← Book details Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 26

Sashe 8

Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata ankara ba ta ji an make mazaunanta ta juyo tana hararanshi, shi kuma da yayi aika-aikan dariya yake yi.

"Nace miki bani da lafiya shine kika yi gaba kina nuna mini abubuwa ko?"

"Mutum mara lafiyan ne idonshi zai je can? Dama sakalcinka ne ya tashi kake son baccin rana."

"Na ji." Kawai ya faɗa yana taɓa wani sashe na jikinta.

"Bee." Ta furta a lokacin da suke shiga É—aki.

"Na bari, amma ina tashi zan baki saƙo." Ya ƙarisa maganan yana kashe mata ido ɗaya.

Murmushi kawai ta bishi dashi kana ta taimaka mishi ya cire kayan jikinshi sannan ya kwanta ita kuma ta koma falo don bata jin bacci. Wayarta ta É—auka ta kira Salima tana tambayarta jikin Muhammad don a yanzu bata son ko da wasa ta ji bashi da lafiya.

“Jiki da sauƙi za'a ce, gashi can dai a ɗaki ya kwanta."

Dariya Juwairiyya ta saka wanda daga ita har Salima sun yi mamakin hakan.

"I'm sorry, amma wallahi ba dariyar rashin lafiyarshi nake yi ba, É—azu Hafiz ya dawo shima wai kanshi yana ciwo ya kwanta yana bacci. Shine na yi picturing É—in mu a matsayin Nannies abun ya bani dariya."

Wannan karon itama Salima ta dara kana suka yi sallama. Da haka Juwairiyya ta cigaba da danna wayarta wanda karatun littafin Hausa take yi, lokaci-lokaci tana murmushi idan aka zo gurin soyayya wanda sai take ganin kamar ita ce da Hafiz É—inta.

Tana nan zaune har aka kira sallan la'asar aka shiga sallah sannan ta tashi don ta gabatar da nata kuma ta tashi Hafiz.

"Bee ka tashi lokacin sallah ya yi." Ta faÉ—i hakan a yayin da take shiga banÉ—aki.

Bayan ta gama alwala ta fito ta samu ko motsawa Hafiz bai yi ba, hakan yasa ta saÉ—aÉ—a a hankali zata watsa mishi ruwan hannunta sai ta sameshi idonshi a rufe yana murmushi.

"Allah Ya taimakeka domin na tuno baka da lafiya. Ka tashi mu yi sallah."

Shiru bai amsa mata ba, hakan yasa ta watsa mishi ruwan kaÉ—an a fuskarshi amma ko firgita bai yi ba haka kuma bai motsa ba. Nan take ta ji wani tsoro ya É—arsu a zuciyarta ta sa hannu ta fara jijjigashi amma kamar bashi da rai.

"Wayyo Allah na, Hafiz! Ka tashi bana son wannan wasan wallahi. Ka bari, ka bari, ka bari." Tana faÉ—an hakan tana jijjigashi amma babu alamar rai a tattare dashi.

Ihu ta kwala mai ƙarfin gaske nan take kuma jikinta ya fara rawa ta kamo kafaɗunshi don ta miƙar dashi zaune amma ya fita nauyi sai ta gagara yin hakan.

Wani ihun ta sake kwalawa kamar wacce ta zauce kana ta fara kiran sunan Allah.

"Allah ka rufa mini asiri, Allah kar ka mini haka. Wayyo Allah na!!"

Fita tayi da gudu zuwa gurin maigadi wanda tun ihunta na farko ya jiyota amma bai je ba, sai dai ya tsaya on alert, ihunta na biyu kuwa yasa ya zo bakin ƙofar falon ya fara kwankwasawa yana kiran sunan ubangidan nashi tunda yana gida. Tana buɗe ƙofar ta kamo hannunshi tana nuna mishi ɗaki tana cewa,

"Baba... Hafiz... yana ciki baya motsi. Hafiz ya mutu."

