Yake ya kwance Mata inta bullo tanan sai wani abin ya bullo tacan.
Tace nana karkiyimana haka nasan ke yanzu kinfara hankali ko na boye Miki wani abin dolewani Zaki fahimta Daban shigo dakinnan ba Haka Zaki tafi da wadannan kudaden kibasu bansani ba ?
Zaki fara nunawa Yan uwanki gazawarmu ne duk fadi tashin da akeyi dominku yatashi awofi kenan,
Shiru tayi nadan lokuta tare da zubawa yar tata Ido ta hango karaya atare da ita domin kwayar idonta ta nuna balle datayi la,akari da hawayen dake satata a idonta.
Tace ba kuka zakiyi minba magana nakeso kiyi domin inji tabakinki.
Bahaka nake nufiba nidai kawai basu zanyi nasan in sun gaya miki yanzu bakida kudi hankalinki ne zai Kuma tashi shiyasa Zan basu amma bada nufin hakaba kiyi hakuri umma
Shikenan amma karki Kuma haka in ma basun zakiyi kiringa gayamin sai ingaya Miki yadda,zayi shi yaro indai Yana da iyaye baya girma komai zayyi sai yayi Shawara karki Kuma yankewa kanki hukunci kowane irine batare da kingaya minba ,
Ki tashi kutafi kice da malaman zanzo da kaina in anjima nakawo musu .
To umma inba fushi kikayiba kibasu wadannan sukai ko Basu kaiba inyaso inkinzo din Kya cika musu ( tasan dai karshenta ban hakuri zatayiwa malaman kafin asamu akai).
Toke nana Wanda yaje yakai irin wannan kudin biyar da goma ai yanemowa kamsa abin magana yadda wasu malaman suka lalace sai kiji ansa muku suna Akan wannan kudin Basu San da yadda aka hada kudinba gara Baku kaiba da dai Yan hamsinne to da sauki wani yanzu aciki inkuka Kai yaringa kiranku Yan biyar da goma.
Dariya sukayi tare sannan suka fito suka tafi suna muntafi ita Kuma tana yimusu tinin addu,ar fita daga gida sannan ta bisu da addi,ar allah ya kiyaye ya kuma tsareminku, mutuncinku ,kimarku lafiyarku ,sukuma suna amsawa da amin.
Bayan suntafine tacigaba da kujiba kujibarta daki tashiga ta hau bincike wata tsohuwar wayar shu,aibu ta dakko domin yadena amfani da ita ta Dade da lalacewa shine ya ajiyeta da yara sun fara Wasa da ita shine ta dauke ta adanata ,juyata tashigayi tana cewa kozasu siya masu way gata dai da kyanta afuska bansaniba ko za,asiya , haka tadauki waya ta bugawa shu,aibu domin neman iznin fita Gaya Masa takeyi zata makarantar su nana sabida matsalar kudin wata harta ke cewa kozasu Sami wani abun sai arage kodaga bayane acika.
Wai wai wai ita yafara ambata yace anya ko zasu samu toow sai dai ko innadawo din za,a duba amma kije kibasu hakuri za,a biya insha Allah.
Haka ta ajiye wayar jikinta asalube dan duk sanda yayi Mata irin Haka jikin mutuwa Yake kumayi kullum mutum ba karfin gwiwa atare dashi kullum babu haba haba abin Yana neman yin yawa .
Sai Kuma waji wani tinani yashigeta toma mezai bata mutumin da kullum sai ya Kare karfin aljihunsa kafin yabar gidan nemannan dai shine tinkan ya aureta Abu days ake samu gashi har sun tara yara akan kadami guda Aiko hakuri yazama dole inhar tana neman kwanciyar hankali gareta da yayanta dashi kansa mijin Musamman domin bashi karfin gwiwa gurin nemi musi abinda zasi saka abakinmu salati.
Goya nana Fatima tayi ta kulle gidan bakin titi tayi gurin masu Saida ways Basu tayi tace su siya naira dubu da dari daya aka siya ta kirgi Yan ashirin na naira dari ta hada suka Zama dubu da dari biyu dama dari biyune kudin watan aiko saigashi take ta biya tare da Kara basu hakuri najinkirin dasukayi gurin biya.
