← Book details Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 25

Sashe 24

Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*KAINUWA WRITERS* *ASSOCIATION* aminiya ce zaune gaban malam tana Kara Masa haske shikuma Yana dorata tana hawa ,har Yake cewa ai ita wannan mardiyyar inba,atashi tsaye akanta ba to kuwa zata Zama matsala Dan dama bason sadiyar takeba , yakara da cewa badan itama sadiyar atsaye take ba da tini tasa yayan ta yasaketa Dan duk wani gun boka da malam tasani Dan Haka yanzu aikinnamu kasashi zamuyi dole akara Shiga tsakaninsa da uwar tasa domin aikin da mukai yadanyi sanyi inkuma akasake tofa kwabar zatayi ruwa Dan Yana dawowa hayyacinsa komai zai iya faruwa, Game da kishiyarta kuwa ai sai tayi nadamar shigowa gidan zamuyi Mata aikin da sai ta gudu da kafarta sannan duk wani abu daya fara yawo akansa agame da ita zai manta in kuwa yasake lekawa gareta to kuwa kice aikin danayi karyane Nina tabbatar Inna rabasu sun rabu har abada, Nan dai tacake Masa Rabin kudin data wawuro ta watsa sauran a aljihunta kulla kulle ne guda uku yace daya a binneshi a kofar gidan daga ranar da akasaka mardiyya tabar Kara zuwa gidan daya Kuma abar bada abakin kofar dakin ameera dayan Kuma umma za,a watsawa adakinta inhar tasheka tabar gidan kenan har abada sai dai anemota ko Bata bataba to kuwa gidan tabarshi kenan, Tace to malam itama ameeran tabisu kawai , Yace bar wannan kwallon shegen kwanyarta karfi gareta wannan ma dazaku zuba kuyi addu,ar yasameta inkuma Bai sameta ba kudawo dashiri mezaki akwai Wanda Zan hada inkuwa akayi amfani dashi to kuwa shida Kara kusan tarta sai anbashi umarni Kinga kuwa abin dakamar wuya, Jikina asalube na wuni Dan komai Dakar nakeyi bansan inada saka Abu araiba sai da wadannan abubuwan suka faru ballantana da malama ramla ta Kuma kashen jiki da labarinta tare da cin fuskar daya biyo bayan sadaukarwarta ga megidanta, Hajiya ce tazaunar dani take tambaya ta shin ko wani abun nadamunkine? Murmushin karfin Hali nayi nace laaa Babu komai hajiya kawai dai Yar gajiya ce Kuma nasaba da haka ballantana in Rana tatake dinnan sai kiga abin sai a hankali , Kallona tayi ta gyada kanta tace nidai abinda zance akara hakuri juriya da kauda kai shidai namiji sunansa kenan ayyukan sa yawa garesu inyaso kayi dariya sai kaji Nan duniya bayakai inkuma yaso yasaka akasin haka sai kaji kamar kagudu kabar ladanka,hakan bashi zai Sagar maka da gwiwa ba, azama zakasa domin koyaushe kazama cikin farin ciki shi baiki kadawwama abacin raiba Dan haka nidai nasihata gareki yata akara hakuri duniyarma nawa take ita Kuma aljanna nemanta basauki gareshiba ,sai Kuma takautar da zancan kamar ba ita tayi ba tace kingama abincine naga yara suna hanyar dawowa daga makaranta amma kamar baki doraba, Sunkuyar dakaina nayi Dan sai nauyinta Yakuma Hawa kaina danniyata da ita da jikokinnata suzauna da yunwa har sai yadawo yanemi abinda zai Basu suci, Nace yanzu Zan Dora kotaliyace ,namike Ina cewa iceko hajiya kinacin taliya kar indafa Kuma bakyaci? Yo badoleba ai Dole inci a lokacinnan har wani zabine dakai Akan abinci, dama Allah yadubemu badan halinmu ba Yake ciyar damu Aida danmune da halinmu Aida tini ko buzunmu baza,aganiba kedai Allah yasa mudace, Duk munci mun koshi sai megidan ne can gefe Yana juya abincin Dana zuba Masa dayagaji da juyawane Yake cewa wai menake gani kamar taliya da manja kinsan bacima tabace yaza,ayi kidafamin taliya in ma itan kikeso kidafa sai kiyi me Miya ko jallof amma Ni wannan mezanci