← Book details Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 25

Sashe 17

Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*22(V)*
*KAINUWA WRITERS*
*ASSOCIATION*
Yo amma kinsan haka Kika barni gida zaune bawani dan temako da Zaki bani Nima inkoma gidan nawa mijin kinaganin inda nake fama da babanmu nazame mata kamar kishiya Kan zaman gidannan danake..
Takatseta tare tintsirewa da dariya tace anti Wannan gigicewa haka kwantar da hankalinAInsha Allah gobe aminiya zata dawo tayi tafiya ne ai da tini kunsan juna,
zata rakaki kuwa indai wannan teacher dinne kamar kinkoma kingama kikuma jashi inda ranki keso,
Baishiga takofar dazata ganshiba sai yashigata kofar baya tinani yakeyi wai meyashiga kansane sai yayi wasu abubuwan sai yazo yayi ta tinanin hujjar yin hakan,
ummansa ce ta wado Masa da sauri ya Mike domin zuwa gunta jiyayi wani abu ya gilma takansa Wanda yasashi dafe kannasa Zama yayi yarasa meke Masa dadi wani abu yaji yatokare Masa kirjinsa dafe gun yayi Yana Kiran sunan Allah a hankali yaji Yana samun sassauci. ajiyar zuciya yasaki da yatuno wai ameeara umma ta aura Masa amma har kawo yau wai baije yaga kalar amaryarba sai da mardiyya tajashi gun dazu tsaki yayi yace yo Ni inbanda ma ta tinamin ai shaf namanta rigingine yayi Dan yafijin dadin tinanin sannan yakara murmusawa yace lallai yau ango nake akwai shagali kenan ,
tinawa yayi da sadiya zumbur ya Mike Yana lekenta ta taga kwarjini takara yimasa wani irin tsoron tane yadirar Masa sai wata uwar zufa datake kwaranyo Masa.
Yanzu umma kinsan da wannan matsalar Amma baki taba gayanba kema ameera aikya bugo kisanar Dani kome akwai Koda bazanyi maganin matsalar ba aikwaji dadin kunsanarwa da wani,
To mardiyya abinda yafi karfinka ai sai kamarshi wasa abin ya wuce tinanin me tinani sai dai Mika Al,amarin ga Allah Dan Haka karki tada hankalinki muyi addu,a akwai Allah akwai kuma lokaci dukkanin abinda mutum yayi domin kansa kedai fatana kirike Taki uwar mijin kamar itace ni Inka mutunta uwar wani kaima sai amutunta taka Kuma shi tsoho daraja ce dashi balle wannan zamanin bakayi ba ma anmaka Allah dai yasa mudace.
Hajiya Taji jiki gaskiya domin masassarar datayi takwana biyu tabata wahala Haka nasha jinyarta harta warke Dan makaranta ma sai da nadau excuse din kwana biyu saboda inkula da ita taji Dadin hakan shima megidan yaji dadi sosai ,
A wannan kwanakin datayi kawai Ina lallaba wane tasami lafiya nikuma insami nutsuwa domin kamar akwai son zuciya cikin lamarinsa yadda nake fama da dawainiyyar yarana inbasu da lafiya nice siyan magani nice sewa yaro abinda zaisa abakinsa yaji dadi Kai duk wata hidima ta asibiti nice sai dai yayi min godiya,
to Haka ma yabarmin hidimar hajiya ko kudin mota Bai bamu ba Dana matsa masane ma ya dakko dari biyu yace muyi kudin mota abinda nasan yahadani dashi kenan shiyasa nakeso tagama warwarewa nadau mataki Dan bazai yiwuba da innayi hidimar gida nasan Babu ne yanzu ko nasan akwai sauyi ba abinda ma Yake bani mamaki sai inzai bani kudi da yakan juyemin abinda Yake dashi har sai nadau wani abin aciki nabashi yayi kudin mota yanzun ko inzai bani kudi sai yashiga bandaki ya kirga sabida karnaga yawan kudin dake gareshi wato nidin Yake neman ya manta alherina gareshi,
ko Kuma inyaga nagane shi sai yajuya bayansa sannan ya kirga abinda zai bani badai zai Bari naga kudinba sabida San zuciya irin nada namiji Dan haka nakeson nadau mataki danni bazan jure irin wannan ba yazama kamar cin fuskane agareni to meyake nufi shinakeso nafara ji sannan Kuma into Masa tini da nauyin dayake kansa bani Allah yadorawa nidin wani yanki ne natemako da aka sani gareshi Dan Haka lallai komai sai an sauya Nima macece bakuma matar wahala ba inda najure yanzu Nima gashin kaina nake nema.
pls share
*INA* *BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*
*DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU*
*ABINDA KE FARUWA*
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
*FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU*

