← Book details Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 25

Sashe 22

Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

*ABINDA KE FARUWA*
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
*FAUZIYYA* *AUWALU ALIN BABA JINGAU*
*
29* *(C FOR CHANGE* )
*KAINUWA WRITERS
ASSOCIATION*
sadiya ce tafuto da masifa tace karki kuskura ki tabamin da!
Yar shishshigi kome yahada biri da gada dahar kikasami damar shigomin daki koko damar da jiya yabaki ita tasa raini Yake neman Shiga tsakani,
Tokiji daga kar ki kuskura kikara shigowa falonnan balle kazamin hannunki yayi kasadar tabamin da.
Hannu tasa tadaukeshi tana jijjigashi,
Itako wani tsinannen kallo tabita dashi tare da mikewa tsaye kugu tarike tace kindade bakimin warning ba Ni agidannan har akwai gun daza,ayimin shamaki dashi inkin manta natina Miki inkuma baki sani ba nagaya miki yarkaroro inwata takamace dake toki sauketa Dan wannan gidan dakike gani banakibane bakuma na Yaya sabo bane ,gida gidan ummane gidan ummako Babu me iko dashi saimu koshi dakike gani bashida iko dashi inma zakisa yagina Miki wani to gara Dan muna dab da turaki gaba Yar iya Kinga Kuma ba lallai yayi Miki kyauba Dan karshe akare a haya Dan Haka inzaki saita halshenki kinutsu kanta kwale miki inkuma kinki to nidai dai nake dake,
Shiko gorin da kindade bakiyiba dan Yaya sabo bawanda zaimin shamaki dashi dannafiki iko dashi nibangare biyu gareni keko sai dai kiyi iko dashi na uwa kadai Niko Dan wanna Dan mijina Dan kishiyata Kinga tudu uku kenan ,Kuma kifara lissafi daga yau kiga meyarage akwanakin danima Zan kawo wani to wata Diya Nan gidan domin nidin outo ce inkika tsaya Wasa sai incika gidan da Yaya nabarki,
Hanyar futa tayi zata bar falon ,
Shiko yanagun atsugune tinda yazube sanda zai Bata hakuri jiran umarninta yake soyake tace ta hakura danshi wannan zantukan bagane abinda suke cewa yakeba hankalinsa bayatare dashi makomarsa yake tinawa Dan yasan makomarsa gun sadiya bami kyau bace yasan anbata Mata yarasa wannan kiyayya ta umma da matarsa shikawai tabakin sadiyar gara umman tatashi daga gidan koshima yasami sa,ida Dan zamannasu tare ba abinda ya amfana Masa shikansa basan kallonta yakeba toma nameye zai mayance Zama da ita shifa cutuwa ma Yake gwarama tatashi tabar musu gidan....tsawar da sadiya tabuga ita tadawo dashi daga tinanin dayake ,
Yau Naga masifa kamar bame jegoba ajiye Dan jinjirin dake hannunta tayi tayo Kan ameera tacakumeta da kokawa ,
Ni,sa,arkice dazaki sani gaba kina min maganar da Kika ga dama yauzanci ubanki Yar iska gadon tsiya da talauci,
Ashe dai ameeara da karfinta saiga mejego ana neman murkusheta hannu tasa ta naushi sadiya abaki Aiko taji naushi batasan sanda ta girgije sadiyarba sai gata akasa ,tace aibanice gadon talauci ba kece inbanda igiyar talauci mezaisa siriki yakamawa iyayan matarsa gidan haya ko kinsan bamu saniba toki kwana dasaninki alkadarinki yakusa shegiya matsafiya kokinzata bamusan asiri kikayiwa Yaya saboba Kika rabashi da umma to ta Allah batakiba,
Tana masifa tana Kuma dukanta shikuma kamar ankafeshi agun sai binsu Yake da kallo
