← Book details Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 26

Sashe 5

Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A nan ya sanar dani cire rai da yayi da rayuwa wanda bai bari muka rabu ba sai da yasa na yarda da wani alƙawarin da yace in ɗaukar mishi."

"Alƙawrin menene?" Ta samu kanta da tambaya don a take zuciyarta ta dawo da saurin bugawar da take yi ɗazu.

  Tunani kala-kala kuwa babu wanda bata yi ba kwakwalwarta na bata wild ideas na wannan alƙawarin da mijin nata ya ɗauka ciki kuwa har da cewa idan matarshi ta haihu Hafiz ya riƙe mishi ɗan kar a barwa Salima saboda mugunta.

Ya saka na mishi alƙawarin duk ranar da ya mutu in auri matarsa Salima in kuma riƙe mishi duk abun da zata haifa kar yayi agolanci a wani gida."

  Cikin azama juwairiyya ta tashi zaune har tana buge bakin Hafiz da kanta ba tare da ta sani ba, sosai ya ji zafi har ya ɗanɗani jini a bakinshi amma yayi shiru bai nuna mata ba saboda abun da yake gabansu yafi ƙarfin zogin ciwonsa.

"Wannan wace irin banzar magana ce?!" Ta tambaya tana aikawa Hafiz wani mugun kallo wanda har lokacin yana kwance bai ko motsa ba yana ganin yanda fuskarta ta rikiɗa lokaci guda da tsantsan kishi, ɓacin rai da kuma wani abu kamar tsoro a kwayar idanunta.

"I swear Juwairiyya ban san me yasa yayi wannan maganar ba, kuma kukan da yake tayi kamar ƙaramin yaro yasa na ɗauki wannan alƙawarin ba don na taɓa kawo hakan a cikin raina ba. Sannan gani nayi cuta ba mutuwa bace, don yana yawan rashin lafiya bashi zai sa ya gane mutuwa zai yi ba saboda wani yana kwance ma a gadonshi lafiyarshi kalau za'a zare ransa idan lokacinsa yayi. Wani yana tafiya yake faɗi ya mutu yayin da wani abinci ma yake ci zai yi lomarsa ta ƙarshe ya kwanta ya mutu. Na amsa mishi ne don ya daina kukan da yake yi kuma ya bani tsoro ne saboda ban ta6a ganin yana kuka cur-cur da idanuwanshi irin haka ba, ko lokacin da mahaifiyarsa ta rasu bai yi kukan da yayi yau ba. Juwairiyyah tsakanina dake babu 6oye-6oye, shiyasa nake faɗa miki duk abun da ya shafeni bana son na 6oye miki daga baya ki ji ranki ya 6aci kiyi zaton ban ɗaukeki da muhimmanci ba."

  Shiru Juwairiyya ta yi amma tuni idanunta sun fara tara kwalla, wani irin tsana Muhammad yake mata da tun kafin ya mutu zai bada wasiyyar a ƙuntata mata ta hanyar mijinta ya auri matarsa wacce ta kasance ƙawa a gareta? Shanye hawayen idanun nata tayi ta hanyar kallon saman ɗakin ta buɗe bakinta a hankali tana jan numfashi ta nan tana kuma furzarwa. Sai da ta daidaita kanta sannan ta dubeshi har lokacin zuciyarta bai daina bugu ba wannan karon tambaya zata mishi wanda take tsoron amsar da zai bayar.

"What if in ya mutun? Zaka cika alƙawarin ne ka auri Salima?"

Ƙura mishi ido tayi tana ganin ruɗu a fuskarsa wanda ko bai faɗa ba ta gane amsarta.

"Juwairiyya ki bar maganan nan haka, shima da yayi maganar bana tunanin yana cikin hankalinshi ne sannan who does that for God sake? Ki É—auki abun tamkar ba'a yi ba, don ni wallahi har na fara dana sanin faÉ—a miki saboda ban yi tsammanin zaki É—auki abun da zafi har haka ba. I thought zaki É—auki hakan ne a matsayin shirme mu wuce gurin."

"Zaka aureta ko ba zaka aureta ba?" Ta share duk zancensa ta ƙara mishi tambayar a karo na biyu.

  Sai a lokacin Hafiz ya gane da gaske ta ɗauki maganar da zafi ya tashi zaune ya kai hannu zai jawota jikinshi ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga mishi hannu tace,

"Just answer me."

"Riya I told you...."

"Hafiz don Allah ka amsa mini. Please." Ta yi saurin katseshi muryarta har ɓari take yi wanda har sunanshi da bata iya kira a gabanshi yau sai da ta kira.

  Sunkuyar da kanshi yayi ƙasa kana ya ɗago a hankali yace,

"He made me promised tare da rantsuwa da Allah akan zan nemi aurenta sai dai in ita ce ta ƙi amincewa sannan zan haƙura, and I know itama ba zata yarda ba saboda ƙawancen da yake tsakaninku."

"Baka sani ba dai, babu macen da zaka je mata da zancen aure ta ƙi amincewa da kai Hafiz. Kana da qualities ɗin da mace baza ta iya bari ka wuceta ba."

Sai a lokacin kafaɗun Juwairiyya suka sauƙa alamar defeat domin a yanda take faɗawa Salima labarin kyawawan halayen Hafiz zai yi wuya idan ya je mata da zancen ta gujeshi sai dai in ta ji kunyarta ne ta ƙi amincewa.

Kwanciya ta yi nesa da Hafiz wanda yana ganin hakan yaji babu daÉ—i a ranshi domin bai ga abun tashin hankali a cikin wannan zancen ba, shi wanda ya kawo maganar ma yayi imanin tsoron mutuwa ce tasa yayi maganar amma ba don zai mutun ba duk da cewa cikinsu babu wanda yake da guarantee É—in kai tsufa.

"This is all stupid, da maganar da reaction É—inki da kuma fushin da kike son ki mini Juwairiyya. But I will let you sleep on it zuwa gobe mu ga ko kema zaki yi tunani irin nawa. Sai da safe." Yana faÉ—in hakan shima ya kwanta zuciyarsa a cunkushe bayan ya kashe musu wutan É—akin.

https://www.wattpad.com/story/286189663?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details&wp_uname=suwaibamuhammad36&wp_originator=WLgoX5LRZroSfrBXS%2FvJrrmcD4YgBmuG2AZVLtFDowb3gKdO5KroKIOwg6bGrFV8QQ8fuBBc7AoDDvlLV9Nvw3NykipgrNBJaNLKpKqXzAcz2XEZcJ%2FQyfCE1gepfEdH

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey)

Wattpad https://my.w.tt/IKR4zCOYfbb

(3)
Washegari da safe Hafiz da Juwairiyya suka tashi dukkanninsu jiki a sanyaye. Ƙarfe goma na safen lahadin ta gama musu breakfast suna ci cikin silence kamar ba su ba, lokaci-lokaci tana satar kallonshi tana ganin yanda yake juya taliya da sauce ɗin a jikin fork wanda sai ya yi kusan minti ɗaya kafin ya kai bakinsa, bai gama cin abincin ba ya tashi ya kai plate ɗin kitchen ya fito yana cewa,

"Zan je gidanmu, daga nan kuma akwai wani abokina da ya shigo gari zamu haɗu. Zan dawo bayan la'asar, akwai abun da kike buƙata ko kike so in dawo miki dashi?"

"Babu komai. Allah Ya dawo da kai lafiya." Kawai ta faÉ—a tana kallonshi cikin ido tana jin zaman nasu a haka har ya gundureta.

"Ameen. Take care, sai na dawo." Da haka ya sa kai ya fice.