*23(W)*
*KAINUWA WRITERS*
*ASSOCIATION*
toke yanzu duk hakurin da baiwar Allahnnan tazo tabayar bemikiba mekikeso Kuma tayi miki Aiko bada gaske take ba kyayi hakuri kikoma kigani insun tuba da gaske Kuma ita rayuwar aure tagaji haka bakowa ce, mace ce take dacewa da abinda takeso ba Kota dace din akwai kalubale dasuke biyo baya ,
Umma wallahi tariga tace batasona gara muhakura Allah yahada kowa da rabonsa na alhairi shikansa tayata yakeyi abinda takemin Dan Haka kikyalesu kawai zasuga in inada Rana in ma banida ita zasu gani,
Haba zainaba Aiko sungama ganin ranar da kike da ita tinda gashi ita takasa jiyyarsa har tana kukan kitemaka Mata ki koma kodan kiyi jiyyar mijinki Aiko ranarki tagama fitowa,
Kije gidan aure ne, ai kome Kika ci Karo dashi ladane, lada kuwa me tsoka, Kuma dama masu iya magana sunce fini da gidan uba nafiki da gidan miji , fini da gidan miji nafiki da gidan uba ,
Dan Haka kitattara kayanki kikoma nikuma zanbiki da addu,ar neman sa,a ta gidan aurenki Allah ya doraki akansu ko Dan kuzauna lafiya,
Baki ta zunbura tace to ni nace yaje ya karye dazasu ce sai nayi jiyyarsa wayasani ma ko alhaki nane Allah ya Kara ma da ya karye din,
Alhakinki dan kunyi fada Kuma ya karye sai kice alhakinki ne ,
Wallahi alhakina nane banace Miki har marina yayiba ,Niko danaji zafi nace Allah yasakamin ko a tsokar jikinsane Aiko gaba yakuma wallahi inkarayi Masa wata addu,ar.
Hannu tashiga tafawa , tace niyasu dama bana hanaki yiwa mutum irin wannan addu,ar ba dama baki denaba Aiko ko kinaso ko bakya so sai kinyi jinyarsa tinda ke kikaja masa Allah yashirye ki yarabaki da wannan baki naki,
Haka ta tattarata tasa aka rakata gidan ranta baisoba Dan ita tagama da Yan kayansu, tana da hakuri da juriya amma inta botsare abin bakanta,
Sanda sukaje gidan dagashi sai baban ,
tana ta kiciniyar dagashi zata dorashi afo takasa,
dama takan leka waje ne inyana bukatar temako irin wannani tasami irin masu zaman majalisa su temaka Mata tosuma ganin tana damunsu yanzu sundena zama shiyasa yanzu Kan ta daga shi sai ta wahala,
Sannu suka Shiga yimasa itako dauke kanta takuma yi gefe Saida kanwar babanta tace tashi kitemaka Mata Mana Kika zuba musu ido bamu mukulin dakinnaku sai mu Shiga kafin kifito,
Mika musu nayi suka tafi domin bude dakinnawa,
Niko Dakar cikin bacin Rai nadoshe su duk yarame sai ido dama shi Abu tibar kalla gwaragwara,
Haka badan naso ba nakama matashi ta zare Masa wandon nikuma na turo Mata fodin ta daidaitashi ,
Ruwa ta tafi ebowa na tsarki ta barni dashi,
Ahankali ya kalleni yace Zainab abin har yakaimu ga haka kikasa yimin sannu da jiki,
O sannu ko to madallah,
dakasamu nadawo kaga in matsamin zakayi da magana wallahi sai na koma dama tilas akayimin nadawo sai kace Nina karyaka,oh Ashe fa alhakinane gara ma Haka wallahi duk Randa kakuma sa hannu ka mareni adduar da zanma tafi wannan ,
Na murguda Mai baki,
Kallonna kawai Yake yace Zainab ko me nayi Miki yakamata kiduba halin da nake ciki ki tausayamin ninasan abinda nakeji inhar wannan radadin danakeji alhakinkine toko nadandana kiyi hakuri badan niba kuskurene nariga nayi bazan sakeba lokacinma sharrin shedanne amma nasan bakida laifi duk laifinane Dana baba,
Hhh Allah sarki Ashe kasani katake ai shikenan inkun gyara magyara inba hakaba daidai nake Dana bar gidannan inyaso wadanda kake kaiwa zumar taka sai suzo ku hadu kuzauna agidan ,
Tashi nayi natafi dakina Daman a dakinta take jiyyar tasa tararwa nayi suna Shirin tafiya Nan mukayi sallama dasu suka tafi nikuma na haugyaran dakina inajinta tana kwalamin kiran inzo ayi Mai tsarki Niko nayi banza da it's nabi lafiyar gado,(illar takura kenan Tin mutum naganin mituncinka har sai kakoma dakai da Babu duk daya wasu surukan kenan ).
Damisalin karge takwas ne nadare dukkaninmu muna zaune atsakar gida har da hajiya wacce take cikin nishadin kasancewarta da jikokinta cikin koshin lafiya gefe daya nanace da su saddiku zaune tana koya musu homework can gefe shimfidar babansuce wacce najere Masa kayan abincinsa akai har da su lemo na hada Masa daga gefe cikin abincin kuwa dankwa leliyar jelace takifi tare da kwai guda daya aciki ,nikuma tawa shimfidar tana tsakanin tasa data hajiya,
Suna cikin homework dinne sun bude littafin maths sai ga takarda tawado daga ciki aminullahi ne yayi sauri ya dakko
*ABINDA KE FARUWA*
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
*FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU*
Chapter 17 · 0% Book details