Sashe 20
Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*26(Z)* *KAINUWA WRITERS* *ASSOCIATION* wata razananniyar Kara tasaka tare da dafe gurin datasha Marin, Umma ce ta nunata da Dan yatsa tace wannan zubar min da miyan da kikayi kin ruguza dikkanin ayyukan da Kika dade kinayi kinyi kinyikure sadiya ,wani Dan guntun ruwane yadigo daga cikin idonta tace akwai ranar kin dillanci ranar da baki da mataimaki, Kasacewa komai tayi domin Marin yashigeta ga banbamin fadan da umman takeyi kamar zata daketa, Juyawa tayi zatashiga dakinta cinkaro tayi da Mai gadi da yatada Kai da hannunsa ,domin yagigita yasan gidan yadan hargitse Bai tinanin abin yakai hakaba, Rabeshi tayi tashige batare da tasake kallonsa ba, shima juyawa yayi domin bashida abin cewa masu abin fadinma ba,a basu daraja ba balle shi megadi amma yakamata dai to........ Jin ba kowa agunne yayi kokarin fitowa amma dake ameera tana kanhanyar sai tamayar da kofar batare da yafitoba ta rufe da alama ta shirya taryan dukkanin wani shiri na sadiyar, Bata koma bacciba sai tashiga ta hada ruwan dumi ta gyara jikinta tare da yin wanka sannan tadaura alwala, Sanda tafito Yana tsaye inda tabarshi tausayin sane yajata izuwa gareshi tace kaje kayi wanka ga ruwancan nahada maka, Baice komaiba sai bin hanyar bandakin da yayi ,ita kuma ta shinfida dadduma guda biyu tahau guda daya ta fara sallah Dan ko ta kwanta dinma ba abinda zata iya, Futowa yayi daga bandakin Bai tsaya sauraronta ba ya doshi kofar futa ita kuma tana cikin yin tahiya domin sallamewa, Bata tsaya yin addu a ba ta Mike da sauri ta rukoshi tace Yaya sabo Ina zaka adarannan bayan ga dadduma tana jiranka ,nasan koka koma bazaka iya bacci ba gara karaya daran kodan saukin abubuwa. Bai Musa Mataba ya koma domin jiyake inyayi maganar kamar zuciyarsa zata Faso kirginsa tafuto, Tana tsaye harya futo daga yin alwalar ta kara gyara masa sallayar sai da yatayar da sallar sannan itama ta tayar , Tin tana jiran ya idar har sai da tafara gyangyadi ganin bashida niyar gamawane yasa tayi masa magana sannan yadakata, Hannu yadaga zayyi addu,a amma kuma yarasa mezaice data fuskanci haka sai tafara yin addu,ar afili Aiko cikin ikon Allah shima ya karba tin Yana cewa Amin ,amin har sai da shima yafara rokon Allah bukatunsa, Duk abinda akace Allah angama domin damuwar dayake da ita tafara raguwa har sai da yadingaji ma gwara yadan kwanta ya huta anan Dan in ma Yaje gun sadiyar aibayyi daidaiba domin kwana bakwai musulunci yabashi anan dai Kan daddumar bacci ya kwasheshi , Ya Allah, ya Allah, Kalmar datake ta Mai Mai tawa kenan domin komai yadaga mata hankali inhar Haka sadiya take to dole tasake mata zama kodan farfado da soyayyar dake tsakaninsa da mahai fiyarsa gatata rayuwar wadda inhar bata bawa mardiyya hadin kaiba to kuwa har da ita za,a kwan ciki balle inta tuna alherin umma garesu lallai yaci ace tasaka Mata da alheri, Zainab kitaho Yana kiranki , To ganinan akwai abinda nakeyi , Itafa tafara kaiwa makura da basusan mahimman cintaba sai yanzu da lalura tasamesu , Futowa tayi tashiga dakin baban Wanda har yanzu Yana dakin, tana tausaya Masa amma inta Tina yarda suka rabu akwanakin baya sai taji dik sun futa aranta, Sannu tace Masa , Ido yadago ya kalleta sannan yace medorine yace nadinga dan gwada mikewa ga sanduna nan ankawo min, Toni meye nawa aciki sai dai inkara