  Ajiye fork ɗin hannunta tayi tana sauraran duk motsinsa a farfajiyar gidan, bayan ya kunna mota yayi warming ɗinta na wasu mintuna sannan maigadi ya buɗe mishi gate ya fita daga gidan. Tana jin ƙarar rufe gate ɗin idanunta suka ciko da hawaye kana suka silalo kan ƙuncinta. Wai me yake damunta ne? Cewa aka yi Hafiz zai yi aure ko kuma ta ga Muhammad ɗin ya mutu? Sannan ta yaya ma Salima zata yarda ta auri Hafiz alhali suna ƙawance da ita? Menene laifin Hafiz? Shin ta mishi adalci ko kuma tayi aiki da hankalinta wajen auna wannan zancen? Me amfanin wannan cold shoulder da take bashi? Shi yayi laifin ne ko Muhammad? Bata kyauta masa ba, idan tayi haka bata mishi adalci ba, sannan hakan da tayi zai sa a gaba ya 6oye mata damuwarsa saboda tana amfani da emotions ɗinta ba kwakwalwarta ba. Babu mai laifi kuma mugu irin Muhammad da ya nemi a yi mata kishiya, sai yanzu ta ƙara tabbatarwa tsanan da yake mata ya wuce yanda take tsammani. While Hafiz did not deserve any of this!

  Wannan duk tunani ne da Juwairiyya take yi a cikin zuciyarta tana jin tausayi tare da ƙaunar mijinta na ƙara shiga zuciyarta, ta wani gurin kuma tsanar Muhammad ne ya yawaita har tana jin da zata ganshi da ta kwaɗeshi da mari. Sannan ko mutuwa Muhammad ɗin yayi ba zata yarda Salima ta aure mata miji ba, kai Muhammad ɗin ma ba zai mutu ba, daga yau zata fara sakashi a addu'a Allah Ya bashi lafiya Ya ƙara mishi tsawon rai. Ita kuma wannan shine alƙawarinta.

  Kafin la'asar Juwairiyya ta gama girki ta gyara gidanta ko'ina sai tashin ƙamshin yake yi tana jiran a kira sallah ta shiga wanka, ana fara kiraye-kirayen sallah kuwa ta shiga banɗaki ta sillo wanka sannan ta yi sallah ta zauna a gaban mirror ta fara ƙawata fuskarta.

Jim kaɗan da haka ta gama tsara kwalliyar ta sanya Atamfa riga da siket ɗinkin Borno Style da yayi matuƙar karɓan jikinta mai kyawun shape. Falo ta koma ta nemi kujera ɗaya ta haye ta ƙame tana jiran maigidanta Hafiz.

  Ƙarfe huɗu da rabi Hafiz ya dawo ya tarar da Juwairiyya ta kunna kallo a falo tana zaman jiranshi. Ajiyar zuciya ya sauƙe domin ganinta kaɗai kan tafiyar da wani kaso mai tsoka na damuwarshi da kuma gajiyarshi.

Da murmushi a fuskarshi ya mata sallama ta amsa cikin fara'a kamar yanda kullum ta saba sannan ya shigo ya ajiye abun hannunshi a kan center table dake tsakiyar falon yana cewa,

"Da ba don ina kishinki ba da na kai ki inda ake zaɓen sarauniyar kyau ta duniya, amma ni ɗaya nake son ganin wannan kyau da kwalliyan."

Murmushi tayi mai ƙayatarwa har kumatunta na lotsawa don ba ƙaramin daɗi take ji idan Hafiz ya furta kalamai irin haka a gareta ba, ko ba komai bata yi asaran zama a gaban mirror tana shafe-shafen ba, domin kuwa wanda aka yi kwalliyar domin shi ya gani kuma ya yaba.

"Bee kana ƙara zugani." Ta faɗi hakan don bata gaji da jin kalaman yabon daga gareshi ba.

"Babu zugi Riya, shin kina kallon kanki a madubi kuwa? Da kina ganin me nake gani da baki kawo kokwanto a ranki ba, you are the most beautiful woman I have ever seen and you are mine, mine alone." Da haka ya miƙar da ita tsaye ya jawota jikinshi kana ya sumbaci goshinta affectionately.
Chapter 5 · 0% Book details