wani Mari sadiya tasamu takaiwa ameera Aiko itama ta falla Mata Wanda yafi nata hakan yayi daidai dashigowar rahane Niki Niki da kayan cefanen miyar suna bayanta Kuma mardiyya ce dayaranta Wanda sukataho domin cin sunan jinjirin Yaya sabo masifarsu tasa tayonan domin ummace tace tashiga taga mekefaruwa,
Rahane ce tayi watsi da kayan miyar Tayo kansu riko ameeran tayi zata shigarwa Yar,uwarta hakan Kuma yaba sadiya damar Kara dukanta itama kafa tasa tadaki bakinta saiga hakorin gaba ya wado,
Kukan kura tayi zata maka Mata wani kofin silba dake gefe a ajiye Aiko tsautsayi sai a,goshin alhaji sabo kamar bada umarni ya Mike aguje yayi kanta yace meya sameki kekuma ameera lafiya ke cikata mardiya meyafaru suke fada,
Takaici ne ya hanata kallonsa Saida ta juya baya tace ai dake ba mune agunba sanda abin yafaru,
Takama hannun ameera zasu fita sadiya ta kulle kofa itada rahane wadda taci damara za,a dambata da ita tace yau wallahi koni ko ke agidannan ke har wadda tadaure Miki gindin yimin iskancin,
ta nuna shi da danyatsa cikin tsawa tace SABO kazaba Dani dasu wacece zata bar gidannan nikosu kazaba yanzunnan kokuma Rai yasake baci,
Tabashi tsoro ta Kara yimasa kwarjini harshensa Yake ta juyawa yakasa cewa komai ,
Tace kayi magana mana babban munafiki ai agabanka akayi komai sabida angama dakai ka kasa daukarmin fansa ace daga haihuwata danginka naneman halakani,
Yace kiyi hakuri Zan sake musu gida kwanannan yanzu insun tafi basuda inda zasu ko....takatseshi take to aini sai inbar gidan tanufi hanyar waje amuliyan yabita yanajanta amma sadiya ta juye tace yau bazata Kara kwana dasuba ,
Itako mardiyya komai kallonsa take days bayan daya tamarasa mezatace daga karshe yayanta taka gefe daya itama tasami gu tazauna domin kallon karshen tijarar sadiya tare da ganin karshen hukuncin da yayannata zai Yanke,
Dayaga bazata dawobane yace kiyi hakuri zasu bar gidan yau dinnan inkika tafi Kika barni Zan mutuwa
iya mutuwakece rayuwa ,sai yajuyo yakalli ameera Dan yama manta dawata mardiyya yace ameerakije ku had a kayanki dake da umma kutafi zannemeku in sadiya ta huce kinji kibawa umma hakuri zansamo muku gida kinji kuyi hakuri,
Kallone tare da rasa abincewa take binsa dashi itako mardiyya dama gundatake jira azo kenan mikewa tayi tare da tafa hannu tace tha game is over aikinki yayi kyau sadiya kije ki Kara biyan bokanki aikinsa nakyau Tamika hannu takamo ameerawadda ta mutu atsaye baki bude,
Tace muje ameera ai angama wasan sai dai Kuma yanzu za,a saka sabon da kowa sai yayi hakuri Musamman wanda yace ayishi,
Itako tana tsaye kikam domin abin yawuce mamaki,
Kuyi manage,
*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO* *NACIGABA*
*DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU*
*ABINDA KE FARUWA*
*BY*
*FAUZIYYA* *AUWALU* *ALIN* *BABA* *JINGAU*
*
30(D* *FOR* *DRONEPIPE)*
*KAINUWA WRITERS*
*ASSOCIATION*
Janta takuyi amma ko motsi takasa, sai da ta jijjigata tukunna sannan tasaki ajiyar zuciya,
Tace banni mardiyya zanga karshen asiri agidannan wallahi ko sakina tasa yayi bazan bar gidannan ba balle har ace umma ma ta bini zanga karyarki sadiya zakiyi nadama Mara amfani tsakanin mudake za,aga Wanda zaibar gidannan walau ki hakura kizauna damu yarage naki,
