← Book details Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 26

Sashe 9

Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wato har yanzu baki daina karance-karancen littafin Hausan ba? Kenan duk nasiha da kuma faɗan da nake miki baki ɗauka ba? Laifina ne da na sayi waya na baki, ki tashi ki ɗauko mini wayar daga yau babu ke babu riƙeta har sai kin gama secondary school an kusa miki aure. Ina ce dama auren kike so shiyasa kike karatun soyayya? To ko yanzu wani ya zo yace yana sonki aurar da ke zan yi sai ki je can kiyi karatun da tushe."

Kuka Surayya ta saka ta fara bawa Mamansu haƙuri amma ta kafe, ƙarshe ta zare mata ido ta ce in ta sake magana sai ta mata duka. Da haka ta tashi tana kuka ta tafi ɗakin baccinsu don ɗauko wayar tata.

Nan ido ya dawo kan Juwairiyya wacce ta wani gefen ta ji daɗin karɓe wayar Surayya, domin watarana har ƙarfe biyun dare take kaiwa tana karatun novels wanda ta tabbatar ciki har da na batsa tunda ya zama tamkar ruwan dare a gurin marubutan online ɗin. Ta wani gefe kuma ta ji tausayinta domin in bata manta ba itama a baya Mama ta sha kwace nata tana ɓoyewa in tayi laifin da ya kai a hukuntata da haka, tana tunawa in aka kwace sai ta ji kamar ranta aka karɓe ta yi kuka har ta bonu kafin ta haƙura.

"Ke kuma kika zauna kina ta ashariya a gabana ko? Mutum daga cewa yana sonki sai ki ce zaki tara yara su mishi wanka da kwata? Ke Æ´ar daba ce ko Æ´ar iskar unguwa?"

Shiru Juwairiyya ta yi kanta a ƙasa tana wasa da ƴan yatsunta.

"Ina tambayarki kina mini shiru."

"A'a Mama."

"To wallahi akul in ji ko baƙar magana kin mishi. Ki nemi yanda zaku rabu lafiya kar in kuskura in ji abun da zai ɓata mini rai, ba tarbiyyar da na baku ba kenan. Allah Ya gani nayi iya bakin ƙoƙarina kuma ina kan yi akan tarbiyarku har kika yi aure ana yabonki a cikin unguwar nan cewa kin fi sauran ƴan matan kamun kai. Baku tashi da uba ba amma ba'a zageku a dalilin rashin gurbinshi a rayuwarku ba. Kar ki ga kuma kin taɓa aure kiyi tunanin zaki ci gashin kanki a cikin gidan nan, as far as ni nake ciyar da ke, kike kuma zaune a gidana ni ce mai last say babu abun da ya canja."

Sumayya mai bin Juwairiyya, tana da shekara sha takwas wacce a yanzu ta gama secondary school tana gefe tana jinsu, ita dama ba kasafai ake mata faɗa ba domin tana kiyayewa sannan kaff yaran Mama ita ce shiru-shiru. Autansu Walid kuma shine yake son gagaran Mamarsu, shekararshi yanzu goma sha ɗaya amma yawo ya saka a gaba sannan baya son karatu. Kuma duk dukan da zata mishi ba zai hana gobe ya ƙara abun da aka dakeshi a kai ba. Wannan kenan.

"Adda Juwai wai Hussaini yana waje." Faɗin Sumayya daga can bakin ƙofar ɗakinsu.

"A faɗa mishi na samu mijin aure har na ƙarɓi sadaki." Ta bata amsa a numfashi ɗaya.

Dariya Sumayya tayi sannan ta wuce ta faɗawa yaron saƙon yayartata shi kuma ya fita don isar da nashi. Sai dai bai jima ba ya dawo.

"Wai don Allah magana ɗaya zai faɗa mata ta yi haƙuri ta fito."