yimaka addu ar samun waraka, Hakane amma inabukatar temako kogurin Mikewa gashi inason kihadamin kayana zankoma daki saikicigaba da kulawa dani sai ita baban ta huta, Ai shikenan amma dakayi zamanka ai Ina temaka mata, Kuyi hakuri da wannan banajin dadi ga diyata ma ba lafiya wannan ma daurewa nayi nayi muku. *INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA* *DAGA* *ALKALAMIN* *YAR* *MUTANAN JINGAU* *ABINDA KE FARUWA* *LABARI DA RUBUTAWA* *BY* *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* * (A )FOR* *ANDROID* *KAINUWA WRITERS* *ASSOCIATION* yace itace tabukaci hakan amma inkina ganin da matsala komawar tawa sai ince mata abarshi kawai, Kallonsa nayi yakuma bani tausayi domin kalarsa takomamin yanayin damuke dashi ada before baba tahargitsa Mana zaman, Nace shikenan tare da fara tarkata Masa kayansa dasuke gun Ina cikin hada kayanne baba tashigo tace inkin gama kikamashi kukoma dakinku ainayi na Allah, tinda kenaga haryanzu hakurin da akebaki baimikiba inzaki yi hakuri kiyi inkuma bazakiyiba kujecan kukarata amma dai akiyaye Zama dani domin dab Dan lele Yake da Karo auran wata, wannan karayar ce tadakar da komai amma datini komaima ya wuce ato inzaki sauya hali kisake barganin ana lallabaki, Dagowa nayi nakalleta harna bude bakina zanyi magana Kuma wata zuciyar tace min inyi shiru, Shiko gogannaku ko kallon gefen danake bayyiba yadda yanuna baiji abinda taceba Haka nima nashare bankuma bi takansa ba , Haka nagama tattara komai nakai daki sannan nadawo nakamashi mukashiga dakin katifata nafuto Masa da ita falo domin shigarsa bed room bazayyiwu ba , Cigaba nayi da kula dashi cikin amincin Allah hakan Kuma baisa baba tarage yimin wani abinba koya taga Ina neman yin wani abun domin tallafa Masa gurin jiyya taringa maganganu kenan kar inkara karya Mata da domin alamu sun nuna bazansan zafin haihuwa ba tinda gashi ana niyyar shekara biyu dayin aure amma har yanzu shuru bawani labari. Cikin ikon Allah bana Jin wani bacin rai kamar nada kodan naciresu daga Yan kayana basa gabana daga ita har dannata ne oho . Wata rana Ina tsakar gida inayin Yan Kaye kaye kauda wannan dauke wannan domin nakwan biyu banyi irin aikinba , Wadansu Yan Mata ne sukayi sallama su biyu dago kaina nayi tare da amsa musu sai Kuma sukayi cirko cirko ganin Haka Nima sai natsaya da abinda nake Ina tambayar su wasuke nema? Ba wacce tabani amsa ganin Shirin yadan ja Basu ce komai ba sai na leka dakin baba inayimata bayanin bakin da mukayi dasaurin ta tafuto tanayi musu maraba tabasu umarnin su Shiga daga ciki, Nidai bansan suwayeba ban Kuma San mesuka tattauna ba sai ganinsu nayi sun futo tare da baba tayi musu jagora zuwa nawa dakin ban kawo komai ba nacigaba da aikina amma wucewar baba da minti biyar Yan matannan Basu futoba Dan inganewa idona komene Yake faruwa natafi dakin , Batare da nayi sallama ba nadaga labulen , Turus nayi Ina binsu da kallo daya bayan daya, Lallai ana neman yimin wani rainin hankali wato Yar farar ce zaune take yimar karairaya buta ce ahannunta tana zuba Masa ruwa yana alwala dake yanzu yafara amfani da ruwa ada saidai nayimar taimama yanzun ko alwala nake mar da ruwa shine wato kannazo nayimsa shine nasami magajiya lallai sin taro kwandon Bala,i. Yau da rigima natashi agidan domin komai ya kureni baga sabgar cikin gida ba bakuma a biyan bukatar aureba bantaba