kice sai munbar gidan wallahi narantse sai dai mukone gidan nidake za,aga me,asara acikinmu Mara hankali tijararriya,
Toke wayace Miki zaku bar gida tsakanin ita da yayan wanene Mai ikon tashin umma agidannan yadda basuda iko to kuwa badamar barin cikin gidannan Kennan ,
Juyi tasakeyi tana Kuma tafa hannunta tace sadiya kinshigo gonar dabatakiba naso ace bada makami zamuyi wannan fadanba dakin gane shayi ruwane Amma
duk da haka kirike naki makamin muma zamu rike namu domin namu yafi naki ,
naki zancan banzane muda muke da Muhammadurrasulullah a hannu to kigayan wanene keda riba,
Zagayeta takumayi tace sadiya,as from today zakifara Wasa da dangin mijinki anacewa dangin Miji ko toda kinbimu a inda kika samemu toko dakin more yanzun kuwa zakiyi Wasa da abinda zaifi karfinki narantse Babu abinda zai hanani Kai kararki gurin ubangiji wallahi sai kin dandani zafin dayafi Wanda mahaifiyarmu tadandana akanki ,cikin tsawa tayi kanta harsaida ta firgita,
Jaririn dake hannunta tafuzga da sauri tasakar matashi domin tafurgita dayanayinta,
Sama tadagashi ta nunawa Allah shi,
Cikin karaji nawanda akazalinta take neman dauki gurin Allah tace Allah nakawo karar azzalimar baiwarka,
taraba abinda kasaka soyayya mafi inganci atsakani yadda taraba mahaifiyata da danta itama Allah karabata danata Dan Allah ka saka Mata bukatuwa da soyayyar danta ka Kuma haneshi daya kyautata Mata fiye da abinda tayi tsakanin sabo da ummansa,
Direshi tayi akasa taja hannun ameera afusace suka bar dakin turus sukayi ganin umma adurkushe a bakin kofarta tana kuka wiwi kamar zata hadiyi zuciya,
Rungumeta sukayi suna rarrashinta ameera tace kiyi hakuri umma kaddarar muce a Haka kidena kuka zata ga karshenta,
Mardiyya ce tace kikara hakuri umma komai zai wuce muje mutattauna matsaya zubawa Yaya Ido yayi tazama a haka ba inda zai kaimu sai gadar bacin rai muna neman shawara bazamu iya mukadai ba,
share hawayen fuskarta tayi tace Ni nasare da wannan Al,amarin yaushe nayi saken da har mace zata rabani da dana yaushe duniyar tazama haka dole Mata mutashi tsaye bakuma wai tashi tsaye na gallazawa sirikaba ,
Yakamata tin daga Randa akace kin haihu tokuwa wani hutu da jindadi yakare Miki meye agaba mikawa Allah lamuran kar muzama cikin mutanannan masu cewa sun haifawa mace da kar Kuma muzama cikin masu kalamai nabatanci gadan wani domin duk kalmar dazaki fada ga Dan wani to kuwa tamkar danki Kika gayawa inkika nemowa Dan wani Bala,I kitabbatar sai yadawo Kan danki duk dadewar daza,ayi kuwa sannan kitsabtace halshenki duk tsananin bacinrai karki bi danki kodan wani da kalmar da bazatayi dadiba gareki ko gawata,
Inkinyi sallah kitabbatar kinyiwa yaronki addu,a ki nema Masa Allah yabashi mace tagari kice Allah ya dorashi akanta kema Allah yadoraki akanta ,in macece Nemo Mata miji nagari kice Allah yadorata akansa kema Allah ya doraki akansa karki Raina wannan addu,r dazakiyi Masa muna cikin yanayi yayanmu suna bidar addu,a Kuma karki Raina shekarun danki duk kankantarsa bishi da wannan tare da tsarewar rayuwa ,