Tun kafin Sumayya ta shigo Juwairiyya ta miƙe a hanzarce domin a yau tana son ta kawo ƙarshen rainin hankalin Hussaini, ta gane in ba ita ta sameshi suka yi magana ba zai yi wuya ya haƙura ya barta.

A bakin ƙofa taci karo da ƙanwar tata,

"Ohh ashe kin jiyo mu."

"In ba saitashi nayi akan hanya ba yanzu zai buɗewa sauran ƙofar zuwa su dameni. Ba aure ne a gabana ba, kwata-kwata ma yaushe Hafiz ya rasu? Yanzu ne ma yake cikin wata na shida shine zai zo mini da maganar banza?"

"Kiyi haƙuri, wasu mutanen basu da lissafi. Amma dai ki bishi a hankali kar yi abun da Mama zata miki faɗa."

Bata amsa ba ta wuce waje tana rangaji domin ramewar da ta yi har yanzu bata maida jikinta ba. A ƙofar gida ta samu Hussaini jingine da gate ɗin gidan nasu yayi wata tsayuwa tamkar ciwon baya, shi ala Allah yayi hakan ne don ya burge Juwairiyya.

"Gimbiya kuma tauraruwa cikin mata. Nagode kwarai da kika bani wannan damar na ga kyakkyawar fuskarki."

"Shi ɗan aikan bai faɗa maka cewa na karɓi sadakin wani ba? Ko ƙarya kayi da ka aiko cewa magana ɗaya zaka faɗa mini mu rabu?"

"Ashsha! Kin san Bahaushe ya ce matar mutum kabarinshi. Sau nawa ana taruwa don É—aura aure amma ki ga an watse saboda Allah
bai yi zasu zauna a rufin auratayya ba?"

Wani malolon baƙin ciki ne ta ji ya zo ya tokare mata a maƙoshinta, so take ta kurma mishi ashar ta zagi uwarshi da ubanshi ta yanda ko labarinta ake yi zai bar gurin amma Mama ta mata katanga da aikata hakan. Don haka kamar zata yi kuka ta ce,

"Hussaini ina ganin girmanka ina kuma tuna zaman da muka yi a school cikin aminci, don Allah ina roƙanka kar ka ɓata wannan zumuncin. Ba aure bane a gabana ba, in ma auren ne ba zan aureka ba dalilin na ƙarbi sadakin wani. Neman aure a cikin wani auren haramun ne kar ka saɓawa Allah don son zuciyarka. Na barka lafiya." Ta juya da niyyar shiga gida ya sha gabanta ya haɗe hannayensa guri guda.

"Wallahi Juwairiyya tun muna makaranta nake sonki amma nasan kin fi ƙarfina shiyasa ban taɓa nuna miki ba, yanzu kuma da kike bazawara ni kuma nake saurayi na san akwai chance ɗin kasancewarmu tare kuma wallahi ba zan damu da maganar mutane cewa na auri bazawara ba. Ki ceceni ki karɓi soyayyata don wallahi na jima da sonki a birnin zuciyata."

Yanzu kam ji take yi kamar ta rufeshi da duka har sai ya daina motsi, wani wawan kallo mai cike da tsana take bin shi dashi. A yanzu bata damu da duk hukuncin da Mama zata ɗauka a kanta ba, sai ta zage Hussaini zagin da ba'a taɓa mishi irinshi ba, zagin da ko a hanya ya ganta zai canja akalarshi.

Ta buɗi baki da niyyar fara azalzalarshi motar Muhammad ta yi parking a ƙofar gidansu. Da ita da Hussaini tsayawa suka yi suna ganin lokacin da Muhammad ya buɗe marfin motarshi ya kwalawa wasu yara kira dake kan yashi suna wasa, da gudu suka iso gurinshi fuskar nan tashi kamar kullum a turnuƙe amma ba shine damuwarsu ba, ɗari biyu-biyu da zai basu in sun gama mishi aikin ne damuwarsu. Suka gaisheshi bai amsa ba, dama sun san za'a rina wai an saci zanin mai hauka.

