← Book details Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 25

Sashe 5

Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*8(H)*
*KAINUWA WRITERS*
*ASSOCIATION*
Hajiya amina ce kwance tinanin duniya ya isheta tin misalin karfe uku tafarka tasaka wannan ta kwance wannan.
Tarasa meke Mata dadi itadin macece mekawaici akalla intace zata dauki mataki Kan sadiya bazayyiwa sadiyar dadiba.
takanyi tinanin inhar tace zata rabata da sabo tokuwa itama tata Yar dake gidan nata mijin baza ayi Mata uzuriba shiyasa take yin hakuri da duk wani cin Kashi datake mata hannu tadaga sama tana yimar addu,a Musamman datake hango irin musibar data kunno Masa Kai dan sadiya alamu sun nuna zamansa da ita bashida alheri Musamman yadda take gani da Jin take takenta.
Tinani tashigayi na irin wuyar dataci da yayanta.
Su biyu ta haifa sabo shine babba sai mardiyya tazarar shekara biyune atsakaninsu sabo Yana dan shekara goma Sha biyu mahaifinsu ya rasu bayan share makokine dangin babansu suka nemu tafiya dasu ,
Alfarma ta nema abarmatasu dake Suma basu zafafaba sai suka amince abubuwa da dama ne sukasa tace abarsu gunta batun yauba tasan ko mahaifin sune ya nemi taimakonsu sukance Suma nema suke Kai ko rashi yatashi dashi yadau kwano a matsayinsu na Yan uwansa yace azubo Masa abinci to tabbaci hakika ko sunbayashi sai gori yabiyo baya.
Sukanje duk juma,a su gaishesu ko lomar abinci bata hadasu ko angama dafawa insunje akan mayar da murfin tukunyar sai sun tafi sannan aci.
inko akaga basannan zasu tafiba akan ringa cin abin
cin cikin hikima yadda dai baza,a zuba musuba ,
Suma dake yarane masu nutsuwa in rabo yarantse an zubo sukance akoshe suke to tin Yana darai kenan balle da kasa ta rufemar Ido.
Rayuwa ta wahala mun dandanata tin Ina Yan saide saide muna cin abinci sai da yazama mun cinye jarin aka wayi gari abinda zamuci ma Yana gagararmu sai Kuma na lura wannan hadisin Yana yawo akanmu yadda tsuntsu Yake wayar gari bashida me bashi Kuma yakan wuni a koshe.
Duk Wanda ya wayi gari a Kano yasan gidan hajiya mariya,
indai kanada matsalar abinci ko almari to kuwa inkadaurewa layi da cunkoso tare da turmutsutsu to kuwa zaka samu agidan sadakace sabida Alla suke rabawa ,
tonima nan nake buga sammako bayan nasallamesu sun tafi makaranta nakanje nabi layin masu karbar abincin sadaka innakarbi na safe nakan dawo gida inbasu suci sannan sun dawo daga makaranta nikuma inya ragu sai inci ragowar bayan munyi sallar azahar sai sutafi Islamiyya nikuma sai inkoma karbo Mana na dare shima nakan Kai magriba bandawoba nakanzo in taddasu a kofar gida suna jirana .
bayan nazuba Mana abincin munci nakan rage wani domin su samu suyi Karin kumallo dashi ,
Zuwan nawa sai Allah Yakuma kawo Mana dauki domin innaje gurin karbar abincin nakan zauna muna yin hira da almajirai Mata dake gurin dake gurin unguwa ce ta alhazawa haka zasuyi ta Miko sadaka muna karba wannan kudin nakan tarasu domin bukatun yau da kullum yazamto yanzu indai matsala ta taso ko ta rashin lafiya ko ta makaranta banida damuwa domin Ina tara Yan kudadena.
Anan Allah ya hadani da wani mutum me sunbo tanko shima zuwa Yake karbarwa iyalansa abinci yadda yake cemin shima yara ne dashi guda uku sai kanwarsa dake kula dasu itama bakarfi ne da itaba bazawarace shine Yake futa Yana samo musi dan abinda zasuci .
yace lokacin danake da dan jarina haka zankasa Kuma in kwashe kinsan mutanamu mune muke durkusar da kanmu memakon kayi kokarin siyan kayan da talaka yakasa kodan yasami na abinci amma Ina sai katafi siyan nawanda yafi karfin ci dasha ,
yace ba irin buga bugar da banayi ke daga karshe natsaya akan kayan gwari aiko dake jarin bawai Wanda zai ja hankalin jama,a bane kaina.
sai aka wayi gari albasar ta dafe tsabar dadewar datayi ba,asiya ba suko su timatir haka nadinga watsarwa danaga basarki sai Allah ragowar kayan gida nakai sukayi Miya dasu Haka nakoma bawan ba kanin ga iyali haka na hakura hakurin dole nake tahowa nan tin daga burget da kafa nake zuwa karbar abinci gurinnan Kuma nakoma da kafa.
Bayan mun daidaita andaura tare da cewa ajalanne sadakin ba lakadanba .
yakan je yasamo abinda Allah ya bashi agidan muci dan sukansu yayan nasa sawa nayi suka dawo nan na hada danawa itakuma kanwar tasa dama akwai mesonta rashin inda zai Kai yayanne ya hanata aure to kuwa ana kwasominsu itama tayi aurenta shi Kuma gidan dama nasune sai yazuba Yan haya ciki nikaina auren dolene gudun kar awayi gari sunan yayana ya bace ya koma yayan mace don kadan daga aikin mutananmu ga inda yakamata suyi magana amma bazasuyiba sai inda ba,a sasuba.
Rayuwa muke cike da godiyar Allah domin komai atakure yake duk inda bawa yajuya badadi amma inbanda haka ace duk cikar unguwa arasa Wanda zai tallafawa marayun Allah Koda da lomar abinci ne Koda Yake ABINDA KE FARUWA KENAN sai dai ka leka waje kaga anfuto da abinci an zubawa akuya memakon abawa mabukata niko rubabban aka bani zaimin amfani ko wankewa nayi in shanya innayi wani tinani sai ince to wandama yakasa baka loma daya inashi Ina baka Wanda zaka shanya haka .
Da wuya tayi wuya sai nakoma wankau ban ritsa wata inayiba sai ga kanta a hannuna gashi banason yarannan maraici yatabasu shikansa megidan yanzu yakwan uku baikarbo Mana abincinba sakamakon masassarar dake damunsa inda Allah ya temakeni nasa yayan sundan fi nawa girma sukan saka hannu muyi wankin tare .
A haka sabo da mardiyya suka gama makarantarsu.
. dama su nasa yayan basayi Kuma ban dorawa kaina wahalar sasu ba dannauyin sai yayimin yawa.
Tafi tafi saiga sabo da mardiyya sun kammala karatunsu na secondary ammafa mun doku dan sai da aka wayi gari sutturar sawa tagagaremu amma cikin amincin Allah innadan Tara kudina nakanje wanbai indan tsinto musu kayayyaki .
Shidai sabo ya kafe sai yacigaba da karatu Kuma ban hanashiba nadai bishi da addu,ar neman sa,a da Kuma huwa cewar Allah.
*INA* *BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*
*DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU*