Bayan wannan abu nagaba dazamu sa acikin zuciyarmu Yaya muke rayuwa danamu mazajen kitabbatar duk abinda kikayiwa naki mijin tofa kema za,ayiwa danki ,inkin rabashi da Yan uwansa to kema akwai lokaci yananan zuwa to Wannan ma rayuwar bakayiba anmaka ballanta kayi,
Inkina takama mijinki ne ba kekadai kike da iko dashiba akwai mabukatan dasuka fiki bukata Dan yanzu *ABINDA KE FARUWA*
Dazarar mace ta Sami mjij Nan duniya bashida damar kyautatawa danginsa nufinta sai it's kadai to kuwa Yar ,uwa rikeshi kirabashi da danginsa tokuwa kinanan wata rana Zaki kwashi kashinki a hannu kafin kije walakiri ya fara yimiki maraba da sandunansa ,karshe kije azabar da Allah yatanada tanacan tana zumudin ki Isa gunta tarungumeki runguma nafi Muni domin hukuncin Wanda yaraba soyayya mezafine balle ace ta dangi haba Yan,uwa inazamu da hakki me muke nema komai muka samu anan zamu barshi alherinmu shine guzurinmu ,
Tace na rokeku karkuzama daya daga cikin matayennan ,
abin akwai ciwo karkuso Allah yajarabceku da kwatankwacin wannan Bala,in,
Dukkaninsu kukan suke me gadine yayi sallama yace kuyi hakuri hajiya komai yayi zafi maganinsa Allah insha Allah komai yazo karshe zantaimaka muku amma yanzu kuje kusami nutsuwa zandawo sai mutattauna,
Itako tana ciki duk abin duniya ya isheta lallai sai tasa malaminta yayi Mata aiki akansu dan sun shige Mata hanci da kudundune Musamman ameera ko Kuma ta hadasu gaba daya taci ubansu inba hakaba bazasu barta tawataya ba,
Matsowa gurinta yayi yace kiyi hakuri duk zanyi maganinsu har mardiyyan ....dalla mezaka iya kansu bayan kana ganin komai Yana faruwa agabanka Ni wallahi bakada amfani dakai da Babu duk daya ka kasa komai amma akuka da ranar da Zan hantsilo da Bala,oina zata shafi kowa har Kai din dakake daure musu gindin suyimin Rashin kunyar da sukeyimin fuuuuuu tashige daki tabarshi tsaye da rahane agun yace dauki Dan kimika matashi,
Sanda rahane takai matashi kin karbarsa tayi data matsa Mata takarbeshi hadawa tayi da rahanen da jaririn tazage tasss har tana cewa wannan Dan iskan jinjirin dashi da ubansa Basu da amfani agareni tinda yazo duniya Raina Yake baci inba Kuma sokikeyi zuciyata tabuga ba kifuta dashi nadena ganinsa zuciyatace take neman bugawa kurabu Dani ,
Wardrobe tayi tadakko hijabinta tasaka tace kirikeshi yanzu zandawo bakuma zanshigo gidannan ba sai nayi maganin wadancan Yan iskan,
Rukota tayi tace Ina zaki ?
Kibarni innadawo zangaya Miki,
Tace dazakibi shawarata da kin hakura kisami nutsuwa bayan anyi suna anwatse sai kiyi duk abinda kikeso Amma yanzu duk kinfuta daga hayyacinki kamar bakeba,
Suna cikin hakane aka kwada sallama daga falo da gudunta tafito tana nagodewa Allah lallai Allah yanasona daya kawominke aminiya ,
Itako aminiya wani irin kallo take Mata tace ya Haka mejego ?
wannan wanna irin jegone duk kinyi wani iri?
Tace kedai zauna kiji ayau basai gobeba nakeson ayimin kowana irin aikine
sonake kije gurin malam yaraba mardiyya da gidannan na har abada tare da umma da wannan tsinanniyar ameeran sonake yayi musu korar kare.
*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO* *NACIGABA*
*DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU*
Chapter 22 · 0% Book details