Nuni ya musu da booth ɗinshi ba tare da ya buɗe bakinshi ba, babu wani dogon bayani suka nufi bayan motar suka buɗe kana suka fara fito da kayan abincin da suke ciki suna shigarwa cikin gidansu Juwairiyya, ba kaya ne masu yawa ba illa ƙananun buhun shinfakar dafawa da ta tuwo, kayan haɗa shayi, sabulun wanka da wanki da kuma manja, mangyaɗa da maggi.

Duk abun nan da ake yi Juwairiyya da Hussaini suna kallonsu amma shi ko kallo basu isheshi ba. Wani tunani Juwairiyya ta yi wanda yasa wani murmushi ya wanzu a fuskarta kana ta dubi Hussaini da É—an damuwa a fuskarta ta ce,

"Ga wanda na karɓi sadakin nashi, don Allah in ya fito ka nuna mishi gaisuwan rasuwa kawai ka zo ka mini, ka ganshi ƙaton nan wallahi in ranshi ya ɓaci dukanka zai yi."

Muƙut Hussaini ya haɗiyi yawu kana ya dubi yanda Muhammad yake ƙoƙarin fita daga mota girman jikinshi na bashi wahala. Bayan ya fito ya miƙawa yaran ɗari biyu-biyu kamar kullum suka tafi murna fal a fuskarsu, abun ka da yaro, basu san cewa shimfiɗar fuska ta fi ta tabarma ba.

Ganin ya nufosu fuska a tamke yasa Hussaini ya mata sallama ya tafi ba tare da ya tsaya sun gaisa ba, shi har cikin ranshi ya yarda Muhammad zai mishi duka, ina shi ina faÉ—a da wannan basamuden?

"I see har kin fara tara zawarawa a ƙofar gidanku." Ya faɗa bayan ya iso gabanta.

"Idan wannan ne ya kawoka kayi saurin tafiya don baka da amsa."

"Salima ta haihu."

"Ina sane."

"Yau suna bikin suna."

"Shima na sani."

"Ta haifi yaro É—a namiji."

"Haka na ji." Da haka ta juya da niyyar komawa cikin gida amma ta tsinkayi muryarshi yana cewa,

"Na saka mishi sunan abokina Muhammad Hafiz." Da haka shima ya juya ya koma motarshi don dama ya gaji da tsayuwar.

Juwairiyya daskarewa ta yi a gurin tana jin kanta kamar ba'a duniyar take ba, wai da gaske Muhammad ya raɗawa ɗanshi sunan masoyinta Hafiz? Nan da nan sai ta ji kunya ya rufeta domin bata kyautata mishi duk da ƙoƙarin da yake yi a kanta. Sai dai tana juyawa ta ga yayi reverse ya tafi.

Tun bayan rasuwar Hafiz ya koyi yi mata magana, ya mata ta'aziyya wanda daga shi har matarshi a gidan karɓan gaisuwar suke yini tun safe har dare har aka yi sadakan bakwai. Sannan ta samu labarin da Muhammad ɗin ya ga gawar abokin nashi kuka yake cur-cur da idanunshi har aka yi tunanin ƙin zuwa dashi maƙabarta don kar ya ga sa'ilin da ake saka abokin nashi a cikin ƙasa ya rasa hankalinshi. Sai dai babu wanda ya isa ya hanashi, ya je kuma tare da shi aka bunneshi bakinshi bai bar motsi ba har aka dawo yana mishi addu'a.

Juwairiyya ta san Muhammad ba wani mai wadata bane amma ya ɗaurawa kanshi wahalanta, domin kuwa kowanne wata sai ya yi mata shopping na kayan masarufi daidai ƙarfinshi ya kawo mata ya kuma gaisheta. Daga nan ba zata sake ganinshi ba sai wani watan, abun mamaki shine ko sau ɗaya bata taɓa mishi godiya ba balle ta nuna a fuska cewa abun da yake mata yana taimakonta kwarai da gaske.
Chapter 9 · 0% Book details