*ABINDA KE FARUWA*
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
*FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA*

*9(I)*
*KAINUWA WRITERS*
*ASSOCIATION*
Asanda yasa kansa karatun asannan matsatsi Yakuma zuwa rayuwarmu.
Asannanne dukkanin yaran dake gabana suka girma Kuma kowacce tana bukatar abin amfani narayuwa danma wani gida dake daura da gidanmu sun nemi da nabasu yarinya daya taringa zuwa tana Mata dan aikace aikace sai nagayawa megidan ,
Babbar cikinsu wacce take da hankalin sosai ita take zuwa aikatau din da haka muke rage wasu abubuwan Dan matar gidan takan bata Yan tsummo karanta dasu suke da yin gayu ,
cikin amincewar Allah komai ke gangarawa shi Kuma sabo yakan je yayi turin ruwa akalla kullum yakan Sami dubu daya ita Mike tarawa har Allah yasa akasami kudin registration sai ga sabo yafara zuwa University intakai cemuku dai ahaka yayi karatunsa in Yana da lakca yakan hakura da turin kurar sai ya Sami interval sannan yakeyi cikin amincewar Allah ya kammala a hankali cigaba Yake zuwar Mana domin yanzu duk na airar da yaran dake gabana daga mardiyyar har yayan malam tankon danake aure.
asannan Kuma dukkanin wani cigaba yakara zuwarma na dan wuyar da mukaci da yan zun alamu sun nuna muna dad da ketaresu domin sabo yasami aikinyi bakuma nagwamnati ba wani iyamurine yadauke shi Yake kular Masa da kantinsa cikin aminci suke zaune in lokacin tashi yayi kullum Yana bashi dubu daya ga taimakon dayake Masa na sutturu da abinci basuyi shekara biyu ba yafara yimasa zancen sallama .
Yace lokaci yayi dazan sallameka kaima kazama ubangidan kanka akwai kudade danake tara maka kullum inkatashi daga tsarin shago sannan akwai alherin dazan maka domin naji dadin Zama dakai Kai me amanane baka cutata.
Sanda zai sallameshi million biyu yabashi da mota sannan ya zuba Masha Kaya ashago yace yabashi halak malak.
Zokuga umma ranar har suddaja tayi saboda godiya ga Allah .
Aiko kudin dayake tarawa yadakko yase katon fili,
Inda kudi akwai aiki gini yayi amma bai gina gaba dayaba sai yaginawa ummansa iya gun da zata zauna kafin Kuma acigaba , ranar dazasu koma gidan suka tashi da mummunan zance domin gawar mlm tanko akashigo musu dashi ansami wani yabugeshi ya gudu.
Banida caji kuyi hakuri da wannan.
*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*
*DAGA* *ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU*
*ABINDA KE FARUWA*
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
*FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU*
Chapter 5 · 0% Book details