Sashe 3
Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
murmushi tayi tace aini nasan addu,ata na tare dakai balle da Allah yacika min burina kasami macen arziki hakan yayi daidai Allah ya gina maka. Dazancen ba,adau wata guda ba aka kammala gini na daidai talaka dan kuwa bako Ina aka gamaba mundai koma Kuma cikin farin ciki lokacin cikina wata tara dana tashi nasantalo dana namiji Kuma akawayi gari ko kudin zuwa asibiti bashida shi gini yacinye dukka kudin Kuma shidin bame planning bane danma Ina kokarin saitashi memakon yayi kokarin rage wani abun kodan hidima dole nice nayi komai hatta kayan haihuwa dake nasan halinda muke ciki dama nagama siya dinki ko dama nasan ba lallai nasamiba tinda nidai rabonada saka sittirar da yayimin tin lefe haka mukasha shagali dake Kuma akwai halin dan adam dake tare dashi sai da yayimin abinda raina yayi mutukar baci yasami gudun mawar haihuwa memakon yayimin kokari wani abun wallahi sai yashamuke . ku intakaita mukuma hatta ragon da,akayanka aguna yaranci dubu ashirin yasiyo amma dayasami nasa sai yayimin shiru nayi kokarin karba yayi min fuskar shanu. *INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA* *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN* *JINGAU* *ABINDA KE FARUWA* *LABARI DA RUBUTAWA* *BY* *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* * 6(F*) *KAINUWA WRITERS* *ASSOCIATION* Wanda asanda zai karbi kudin karkuga yadda yaringa lallabani dukkanin wata kulawarsa ya tattarata kaina . Gashi dai inada akidar kin bashi kudina domin yayimana sabgar cikin gida , amma haka ganin kar ya tozarta nadauka nabashi . Haka nacigaba da jegona Kuma alokacin sai Allah ya jarabceshi da babu haka nasa duk wasu kudi dake hannuna agaba nacinye gashi nikuma Yan kayan abincin danake siya sun yanke ban tambayeshi meyake faruwaba shima Kuma baice min komaiba inzaifuta yakancemin kiyi hakuri innadawo Zan baki ko Kuma Zan dawo da yamma sai intaho da ko shinkafa ce wannan lokacin nasha wuni ba abinci sai dai yandabaru dake jego nake bana rabo da kunun gyada wuni nakeyi shansa dake na koyawa nana ma shansa itama intaji yunwa shinakan bata. Dake bame muguntar ciyarwar bane wani lokacinma biyar agida take masa ya auno mana Yar gwangwani hudu Kuma da ka kalleshi kasan yaci wuyar tafiya nakance abban nana amma dai akafa kataho ko ? Sai dai yayi murmushi yace to yaza,ai abinne sai addu,a kasuwar tazama abinda tazama. Danayi wani tinani sai naga shidin inbanda wahala ba abinda yakeci mutumin dazaije kasuwa akafa yadawo akafa kuma ya wuni Yana maka bauta ace baisamu abinda zai hau motaba ko abinda iyalinsa zasuci su wadataba aiko wahalace ciki zalla. Wataran nakece masa mezai hana asami wadansu Yan kudi kaima ka Kama shagonka . Kallonna yayi tare da daukar saddiku dake cinyata yace karimatu bakisan abinda kasuwar Tamu take cikiba yanzun ana ganin kayi wani motsi na cigaba sai a kwantarka dan abinda kake futa kana samowa iyalinka ma sai ya gagareka . Nace to ai in akace ahaka zamu cigaba da rayuwa ko akwai kalubale megirma tin yanzun komai Yana gazawa balle ace munkara tara yara kaga Allah ya bamu dama tin farko Kuma kayi watsi da ita yakamata yanzu mugina iyalinmu kodangaba kana gani fa dukkanin Yan uwanka sundareka amma ka fahimceni karkayi min mummunan zato. Ina nufin dukkanin su bawanda bazai iya ajiye abincin shekara agidansa ba amma Kai sun kwakumeka karkashinsu ya kamata ace kaima yanzu kaci gashin kanka shekararku nawa tare bakada cigaba kullum dan uwanka kakewa nema inda yare suka fimu kenan dasune da tini sun yayeka kaima ka yaye wani amma kullum in ya hango cigabanka sai ya dukunkuneka ya Kuma danneka karkashinsa kayi tinani iyalinsa kake ginawa ba nakaba Kuma inda duniyarnan tazama daga kwauri sai gwiwa ko bayanan ranka inhar baka raine mu da tattalin rayuwarmu ba Babu mebi takanmu. Amma kayi tinani . Ajiyar gwauron numfashi yayi yace za,a duba Amma kinsan banida kudin da zanja jarin . Nace indai kudine bazasu gagaraba kabari inkoma aiki zansami dashi inshiga saina baka amma fa kasanni banida dadi nima kudi nawane bakuma kyauta nabakaba kafin kakarba zamuyi yarjejeniya kullum inkadawo daga kasuwa akwai abinda zaka cirarmin na ajiye har Allah yasa kabiya ni in Kuma kayimin halin maza zakaga true color dina domin guminane nabaka aro domin cigabanmu Kuma zance ne nidakai karkayiwa kowa zancen har hajiya mu bashshi atsakaninmu . Gadiya yayimin tare da amincewa da batuna . Nace kwana biyu bamuje nagaida hajiyaba Allah yasa kaje kaima danna fuskanci kamar kwana biyu baka zuwa ? *ABINDA KE FARUWA* *LABARI DA RUBUTAWA* *BY* *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU