← Book details Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 26

Sashe 16

Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daddy da ka barshi kawai." Faɗin Juwairiyya tana ƙoƙarin kwace kuɗin amma ya damƙe har yana shirin kokawa da ita.

Bata yi aune ba ta ji sautin dariyar Daddy a hankali domin da alama abun ya ƙayatar dashi.

"Yaro ma ya fiki sanin me ya dace, he meant to say ba'a maida hannun kyauta baya. Sai anjima." Yana gama faÉ—in hakan annurin fuskarshi ta É—auke kamar wanda ya tuna da wani abu.

Ganin haka yasa Juwairiyya saurin fita daga motar har tana cin tuntuɓe, tana matsawa daga jikin motar ya juya a hankali a bar gurin ba tare da ya ƙara kallonta ba. Sai a lokacin ta tuna cewa ba fa auren soyayya suka yi ba, aure ne na rufin asiri kuma wanda aka yi shi cikin gaggawa, aure ne da aka yi tsakanin ruhi biyu wanda suke cikin damuwar rashin masoyansu. Nan take ta ji ta ƙara tausayin kanta akan wanda take yi, ko yaya rayuwarsu zata kasance? Ko a wani matsayi Daddy zai ɗauketa alhali ya saba da ganinta a matsayin ƙawar ƴarshi.

Bata gama wannan tunanin ba su Salima da suka yi parking a bayansu suka iso suna É—aga nata signa suna dariya.

"Me kika bashi haka har ya biya da tukuici?" Faɗin Hafsat tana leƙen fuskar Juwairiyya wacce ke ƙoƙarin shanye hawayen idanunta.

"Kun fiye gulma wallahi. Masoyi (Hafiz Junior) ya gani wai ya mishi kyau shine ya bashi." Ta faɗi hakan tana miƙawa uwarshi kuɗin bayan ta yi nasarar kwacewa daga hannunshi ganin ya fara kaiwa baki.

Kuka Hafiz J ya dalla yana miƙa hannu ga mamanshi da alama ya tuna da ita ne ko kuma don kuɗin ya koma hannunta ne sai Allah. Hakan yasa su Salima suka fasa faɗin abun da yake bakinsu suka dawo rarrashinsa daga baya suka ɗunguma cikin gidan ganin sauran mutanen da suke waje suma sun shige ciki.

Da la'asar aka saka anko aka yi buɗan kai, zuwa isha kowa ya watse aka bar Amarya da Angonta da kuma halinsu. A daren ranar misalin ƙarfe sha ɗaya na dare Juwairiyya tana zaune a ɗakinta inda zata kwana da mutane biyar waɗanda suka zo biki ta jawo jakarta da nufin ɗauko igiyan charger sai ta ga kuɗi mai yawa har dami biyu. Nan da nan ta gane  Salima ce ta saka mata domin ɗayan babu makawa kuɗin da Daddy ya bata ne ta kasa gida biyu ta ɗauki rabi sannan ta ajiye mata rabi, ɗayan kuma dubu hamsin ɗin da Muhammad ya bata na gudumawa ne ta ƙi karɓa shine ya aiko matarshi dashi.

Samun kanta ta yi da jin sanyi a ranta domin duk yanda ta kai da son riƙe Muhammad a ranta yanzu ta rage, sai yanzu take tambayar kanta dama me ya mata? Da wannan tunanin ta ɗauki wayarta bayan ta jonata a charge ta turawa Salima text ɗin godiya tare da cewa ta miƙa godiyarta ga Muhammad.

Bayan kwana uku gida ya watse ya dawo na masu gidan su kaÉ—ai, ko'ina an wanke an gyara tamkar ba'a yi biki ba sai kuma kewan Sumayya kowa ke yi musamman Iya (Kakarsu) da yake da ita Sumayya take kwana.

Ba'a ƙara wasu kwana biyun ba Mama ta zauna da Juwairiyya akan maganar tarewarta a gidan Daddy.

"Ina ta jiran ki mini maganan tarewanki amma sai naji shiru, yaushe ya ce zaki tare?"

"Yace duk lokacin da na shirya domin gidanshi ba ya buƙatar wani gyara."

"To kayanki na yanzu zaki tafi dasu ko kuma wasu zaki canja?" Mama ta tambayeta wanda ta san amsan ko ba'a faÉ—a mata ba.

"Mama dama tun wancan lokacin na ce miki a sayar ba zan ƙara amfani da su ba, kayan kitchen kaɗai zan ɗauka da sauran ƙananun abubuwa amma banda gado da kujeru."

"Shikenan, zan yiwa Bala Capenter magana sai ya sayesu a baki sabo, in ma za'a yi ƙari ne sai mu yi. Ana ribibin bikin nan masu hayan gidanki suka yi biya na shekarar gaba, sai ki rubuta ki ajiye, kuɗin kuma yana cikin account ɗina in kina so in turo miki."

"A'a Mama ki ajiye, idan ina da buƙatar wani abu zan miki magana." Faɗin Juwairiyya tana jin tsoron Allah da kuma tsoron rayuwa na daɗa shiga jikinta.

