← Book details Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 25

Sashe 19

Abunda Ke Faruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

*25(Y)*
*KAINUWA WRITERS*
*ASSOCIATION*
shiko gogannaku Yana can rungeme da amaryarsa babu komai aransa sai farinciki domin shikadai yasan abinda yaji gashi Kuma ankwan biyu dama ba,a haduba tinda cikinta yayi wata shida tasallamashi,
Gashi yanzu ameera ta ibeshi izuwa duniyarta tashayar dashi zumarta dago fuskarsa yayi Yana Kare Mata kallo ,
Koda ya rayuda ita inuwa daya baisan tana da tarin baiwa hakaba Musamman dayakaiwa dukiyar fulaninta kallo ,jikake makwatttt ya hadiyi wani tattauran miyau abakinsa ,
Yana bukatar kari sai dai yatausaya Mata Dan yabata wuya domin yayi Mata shigarka sauri har sai da tagala baitar,
Sadiya ce take ta sintiri tsakanin falonta da bakin dakin sadiya sotake tatada Bala,i a wannan lokacin amma sai rahane ta hanata tace tabari gari yawaye kokuma tayi shiru sai akara daukar mataki don inkikayi magana karshenta azo takwabe.
Yo badole ta kwabeba zasusan suntaboni wallahi sai na yimata hukunci kwatankwacin na uwarsa zasusan koni wace ,au wato inanan kwance baki sake su Kuma suna buduri,
Tashi tayi da hanzarinta tafuta kofar dakin tahau bugu tana bala,in su bude kotakarya kofar ,
Kana Ina bakin munafuki harni zaka yaudara kashige dakin wata ke Kuma zakisan kinkwana da mijina shegiya matar shige zakiga katshen auran da akayimiki kesa kwanciyar hankali har abada,
Ai alhaji sabo Bai San sanda yahan kade ameera ba aguje yatashi yahau laluben rigarsa ,itako ameera tsabar furgicin datashiga kasa gane komai tayi ga azabar bugewar da tayi agoshinta dafe take dagun itama tamike tana neman yin waje Dan bugun da akeyi tare da masifar sadiya sun mutukar daga Mata hankali,
Hannunsa dake faman rawa yasa yariketa rigar dayakarba dazu ahannunta yadaula ya Mika Mata ,
Yace yi sauri kisa sadiya ce bansan ya akai tasan inananba,
Binsa tayi da kallon bacinrai tace bazan sakaba ai ba Zina na aikataba inta isah ta shigo cikin dakin taga Nima nawa Rashin mutuncin ,
Tsugunawa yayi Yana Bata hakurin ta rufa Masa asiri kar ta Ganta ahaka,
afurgice yasake mikewa dalilin karfen datasamo tana bugun kofar dashi Wanda yatashi mutane dasama ciki ko harda umma Dame gadi kowa hankali atashe yayi waje tare da neman Karin bayani ,
Aiko kamar ankuma tinzirota tasake hawa kamar farashi har dacewa umma ce ai babbar muna fukar data hada komai,
Aciki kuwa ameera takasa ta tsare da tsiraicinta tace wallahi sai dai tashigo taganta a haka inyaso zuciyarta sai ta buga,
Zufa tare da tsoro da nadama duk singama shigarsa sai kaiwa Yake Yana kawowa yarasa mafuta,
Umma ce tayi magana take ameera zoki budemin Koda kinji bude yafuto kozata barmu mukwanta miyi bacci da safe sai ayiaganar,
Zani tadaira akirginta sannan tasa hijab kofar ta hau kokarin budeta ,daga wake kuwa sadiya ce ta saita karfen dake hannunta tanason tasaukeshi Alan ameearan ,
Ummace ta lura da hakan tatsawatar Mata,
Ina ruwanki kome nayi kishiyarki kotawa duk abinda nayi idone naki ta murguda baki ,rahane ce tajata baya gudun kar azo ayi danasani,
Shiko halin dayake ciki yafi nada tinda yaji muryar umma wani Abu yazo ya gifta ta tsakiyar kansa shikenan dikkanin wata nutsuwarsa ta kauce yanzunma arabe harke har ameeitabude kofar anti anyi ya futo yaki daga karshema cewa yayi shi tsoro yakeji waddatake maganar Nan sai ta bargun zai iya wicewa,
Sadiya ce tayirkaraf tace to ai sarakan shishshigi sai a matsa yace bayasan ganin mutum anan,
Share hawayen days zibo Mata tayi tace yanzu sabo nice abar jintsoronka ?
mutum dai yaki tsoron Allah sadiya akwai ranar kin dillanci kuma duk abinda kikeyi akwai karshensa ko badade ko bajima Musamman da Allah yayi Miki tukuici dasamun haihuwa Ina meyi Miki tini daki guji duniya babu komai cikinta sai rudani,
Kanne Mata Ido daya tayi tare da tsartar da miyau,
Abinda tatsana kenan tin tana kuruciya in aka tsartar Mata da miyau takan dau hukunci Alan komawaye Dan wannan shine karshen wulakanci takan dauki komai amma Banda wannan,
Wannan abinda tayi matane yasa tadaga hannu ta kwada Mata Mari Marin dayayi sanadin abubuwa da dama ciki kuwa harda nadama datake biyo bayan rudaddun abubuwa.
*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*
*DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU*

*ABINDA KE* *FARUWA
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
*FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU*
Chapter 19 · 0% Book details