da ita Kai saddiku zonan kadauke bazan iyaciba karkuma akara dafamin taliya in cizakuyi saini adafan abinda zanci, Hajiya ce tamangantu tace karshenta taliyar kabayar shiyasa katarar da ita dabaku iya godiyaba ga Wanda ya kyautata muku ba yarinyarnan tinda tadawo take kaiwa tana dawowa amma shine kabita da sakamako, Yoni ko ajikina Daman inasane nayi hakan Yana cewa bayaci najanyeta nakara barbada Mata yaji nabi takanta Kuma ko kallo Bai isheniba naci gaba da sabgata , saddiku ne Yake cewa umma wallahi nidai gobe bazani makarantaba yauma anti ross harta koromu uncle yabata hakuri gashi ankusa fara exam ko kudin term bamu biyaba gakuma kudin exam shima, Juyowa nayi Zan Masa magana yo aitini ma yabar gun yashige daki cikin takaici nace kace zankawo insha allah sukara hakuri , Yace umma kidena zuwa makarantar mu muma abbanmu yadinga zuwa Kinga kowa babansa ne Yake kai kudin makaranta mukuma abbanmu baya zuwa , Nace to zaije yakai kubar zancan haka badan mungama Shan iskarba namike nasa nana tayi musu shimfida nace kowa yayi Shirin kwanciya Haka nashiga dakin hajiya nagyara Mata inda zata kwanta nasa Mata net nace Zaki kwantane hajiya kosai anjima Naga da sauro? Tace Ina Zan zauna duk Kun gudu Kun barni Nima gara intashi dama tin dazu nake gyangyadi,nayi Mata sai dasafe Nima nashige daki , Bayan nagama Yan abubuwan dazanyine nayo alwala domin inyi sallar isha , Addu,a nake tare da sadaukar da Kai gurin Allah Ina neman daukinsa Ina neman mataimaki domin dukkanin wani hope danake dashi Yana neman rushewa, Yana gefe Yana sauraran radio nikuma Ina lazimi tare da wasiwasin insakemasa magana koza,a dace Aiko zuciya ta debeni nadan matsa gareshi nace in ba damuwa inason yin magana da kai, Rage radion yayi yace inasauraranki , Dama Kan maganar kudin term din yarannanne kaga yakamata abiya musu domin inbanda alfarma kasan lokacin biyan yayi da,azo ana korosu aigwara koyane Adan rage yafi shirun narashin biyan, Shiru yayi tare da dauke kansa gefe, Nace Ina magana kayi shiru, Wani dogon tsaki yaja yace za,a biya, Nikuma duk haushi ya isheni amma haka naba zuciyata hakuri nacigaba da magana, Nace to yanzu dan Allah inba,a biya yanzuba yaushe za,a biya kaga sati biyu yarage ayi hutu gashi ko kudin jarrabawama ba,a biyaba, Afusace yajuyo yace to inbance Miki Zan bayarba mekikeso ince ,babun zankira kokuwa shekaruna Zan kirga nabaki , Aiko nafusata Nima nace inbaka bani shekarunkaba ai kabani wadanda kake tarawa haba nagaji nagaji yaka keso nayi da raina ko sokake zuciyata tabuga kana tabuka wani abunmana amma kasakar min yara komai Ni komai ni bawani taimako to kuwa wallahi dasake inba hakaba Nina gaji Zan dau matakin danaga zaifishsheni, Au gori zakiyimin kidau abinda yafi mataki ma iya kokarina inayi amma burinki ki kureni menene banayi naga Nima Ina iya kokarina inkinyima wa kikayiwa yayanki Ina ruwana ballema mekike yimusu dazaki sani gaba kina neman kureni haba karimatu kirabu Dani Haka kinfara takuramin dazancanki haba,badamar kiga Ina hutawa sai kin batan nishadina nariga naganeki duk sanda Kika ganni zaune Ina nishadi sai kin batan Rai tome kikeso nayi kuka kikeso nazuna inayi kome, Nice zakace menakeyi nice nake Bata maka farin cikinka kayimin adalci kenan nidin nidin shu,aibu ko kowa zai Fadi haka nazata Kai bazakace hakaba hawaye masu zafi tukullumin bacin rai sai motsi nake narasa yadda zanyi ,na ce tsakanin makarantar islamiyya Kota boko ko sittira dasauran abin bukatu duk bazaka iya Tina alherina garekaba, Ai