Wai yau ita ce mamallakiyar gidan ta da rayu ita da Hafiz a ciki? Bayan gama takabanta aka haɗu don rabiyan gado, a nan aka haɗa dukiyar da Hafiz ya mallaka wanda ya kunshi gidan da suke ciki, babban gona, mota da kuma wasu kuɗade da ke cikin banki. Iyayen Hafiz da suka tashi rabiyan sai basu yiwa Juwairiyya kyashi ba, a maimakon su sayar da komai sai a raba kuɗi kamar yanda wasu suke yi sai suka damƙa mata gidan a matsayin nata gadon sauran babban gona, mota da kudaɗe kuma suka raba tsakanin iyayenshi da ƴan'uwanshi. Bayan an gama rabiyan gado aka damƙawa Juwairiyya takardun gida da kuma makulli, a wancan lokacin tana tunawa itama miƙawa Mama ta yi domin kamar haushin kowa take ji, wai har za'a tsaya ana raba dukiyar Hafiz? Yaushe ma mutuwar ta fita a zuciyarsu? Abun da ta manta shine haka Allah Ya tsara domin gujewa fitina da kuma samun sauƙi ga shi mamacin.

"To sai ku yi magana ku tsaida rana a kaiki a wuce gurin."

"Mama wallahi sai in dinga ganin kamar bakya sona kin gaji da kallona, kamar zamana a gidan wani abu nake tare miki." FaÉ—in Juwairiyya a marairaice kamar zata yi kuka.

"Sonki da nake yi yasa nake son ki shiga inda zaki zama mai mutunci abun mutuntawa. Shekaru aru-aru ina zawarci Juwairiyya, na ga mutane kala-kala a wannan journeyn nawa wanda da ba don ku ba da nima nayi auren na rufawa kaina asiri. Amma na ga bazan iya watsar daku ba, tunaninku kaɗai ba zai barni in yi zaman gidan mijin cikin kwanciyar hankali ba, I just couldn't. Ke kuma babu ɗa babu jika ga ƙanƙantar shekaru, aure ne kawai ya fi dacewa da ke. Zaki fahimceni komin daren daɗewa Juwairiyya."

Sati daya da haka aka yiwa Juwairiyya jerenta a gidan Daddy gefen matar gidan ta da, falo ne madaidaici sai ɗakuna uku a ciki wanda ɗaya yake a rufe wanda nan ne ɗakin Mummy na da, ɗayan ɗakin shi aka barwa Juwairiyya yayin da ɗayan kuma yake na baƙi kuma na Halima a da. Gefen maigidan kuma shima falo ne babba mai ɗauke da ɗakin bacci ɗaya da kuma wasu ɗakuna biyu a waje wanda ɗaya na ɗanshi Abduljalil ne ɗayan kuma na baƙi maza.

Yanayin tsarin gidan sosai ya burge Æ´an'uwanta da suka mata jere, bayan sun koma suka faÉ—a mata har sabon fenti aka yiwa sashen nata. Washe gari kuma Juwairiyya ta shirya tarewa.

Sosai Mama tasa aka mata gyara ciki da waje duk da cewa Juwairiyyan ta ƙi yarda a farko, amma da Mama ta zare mata ido sai ta dawo cikin hayyacinta aka mata gyaran fata, kitso da kuma kunshi mai kyau. Nan da nan ta fara walwali ta fito a Amarya sakk sai dai raman da tayi ne ya kasa ɓuya.

Halima ce tare da wata ƙanwar Daddy wacce zata yi sa'ar Mama suka zo ɗaukanta bayan sallah isha, Juwairiyya kuka take yi kamar yau ne za'a kaita gidanta na fari. Sosai ta bawa Mama tausayi wacce ta kasa magana saboda ta san in dai ta buɗe bakinta itama zata taya ƴar tata kuka, tana ji tana gani aka fitar da ita daga gidan don zuwa bautawa ubangiji.

Waɗanda suka mata rakiya basu jima ba suka tafi bayan sun mata addu'a tare da fatan alkhairi. Salima ce ta ƙarshen tafiya wacce Muhammad ya zo ya ɗauka jimm kaɗan da tafiyan sauran. Juwairiyya ta yi kuka har sai da ta ji kanta ya fara ciwo sannan ta tsagaita, duba agogo ta yi taga ƙarfe goma sha ɗaya na dare, to ina maigidan nata yake?

Tashi tayi tana kallon tsarin ɗakin irin yanda tace tana so, babu hayaniya domin set ɗin gado ne mai haɗe da mirror da kuma wardrobe, sai ɗan decoration kaɗan a jikin bango don kar ginin ya zama wayam. Banɗakin da ke cikin ɗakin ta shiga nan ma ta sameshi tsaf irin yanda ta hasko a ranta, alwala ta ɗauro sannan ta zo ta tada sallahn shafa'i da witri. Tana idarwa ta ji ana kwankwasa ƙofar ɗakinta ta yi sauri miƙewa tsaye zuciyarta na bugawa ta dubi kanta a madubi, in banda ramar da ta yi babu abun da ya samu fuskarta don ta wanke duk kwalliyan da aka mata kafin a kawota.

Ƙara kwankwasa ƙofar aka yi wanda hakan yasa ta isa ta buɗe tana mai matsawa gefe. Daddy ne ya shigo ɗauke da wasu ledoji a hannunshi bakinshi ɗauke da sallama amma fuskarshi babu walwala sannan ba'a tsume ba.

Russunawa tayi ta gaisheshi bayan ta zauna a bakin gado shi kuma ya amsa yana mai shiga cikin ɗakin ya tsaya a gefen mirror sannan ya ajiye abun hannunshi akan ƙaramin carper ɗin da yake bakin gadon,

"Ga abinci kici in kina jin yunwa, in kuma kin koshi ki adanashi." Ya faÉ—a yana kalle-kallen É—akin wanda kwata-kwata ma hankalinshi baya ma kai.

Gyaɗa kai tayi kana ta haɗa ta 'to'. Daga nan suka yi shiru na wasu seconds goma kana Daddy ya tako zuwa bakin ƙofa zai fita sai kuma ya tsaya ya fara magana ba tare da ya kalli inda take ba,
Chapter 16 · 0% Book details