← Book details Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 25

Sashe 14

Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

*19(S)*
*KAINUWA WRITERS*
*ASSOCIATION*
Dakar take Jan jikinta ga haihuwa tataho amma batasan yadda zata taimaki kanta ba ,
nishine yataho Mata hade da tahowar wani abu agabanta hannu tasa tashafo jinwani abu tayi kunduldul yatokare mata hankalinta Yakuma tashi ga azabar ciwo ,
Haka tayanke shawarar kiransu dan dole badan tasoba amma cikin ikon Allah takasa yunkurawa data matsa sai ta mikene tatake bakin zaninta aiko abin tausayi menakuda akasa Jikake tim inda Allah ya temake tama goshin tane yabugu,
hakan yayi dai dai da shigowar me gidan aguje yayi kanta jijigata yashiga yi amma dake ta bugu sosai ga Kuma halin ciwon daya gala baitar da ita sai tatafi luuuu,
Kaiwa Yake Yana kawowa yarasa mezayyi gashi su kansu likitocin tinda suka Shiga da ita bawanda yafito tinanin Kiran iya yanta yayi Aiko cikin kankanin lokaci sai ga Yan uwanta sun cika asibitin kowa yayi jugun jugun,
Aikin yafi karfin nurses sai da suka Kira likita babba, bayan zira safa ahannunsa yashiga dubata anan yagano inda matsalar take wato dan jinjirinne badai daiba sannan hannunsa yashige wani dan lungu acikin gabanta,
Haka yasa hannu yadinga juya dan cikin ikon Allah sai gashi yajanyoshi waje ,
Wata Kara tasa data gigita alhaji sabo da Yan uwanta can Kuma sai suka jiyo kukan jinjiri ,
Sannu doctor din Yake Mata kafin yabada umarnin a gyarata ita da jinjirin ga Kari data samu kusan guda biyar haka tanaji tana gani suka dinketa kamar kwarya( Kai yau sadiya taga banu domin manta kanta tayi)tanaji tana gani aka daureta before ayi Mata dinkin.
Bayan bakin gumurzun datasha ne akafito da ita dakin hutu aiko dangi sukayi ta tururuwar ganin me jego da dan jinjirinta,
Shiko angon karnin sai mika wuya yakeyi , yayarta ce ta hangoshi tayi dariya tace kubashi guri Mana muntsare masa abin kallonsa karya kasa hakuri yabi takanmu, Aiko meza,ayi Banda dariya,
Shiko cikin Jin kunya yakarasa ciki hannu yasa zai dauki yaron tare dayi mata sannu yayi Kuma daidai da tambayar da suka jefo Masa narashin ganin babassa tare da abokiyar zaman sadiyar,
Jiyayi kamar andaki tsakiyar kansa sai sannan ya tuna da su ,
Shaf ya manta da Suma ko tinanin su bayayi yanzu yakan shafe kwanaki bai je yaganta ba balle wata amarya da baije yaganta ba balle yakara tantance yadda take,
Wayarsa yadakko zai buga mata hannun sadiya ne yariko wayar dayake kokarin bugawa,
Cikin hawaye take magana bana bukatar kowa acikinsu domin sune silar wuyar danaci nanemi taimakonsu sanda nafara ciwon bawanda yakulani daga karshema umma cewa tayi Allah yasa na mutu nida dan, hawaye take zubarwa kamar gaske ,
Aiko dukkaninsu sukayo kanta dama bakyajin dadin Zama da ita ko kuwa?
Take dama hakuri nakeyi shikansa yasani gashinan akwai randa tace ma zata dakeni sai da nagudun gudun kartayimin illa Kuma Ni ba iya ramawa zanyiba kodan darajar danta.
Jiyake kamar yafashe saboda fushi yaji baya kaunar yaganta ma bare har yace mata wadda bata kauna ta haihu yanzu umman sace take masa haka baice komaiba yajuya afusace yafuta.
Sukuma dangi sunsamu abinyi sai aka bude babin gulmar takurar da uwar mijin sadiyar kemata harda zancan auran datayi masa kowa ya tausaya mata dimin tagaya musu cewar tinda yayi auren hakuri takeeuwarsa tasa yajuya Mata baya yanzuma Dan haihuwa tayi suka ganshi .
Tinda yakoma gida Yake fama da bacinrai yaso daurewa aje yaga mahaifiyartasa amma wani bakin ciki dayakeji akanta shiya hanashi zuwa,
Itako baiwar Allah dukkanin wata damuwa tasaukar Mata domin sanda yafuta da sadiyar taji tashin motarsa lokacin ameera tana gunta suna hira Jin tashin motar bana kwanciyar hankali bane yasa suka fito amma tini yayi gaba ,
Megadi ta tambaya lafiya ?
Anan yake gaya mata matar gidance ba lafiya addu,a tayi mata suka koma ciki batasan asibitin daya kaita ba bare suje ita da ameera haka suka hakura suka zubawa sarautar Allah Ido sanda yashigo gidan tajishi jira take yashigo taji meke akwai amma har yashare fiye da minti goma ba labarinsa,
Yankewa kanta shawarar binsa tayi ,da sallama tashiga falonnasu Yana zaune yayi tagumi cikin firgici sukayi kicibis da juna aguje ya Mike yayi cikin daki itama juyawa tayi tafita da sauri tsna Kiran innnalillahi wa Inna ilaihirraji un,
Tinanin ta gamo tayi shikansa yazata gamon yayi amma Kuma ai muryar ummansa yaji tana sallama meke faruwa ne.
Hala tashiga nata dakin tana me maimaita addu,a a bakinta ameera ce ta tareta tana tambayar ta lafiya ?
Garu tabi tadinga yin kasa domin jitayi wani Abu na yawo akanta,
pls share
*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*
*DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU*
*ABINDA KE FARUWA*
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
*FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU*
Chapter 14 · 0% Book details