kaji aikaji tsiyar badai Akan school fees kike wannan ba todama yadda mukayi dake Zan bada namutum daya alokacin to yanzunma Zan bayar ajirani, Aiko nakuma fusata nace tsakanin sanda kace zaka ringa bada na mutum daya zuwa yanzu kataba bayarwar ko ka taba bayarwar Naga tin suna su uku kafadi haka jataba bani kosau daya yanzun su nawane nace sunawane banaso karike abinka Allah zai dubemu zai Kara rufa Mana asiri, Wai ke duk wannan abun da kikeyi na menene kike Abu kamar Mai iska nidin meye banayi musu naga ko Abu Zan basu cewa kike nabaki Zaki Basu kodama da manufa kikeyi Dan kigayamin maganar banza, Me kake bani inbasu naira biyar din ko goma ko Kuma taken dakake siyo musu, Naja majina domin kuka nakeyi bakadanba yau shu,aibu yagirgizani kalamansa sunyimin zafi sosai,nace wai nice karshena yazo a haka yau shekarata goma Sha biyar Ina aikin gantali a hanya duk Dan narufa Mana asiri Ashe aikin banza nake,Ashe kaidin bakasan inayiba nace shu,aibu yau Ina neman danake yakene nazata dabana Mora maka komai Dana Tara gidaje da filaye a wannan sana,ar tawa Amma dame natsira da tijararka wayyo ni lallai *ABINDA KEFARUWA* yau yazo gareni, Jinayi yajanyoni jikinsa ,Aiko kamar yajonamin shokin Haka naji Dan yanzun bana bukatarsa kusada ni kukana shine saukin abinda zanji, Yace to Wannan kukan Kuma nameye goge hawayen ai na ce zanbaki niba Haka nake nufiba kece Kika dauki zancen dazafi, Nadago kaina nace Babu komai shu,aibu Haka rayuwar take na tabbata bazaka taba Zama bango abin jinginataba , nagada hannu sama Ina hawayen me sheshsheka nace Allah kazamo gatana Allah kabani juriya yadda nakekan bautawa iyalina Allah kasa Suma su kyautatamin Allah karkabasu ikon sabamin bazan jureba Allah, Allah kasani kabani yaya yena atafin hannuna tare da yimin biyayya Allah kafinni sanin abinda nakeso , Aiko nakuma dafe goshina domin yau nayi kukan Daban tabayiba zuciya nakeji kamar zata Faso kirjina tafuto dama inada alwala zuwa nayi nawanke fuskata nakoma Kan sallaya ,gashidai sallah nakeyi amma kukanake mesauti bawai kukan zuciba, Kuyi hakuri zuciyata tayi rauni wallahi nikaina kukanna dagaske naci gaba labarin Nina ya girgizani *INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO* *NACIGABA* *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU* *ABINDA KE FARUWA* *LABARI DA RUBUTAWA* *BY* *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* * 32(F FOR* *FANS* ) *KAINUWA WRITERS* *ASSOCIATION dukkanin tinanina yakare domin ba abinda yanzu nake tunawa sai kalamansa , Shikuma sai faman kame kame yake wai nayi hakuri Shiba abinda Yake nufiba kenan rainane yabaci shiyasa nagaya Miki wannan maganganun amma ainasan kinayi Ni ai ba Wawa bane dazance bakya taimakamin , ba saina fito nafada agaban kiba ai Ina yabonki ko agurin abokanaina ba inajin yadda nasu matan suke musuba nasan kedin tadabance bako wacce mace bace zatayimin abinda kikeba, Kuma zakiji dadi insha Allah kicigaba dayimin addu,a zanbaki mamaki munkusa mu huta insha Allah yadda nasaki kukannan sai nasaki dariya kinji karimata sarkin karamci kidena kukan haka, Uhm nace ai kagama bani mamaki narokeka idan dawani agaba kakyaleni haka nayau yawakilci koma wanne mamaki zaka bani , Baki ganeba Ina nufin sai kinsha mamakin alherin dazai biyo bayan kyautatawarki gareni, Baya najuya Masa nacigaba da istigfari da hailala amma har wannan lokacin bandaina zubar da hawayeba, Dake bansamu nayi bacci da wuriba sai da namakara Haka natashi fuskata duk
Chapter 24 · 0% Book details