Sashe 2
Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*ABINDA KE FARUWA* *LABARI DA RUBUTAWA* *BY* *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* **INA KARA JADDADA GODIYA TA GAREKU NIKAINA BASAI ANMIN TINIBA NASAN WANNAN NOVEL YA KARBU SAI DAI IN GODEWA ALLAH ,FANS KUDIN DAI KUNE MASOYA SHIKUMA MASOYI KULLUM* *ADDU,A AKE MASA ALLAH YABAR KAUNA* Wannan gida metare da abin mamaki bakowa bace matar gidan sai karimatu sarkin karamci mace metarin albarka da karama. sunyi aure da mijinta me suna shu,aib aure nena soyayyar Kuma soyayyar ta kuruciya sanda ya aureta shekararta goma Sha shida yayinda Yake da shekara talatin da biyu tattali soyayya duk ya gwada Mata, Bawani abune da Shiba sai rufin asiri da Kuma taimakon Allah Dan kasuwane bakuma kayansabane kayan yayansane Wanda suke uba daya dashi yakan kular Masa da Kaya daga karfe Tara nasafe zuwa karfe bakwai namagariba dukkanin wata wahala shiyake Masa sai dai in lokacin tashi yayi yakan bashi naira dubu daya itace kudin sallama da ita Kuma muke sabgoginmu cikin amincewar Allah inzai futa yakan bani kudin cefane nayi Kuma harnasami dan abinda Zan adana hakan bayana nufin yin abinci Mara dadiba domin anyimin tirenin sosai kangirki. Kayan abincima bamu da damar ajiyewa sai awo mukeyi yakan siyo kwano biyu da taliya kamar biyar da dan abinda ba,arasaba lokacin ana amfani da kananzir yakan siyo galan daya sai indade Ina amfani dashi lokacin duk rayuwar Bata tsawwalaba shikansa kananzir din lokacin dari biyu da ishirinne galan shinkafa tanayin dari biyu da hamsin shiyasa mukan wadata ga shi bakowa agaban kumafa karkuce agidan kanmu muke a,a hayace mu biyu ne agidan babu kalubalen da ban fuskanta a narayuwar gidan haya dukkanin kalubale naci Karo dashi sai da yazama ni nakewa abokiyar zamana komai yi wannan yi wannanyayanta girki wanke wanke shara Kai hatta jajjage ninake Mata Wanda zatayi Miya dashi hakan baisa na kubutaba. Sai da aka wayi gari bama Shiri gashi nadoshi shekara ko ciki bani dashi itako yanzu ma tsohon cikine da ita. Hatta me gidan sai da yazama bama Shiri dashi balle dake su gidan sune kodan zaman tsakar gida danake domin Shan iska sai da ya gagareni hakan Kuma baisa nataba gayawa shu,aibu ba sai dai Wanda akayi yananan yakan bani hakuri tare da cewa me hakuri Yana tare da Allah . Asalin dena zamana atsakar gida shine ,nidin ma abociyar karatun littafice lokaci akwai fitilar kwai Ina zaune natasata gaba Ina karatu shikuma megidan damuke haya zai kunna inji yaduba yaga bamai hala ya futa yanemo nikuma bansan illar dake tare da man fetur ba shi ko ita damuke zaune da ita agun basuyimin maganar nadauke futular lwannan Haka ya bude yahau durawa Aiko futular karfin Wannan man fetur yasa takama da wuta nikaina sai da jikina yakama da wuta nayi ta tsalle Ina ihu domin radadin shiigar wutar hannuna da kafa fuwana . Hakan danayi sai yabasu dariya nikuma Allah ya temakeni ina burgima wutar ta mutu amma nakone haka namike nakoma daki tindaga sannan bankuma zaman tsakar gidanba komai zafi inda Allah ya temakenima dakin falle dayane. Ashe so suke sutashemu Wata rana naje gidanmu biki wajan misalin karfe bakwai kowa ya watse nace da mamana nidai bazan komaba nagaji . Tace wani Abu Yake mik nace a,a tace to meyasa Kikace bazaki koma ba nan nake gaya Mata yadda nake zaune damasu gidan Aiko ta Kira babana ta Gaya masa mukasha fadan barina da tayi nayi dare yace saiki