Kwace hannunsa yayi ya shiga É—akin da gudu ita kuma tsabar ruÉ—ewa ta É—auki wayarta ta kira Salima wacce ringing É—aya ta É—auka amma kafin ta yi magana Juwairiyya ta rigata tace,

"Ki tayar da Muhammad ya zo ya kai Hafiz asibiti baya motsi, don Allah ya zo da sauri kar ya mutu."

Tana gama faɗin hakan ta shiga ɗakin inda ta samu Baba a durƙushe a gaban gadon inda kan Hafiz yake yana kallonshi with so much pain on his face.

"Baba ya mutu ko?" Ta tambaya tana jin zuciyarta kamar ana toye mata shi, idanunta kuwa tuni suka fara zubar da hawaye babi-babi.

"Ki kira yayunshi su zo su kaishi asibiti likita zai dubashi."

Wayarta da ke hannunta ta duba ta kira babban yayanshi wanda dama a unguwar Tumfuren yake bashi da nisa da su. Yana É—aukan wayar ta fara magana,

"Yaya Aminu ka zo ka kai Hafiz asibiti bashi da lafiya kuma baya motsi."

"Subhanallahi. Me ya sameshi?"

"Bayan sallah Jumma'ah ya dawo yace mini kanshi na ciwo shine ya kwanta ya daina motsi, ni da Baba maigadi kuma baza mu iya ɗagashi ba." Ta ƙarishe maganan tana jan majina tana goge fuskarta da ɗan kwalinta.

"Bani wayar in mishi magana." Faɗin maigadin yana miƙa hannunshi ta bashi babu musu.

"Alhaji sai dai haƙuri, amma Hafizu ya rigamu gidan gaskiya." Ya faɗa a hankali amma Juwairiyya ta ji sarai.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Shine abun da Juwairiyya ta yi ta maimaitawa bayan ta durƙushe a gurin da take. Nan take kanta ya fara juyawa tana jin tamkar itama jan ranta ake yi dalilin mutane da ta fara kallo biyu-biyu zuwa uku, can kuma suka fara yawa har bata iya ƙirgasu. Can ta ji kamar ana saka mata hijabi zuwa can ta ji koke-koke kamar Umma ce mahaifiyar
Hafiz.

Daga nan kuma ta ji an ɗagata daga durƙushen an kaita ɗakinta bayan an lulluɓe fuskar Hafiz da mayafin da ta lulluɓeshi da zai kwanta bacci ɗazu.

Hello dearest!

Transform Your Cooking Skills, Banish Unpleasant Food Odors, and Prevent Food Poisoning

Have you ever been put off by the unappetizing parts of chicken or the lingering odors from certain fish and chicken dishes? Perhaps you've encountered the off-putting residues from cow waste in some dishes. These issues can make mealtime less enjoyable and even contribute to food poisoning. Ga AiLisco ta zo da educative eBook ɗinta mai ɗauke da sirrin kitchen. Ku danna wannan link ɗin domin ku yi mata magana direct ta whatsapp https://wa.me/message/DR5SQZYEPBBEO1 ko kuma number wayarta (09123227777) Kar ku manta launch fee is ₦1000 only, in an wuce ranar zai dawo ₦3000. Ku yi sauri ku yi payment ɗinku tun yanzu.

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064

Wannan littafi na kuɗi ne a ₦500 zaku tura ta wannan Bank account 5139579011 FCMB Suwaiba Babagana, ko kuma katin waya na Airtel a wannan number 09023713064, da number zaku yi amfani don nuna shaidar biya don a sakaku a paid group. Waɗanda basa son hayaniyar group zasu tura ₦650 don a dinga tura musu a private chat.

Kar ku manta akwai sabon book da nake yi tare da wannan wanda shi kuma free ne mai suna CANJIN MUHALLI. Ku mini magana a number wayata don in sakaku a group da zaku dinga samunshi ko kuma ku duba Wattpad da ArewaBooks. Nagode.