jin irin wannan bacin ranba sama da najiya da daddare dama dai a haka nake nakanyi hakuri ne sabida nadanganta hakan amatsayin wahalace takeyimar yawa shiyasa Yake kasa biyamun bukatata ta aure, nasan ada akwai wahala sosai atare dashi kotafiya da kafar dayake izuwa kasuwa Yakuma dawo da kafa ya Isa haddasa Masa gajiya, sai nakanyi hakuri domin Kona matsanta ba lallai yagamsheni yadda yakamata ba , Dan nakance kadinga neman maganin basir Dana sanyi ba gajiya ce kadai takesa ka kasa biyan bukatarka ta aureba nidin me bukata ce hakuri nake kawai Dan bayarda zanyi, To kuwa yanzu ai nasan wahalar ba irin tada bace akwai sauki acikinta ko gurin walwalar aljihu ai komai ya warware sai godiya , Haka naje nagaida hajiya rannan nawa ba dadi sai karfin hali ahaka nadinga Yan aikace aikace na Dan yau ko saurarassa banyi ba wajan tayani yin wani aikace aikacen cikin gida Koda najuye ruwan wankan yara zanyi musu cewa yayi inje shi yayi musu kar aikin yayimin yawa ,ko kallo Bai isheniba danaga zai dameni kawai sai nakira nana dake cikin kitchen nace tabar abinda take tazo ta karbamin wankan yaran Nina hada musu abin Karin , Ina kokarin dibo kayan shayine natina ban siyoba ,afusace nafuto raina abace shikuma Yana inda nabarshi yakurawa gu daya ido, Nace asiyo Mana kayan shayi , sannan asiyo Mana shinkafa itama bani da ita ahado da kayan Hadi insun futo yanzu inkuma Basu fito ba akwai gidan da ake siyarwa in angama shirya yara sai kabasu su siyo , Bina yayi da kallo yaga inda nakumbure ba alamar sauki tare dani baicemin komaiba yajuya yafuta , Cikin mintoci yadawo, yasiyo har shinkafar karba nayi na dagata Ina auna yawanta, nace wannan shinkafar gwangwani nawace baicemin komaiba direta nayi agun nayi gaba batare da nasake cewa komaiba domin dabi,arsace yin shiru Musamman inzancen danake Masa yadanganci aljihu, Haka na hada wa kowa abin karinsa nadau na hajiya na Kai mata nata, Bayan yagama shiryawa ne ya dakko naira dari uku yabani ko kallansa banyiba nace ai dake Kai zaka karasa kayanka nace wannan shinkafar dai ko ba,a fadaba nasan bazata Gaza Rabin kwano ba to ita nake dafawa da rana kaga kenan sai kanemo ta dare tare kayan hadinsu, Turus yayi Yana kallona , Sannan yace wai karimatu meya Shiga kankine kike neman hargitsa Mana zaman lafiyar da muke ciki tinda safe kike ta fushi bansan abunda nayi Miki ba , Kuma kinzo kin billo da wani zance Wanda baki taba yiminshi ba me kike nufi duk kokarin da nakeyi akanku bakya gani ko so kike innadawo daga kasuwar nadinga juye Miki abinda nasamo ya hakane kina nema kidagamin hankali tinda nasami sauyin gurin sana,a Kika sake hali ko kina bakin cikin sauyin Dana samune? Tinda kike nemanki nataba samiki ido ne kwanda larki baki taba dauka kinbani ba balle kice ita kike kokarin hada kudinsu to Dan Haka kiyi amfani da abinda nake dashi in Kuma kin raina to aikema kina nema sai kicika, cikin bacin Rai da fushi ya,ajiyemin kudin yayi gaba, Bazan iya kwatanta yanayin danashiga ba nidai kawai na jini dabar akasa gawani tukullimin amai da yake taso min , Ahankali idona Yake rufewa nikuma Ina kokarin budeshi amma tsabar bacin rai bancimma gaciba sai wata uwar shakuwa datake shakeni ,nana najiyo sama sama tana tambayata manshafawa, Alama nayi Mata da hannu tabani ruwa insha da sauri ta debo tabani cikin amincewar Allah nafara dawowa dai dai sannu take