jirashi dannasan inyaje yaha bakyanam zai biyoki intazo kibishi zamu tattauna dashi daga baya kinji kiigaba da hakuri. Baizoba sai misalin karfe goma domin inyadawo daga kasuwa yakanje makaranta Hala muka shige muka tafi Yana Kuma bani hakuri kiyi hakuri komai Yana da lokaci hajiyata kullum takanyi min addu,ar allah ya ginamin nawa duk da bani da hanyar dazan Gina amma uwace Kuma nasan Allah zai amsa komai dadewa ki Kara hakuri muna tafe muna hira bamu muka Sami motaba sai kusan goma da rabi hakanne Kuma yahanamu zuwa gidan da wuri , Sanda mukaje sun rufe gidan akalla munkai awa biyu nidashi muna bugu amma ba alamar budewa sai kusan shabiyun dare sannan me gidan ya bude Yakuma ce bazamu shigar Masa gidaba yasallamemu haka muka ringa bashi hakuri har Makota sai da suka fito mutumin nan yaki adaran muka koma abin hawa kuwa Babu sai wani Medan acaba muka gani shi kwal a titi haka muka hau nida shu,aibu ya kawomu gida. Wannan kenan nidin dake babana akwai wani gini da Yake domin yanaso ya koma Jin haushin hakan sai yace mana mu koma gidan tinda akwai inda zamu iya Zama, dake Yana da tinani Mai zurfi sai yayi min bayanin Dana fahimta , wani gidan aka sake samo Mana Ni kadaice sai dai shima Yana tare da kalubalensa irin tsohon gidannan ne kofofinsa ma said ka during kusa. Mahade gobe yanzunma dannayi alkawarine masoya shiyasa nacika nagode da bani goyon baya. *INA BUKATAR COMMENT DINKU IN HAR KUNASON INCI GABA* *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU *ABINDA KE FARUWA* *LABARI DA RUBUTAWA* *BY* *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* * 5(E)* *KAINUWA WRITRS* *ASSOCIATION* Yan kudin danake Tarawa suna fito dasu nasamu makarantar matan aure nakoma ta asabar da lahadi bansha wata wuyaba suka karbeni naci gaba da karatu . daga baya kayan dakina naringa yiwa dauki daidai harnagama karatuna ko ficikarsa Babu har nagama, har kullum salamar zuciya meyake su akasuwa sabida nasan inma nadaga hankali inba jiknsa zai dinga yanka Yana baniba tofa sai dai in rigima nake nema, Ga Kuma mahaifiyarsa da kullum acikin abinda Yake samu Yake kikarin kyautata Mata danma matar mekarace takance kaji da iyalinka nidin Allah bazai hananiba. Cikin shekara uku na kammala tare da zana jarrabawar GRED II Kuma har time din ban haihuba ana tafe a lokacin sai siyasa ta kunno Kai dake Yana dan buga bugarsa ya nemamin aiki tare da cewar sai incigaba da karatuna bansami koyarwar da mukeso ba sai aikin nanny nasamu haka nafara inayi Ina temakawa kaina hakan Kuma bairageni da komaiba sai dai kokarin kyautatawa nima Kuma nakan kyautatamar daidai iyawata Ina kula da aikina sosai duk da rainon yara akwai wuya todai haka nake Kuma inajin dadi , Watan da akafara biyana albashi kamar nazuba ruwa a kasa nasha naira dubu shida da dari takwas akabani nayi Munna sosai tare da kokarin cigaba da karatuna shima cikin shekara uku nagama sanda nakarbi takardun haka yayita fadi tashi gurinne momin APPROVAL FOR CHANGE OF CADRE cikin amincewar Allah nasamu asannan Kuma sai albashina yakoma matsayin na malaman makaranta merike da aikin government school aka maida ni GL 7 naji dadi nayi murna banyi shekara da fara koyarwar ba nasami ciki nayi laulayi sosai har Allah yasaukeni lafiya nasami kyakkyawar yata sunan kishiyar babassu yasamata nana Khadija amma nana muke cemata shikansa kayan haihuwar inzanje awo yakan bani dari biyar ko abinda yasawwaka ahaka muka Tara