(5) Free page
Kwanaki suka shuɗe suka dawo satittika, satittikan suma haka suka wuce suka dawo watanni. A hankali duk wasu alamu da zasu nuna ta taɓa rayuwa dashi suka fara ɓacewa. Bata sake ganin fuskarshi ba tun ranar da aka rufeshi da bargonta, sai dai a kullum yana cikin mafarkanta.

Rayuwarta ta fara dawowa kamar da a lokacin da take budurwa a gidansu, zata ci zata sha amma tana cikin gida bata fita ko'ina. Komai ya dawo normal amma banda ita, domin kuwa bata jin kanta kamar yanda ta saba. Ya tafi ya barta da wani gurbi a zuciyarta da babu mai iya cikawa sai shi, Hafiz É—inta.

Tunaninshi yana bibiyarta a kowanne lokaci kamar baƙon da ba'a gayyaceshi ba. A ko'ina take sannan ko menene take aikatawa yana nan maƙale a zuciyarta da kuma kwakwalwarta wanda hakan yasa bata iya maida dukkan hankalinta akan abun da take yi.

Da dare in ta kwanta idanunta zasu bushe daga ƙin yin bacci, zata shafe awanni tana tuno rayuwarsu wanda su suke gaskata mata cewa ta taɓa sanin shi. Da wannan tunanin zata tashi ta ɗauro alwala ta fara sallah tana nema mishi gafara a gurin ubangiji har kwakwalwarta ta nemi hutun dole ta sanyata baccin da bata yi niyya ba.

********
Salima ta haihu ta samu É—a namiji wanda yau ake bikin suna amma Juwairiyya bata da niyyar zuwa. Tana kwance a É—akinta ta jiyo sallamar yaro a tsakar gidansu, bata amsa ba don ba aikinta bane. Tunani take yi da Hafiz yana da rai da yanzu tana can gidan sunan tana shige da fice a matsayinta na matar abokin mijin mai jegon.

Tana jin immediate ƙanwarta Sumayya ta amsa sallamar daga can bakin kitchen sannan ta bi yaron da tambayar dalilin shigowarshi.

"Wai ana sallama da Juwairiyya a waje."

"Je ka tambaya in ji waye."

Jimawa kaÉ—an yaron ya dawo ya ce,

"Wai in ji Hussaini ne wanda suka gama makaranta tare."

Juwairiyya da take ɗaki ta ja wata doguwar tsaki tana jin kamar ta fita waje ta gaurawa Hussaini mari. Yaron ya rainata sosai yanda bata tsammani, zata iya tunawa shine mutum na farko da ya taɓa nuna yana sonta bayan ta gama takaba. Tsabar rashin kunyarshi har cikin gidansu ya shigo ya samu Mamanta wai ya zo yana sonta ta bashi izinin zuwa hira. Duk ransu ya ɓaci amma Mama bata nuna mishi a fuska ba ƙarshe tace ya je ya ƙara haƙuri sai mutuwar ta fita a ranta.

"Wallahi in ya sake taka cikin gidan nan da sunan wai yana sona sai na sa yaran unguwa sun mishi wanka da kwata. Don uwarshi ni sa'arshi ce? Yaro ƙarami da shi wataƙila ma na fishi shine zai zo mini da maganar aure? To don ubanshi an ce mishi neman mijin auren nake? Kuma in zan yi auren in rasa waye zan aura sai kucakin yaro mara sana'a irinshi?"

"Ina tunanin ya ɗauka a littafin Ruwan Zuma kuke, a ciki ne matar ƴar shekara arba'in (40) ta auri saurayi ɗan shekara ashirin da tara (29), suka yi ta soyewa wallahi har abin kunya yake bani." Faɗin Surayya ƙanwarta ta biyu wacce kwata-kwata shekarunta sha huɗu ne (14).

Maman su da tayi kasaƙe tana kallonsu sai yanzu ta yi niyyar magana, da Surayya ta fara wacce sai da ta gama maganan sannan ta gane ta tafka uban kuskure.
Chapter 8 · 0% Book details