Alhaji sabo ne azaune gefen ummansa yamayi Mata sannu da jiki adole take amsawa kodan tseratar da sadiya daga kagen cutar datayi Mata.
Yace amma kannaki yadenako ?
Yadena dama Rashin baccine Kuma yanzu sai godiya tinda nafarka sai naji kamar cirar Kaya .
To allah ya Kara sauki,
Amin Allah yayi maka albarka ya tsareka daga dukkan abin ki nasarari Dana boye.
Yanajin dadin adduar nan ya tabbata addu,ar mahaifiyarsa ce take bibiyarsa dukkanin wani abu dayasa agaba Yana ganin haske duk sanda zaizo ya gaisheta sai tayi Masa wannan addi,ar sanda sukaje aikin hajji yanajinta dukkanin wata addu,arta akansu ne baiji tanayiwa kanta addu,aba saisu sai mahaifinsu har sai da yazubar da hawaye saboda irin feeling din dayaringa ji atare dashi kauna ce zir ta mahaifiyarsa.
Sadiya ce tashigo cikin mutunci da mutuntawa ta tsuguna ta gaisheta tare da yimata yajiki abincine a hannunta nakarin kumallo har kwai ta soyo Mata sukasaka ta a gaba Saida ta ci duk wani motsin umman takanyi Mata sannu kotace wani abun ne umma ko kanne haryanzu haka taringayi Mata sanabe iri iri har yatashi yatafi yabarta agurin Yana futa tafara yatsina fuska takuma janyo abinci tace dama nawane nabaki Danni nadena girki da kowa inma za,a koma kitchen a koma Danni ba baiwa bace ko kisashi ya nemo Mana me aiki ehe ta murguda bakin rashin kunya .
Sadiya tanan Kuma Kika bullo ?
Tokiyi kigama zanga karshen wasan naki danii zakiyi niba kishiyarki bace ko kishiya inkana neman girma da mutunci Jan girmanka kake bareni da ko kinci galaba akwai ranar kindillaci,
Tana cikin maganarne alhaji sabo yashigo yaji karhjen zancen amma baiji farkon ba tambaya Yake meyake faruwa yaga kamar ranta abace yake,
Bakomai tace tambayarta yakarayi takuma cewa bakomai ganin bazata fadaba sai sadiyar wadda tajike da gumin fargaba tayi murmushi tare da mikewa tama me bawa umman hakuri tace kyii hakuri bansan ranki zai baci ba umma amma Zan kiyaye insha allah shigewa tayi tafita tare dasa hannu afuskarta kamar tana share hawayen.
Binta yayi da kallo sannan ya kalli umman yace wai menene umma Yake faruwa mnhh bakomi kaidai Allah ya kiyaye Allah ya tsare minkai jeka kasuwa Rana tanayi.
Bai tafiba sai yabi bayan sadiyar domin yanason yaji kome ke faruwa sun daure Masa Kai daga umman har ita sadiyar.
Bara muleka wani gidan miga wata wainar suke toyawa.
Zainab taci kuka takoshi tarasa yadda zatayi da surukar tata ita kyautatawa tanayi Mata amma duk bata futa yanzunma cin mutuncinta tagamayi sabili da tasa sabon dinkin da tadade tana tara kudi domin yinsa.
Hartake ikirarin saita rabata da dannata in ma sawa tayi malamai suka asirce matashi to ita zatayi maga ninta har Ni zaku munafunta jiya nagama cemasa yasiyo min takalmi yace zai siyomin memakon yabani kudin kafin yafuta shine yayi fucewarsa kekuma shine kikazo kina giftani da wannan dankareriyar atamfar wadda Koda bansan kudin kayaba ta tasawrwa dubu goma to kuwa ko ya dinkan irinta ko Kuma yabani takin a budamin ko inbawa amina tasaka.
*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO* *NACIGABA*
*DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU*
*ABINDA KE FARUWA*
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
*FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU*
Chapter 7 · 0% Book details