kayanmu daga baya da yakasa karasa soyayyar haihuwar nice da mukayi albashi nakoma na Karo duk abinda babu har dinkunan futar suna ninayiwa kaina haka ya tattarasu yakai gidansu suka gani sukuma suka Kai gidanmu amatsayin kayan haihuwa bawanda yasan nice karfin hada kayan haihuwar haka mukagama hidimarmu hatta abincin suna haka muka hada kudinidashi akayi batare da sanin kowaba . Bayan nagama maternity leave dinane nacigaba da zuwa aikina asannan Kuma akayimana promotion zokuga murna guna kafin asakar Mana salary sai da aka fara bamu notification of appointment banyi zaton kudin zasu shigo Mana da wuriba amma cikin ikon Allah muka samu a watan da akayi. Duk Kuma abinnan baitaba samin Ido akudina ba Kuma bantaba daukar naira biyar nabashiba domin nidin Allah yazubamin hangen nesa duk abinda zanyi inhar nasan zai damuni bana tinkararsa nasan inhar nafara daukar kudi nabashi tofa akwai matsala agaba nasan dai dukkanin wasu abubuwa daya gaza nakan yi batare da damuwaba ko akaina ko acikin sabgar cikin gida Kuma har yanzu bai ragemin komaiba a kudin cefanen dayake bani sai dadima danake tintibarsa yayi domin jiya bayauba komai yafara tsawwala kudin dayake bani basa Isa yin komai balle yanzu daya koma bani har kudin awo sai nakoma in akayi albashi sai nashiga kasuwa nayo Yan tsince tsince harsu doya dankali komai na abinci nakan siya in ajiye inya bani kudina sai incigaba da sabgata daga baya nafuskanci karancin kudin dayake bani. Kuma har time din muna wannan gidan Kuma duk shekara muna fuskantar matsalar damuna ga aljanun dasuke firgitani damma inada karfin addu,a tareda rashin tsoro wani lokacin Haka zasuyita firgitani har nakan futa aguje ko Kuma suringa yimin gizo danaga Ina cutuwa shine nama tsanta sai muntashi toshikuma yakancemin bashida kudin dazai kama wani sai dai in Zaki cika sai akama wani ,yo nidinma dake wani lokacin basauki amma Kuma Ni tinkafin matsala tafaru nakanyi kokarin maganceta ,sai nace Masa gaskiya bazan iyaba yayi kokari dai yasamu mutashi . Haka muka cigaba da rayuwa har Allah ya horemasa muka koma wani gida shikuma mugoma Sha biyu ne a gidan amma fa ba,afiya tashin hankali ba sai kaso bare ma ni dabana Shiga shirginsu Kuma Allah sai yazubamin kwarjini suna girmamani ko gulmarsu suka tashiyi basa sani ciki inko anyima inanan baruwana bana Shiga balle ace dani asannan nana tana da shekara hudu asannan nakuma samun cikin saddiku sai abin yazo da goshi Musamman dake da addu ,ar uwa atare dashi ankuma wadawa hatsaniyar Zabe sai wani kanin babana yayi kokarin sama Masa delegate aiko ya samu haka suka kwana kusan uku suna kaiwa suna kawowa domin su zabi Wanda yacancanta dake kowa yakan futo da abinda zayyi kamfen dashi akalla ko wani delegate sai dayatashi da rabonsa shikansa dayaringa bani ajiyar kudin Saida na kirga naira dubu dari hudu da arba,in anan yafara kasafin siyayyar dazaiyi min Musamman dayasan yagazamin a wasu abubuwa Aiko natubure nace bansan zanceba saidai yayi Mana gini ko ba,a gamaba nizan koma ko falle dayane Aiko yayi Munna, yace da Kuma inaso inyiwa su hajiya alheri nace ban hanakaba nidin danaga ruwan kudin nayafe maka balle Wanda baigansuba kasan Kuma hajiya Inka Bata kudi rabarwa zatayi kasamu kasai mata wani abinda zata amfana sukuma kannanka ko dubu bibbiyu kabisu da ita yawadatar tinda kaidin mabukaci ne haka muka zauna aka tsara yadda za,ayi daya je yayi wa hajiya bayanin yadda mukayi