← Book details Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 26

Sashe 20

Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fitowa daga asibitin suka nufi gida bayan sun sayi magungunan, a falonshi suka yada zango Daddy ya shige ɗaki don zai yi amfani da banɗaki ita kuma Juwairiyya ta fara rage kayan jikinta sannan ta jawo ledan magungunan tana dubawa don sanin dosage ɗin su. A haka Daddy ya dawo ya sameta zaune a ƙasa daga ita sai leggings da half vest.

"In ba dole ba bazan sha duka waÉ—annan magungunan ba. Ganinsu kaÉ—ai idan nayi sai in ji zuciyata ta tashi."

"Ohh Daddy ka fiye tsoron magani wallahi, to ko za'a maka alluransu?" Ta faÉ—a cikin zolaya tana murmushi.

"No, bani maganin in sha." Ya amsa yana zama a saman kujera ta fara miƙo mishi yana zubawa a bakinshi yana korawa da ruwa.

Sai da ya shanye sannan ta tattarasu ta zuba a leda kana ta miƙe tsaye don zuwa adanasu Daddy ya riƙo hannunta ya jawota ta tsaya tsakanin ƙafafunshi kana ya ɗaga kanshi yanda zai ga fuskarta ya ce,

"Juwairiyya anya akwai haske a lamarin nan? Anya kuwa zan warke? Aurenmu yanzu wata shida wanda ko sau ɗaya ban taɓa biya miki buƙatarki ba Juwairiyya. Abun yana damuna sosai."

Ajiye maganin tayi a kan kujera a gefenshi kana ta tallafo kanshi da hannayenta duka biyu ta kalli fuskarshi wacce take tattare da damuwa ta sumbaci goshinshi kana ta ce,

"Neman magani muke yi wanda dama ba lokaci É—aya zamu samu waraka ba, dama mutum kan iya shan magunguna kala goma sai a na sha É—aya yayi dace. To mu ma bamu fara don mu bari ba, da yardar Allah zaka samu lafiya ka daina ma kawo waswasi a ranka. Ka ji Babyna?"

Murmushi yayi mai ƙayatarwa yana jin sanyi a ranshi domin Juwairiyya ta san yanda zata kwantar mishi da hankali muddin ya furta mata cewa ya karaya ko kuma ya nuna mata alamun hakan.

"Juwairiyya bana son cutar da ke, kullum buƙatarki ƙara ƙaruwa take yi...." Bai kai ga ƙarisa maganan ba ta tari numfashinshi ta ce,

"Mu bar zancen nan, yanzu ba magani aka É—auraka a kai ba?"

"Hakane."

"To ka gani. Don't lose hope. Ka ji?"

"Na ji rigimatu." Ya faÉ—a yana dariya.

Itama darawan ta yi kana ta É—auki ledan da ta ajiyen ta je ta adana kana ta nufi sashenta don É—aura musu abincin rana dama fitan hantsi suka yi.

A daren ranar Juwairiyya ce kwance a jikin Daddy a ɗakinshi suna hira kaɗan-kaɗan yana danna wayarshi, can ya dakata da danne-dannen ya ajiye wayar a gefe yana jin yanda Juwairiyya take mutsu-mutsu a jikinshi kamar wacce ma hankalinta baya jikinta. Ji yayi hawaye ya taru a idanunshi amma yayi saurin maidasu domin gudun kar ta gani, a jikinshi kuma bai ji wata alama da zata nuna zai iya taimakonta ba wanda hakan shine abun da ya fi tsoro a yanzu. Hannunshi ya kai wani sashe na jikinta wanda ya sa ta ƙara birkicewa ya ce,

"There, there, let me help you a little."

Bayan wata ɗaya Daddy ne tsaye a falonshi tare da Juwairiyya wacce take mishi shagwaɓa dalilin tafiyar da zai yi na sati biyu.

"Daddy to ka tafi dani mana." Ta faɗa tana bubbuga ƙafanta a ƙasa.

"Ke da kika fara zuwa school shine zaki yi tafiyan har sati biyu? A'a kiyi zamanki a gida, next time idan zan yi tafiya kuma kina hutu sai mu tafi tare."

"Ni dai wallahi ba'a kyauta mini ba, sai da na shiga school sannan zaka yi tafiya mai daÉ—ewa haka?"

"Juwairiyya Rigimatu, to ki barni in tafi kar in yi missing É—in flight É—ina."

Da haka ya mata sallama ya fita harabar gidan inda Abdul Jalil zai tuƙashi zuwa Airpot. Har ya zauna a cikin mota ya rufe sai kuma ya buɗe ya fito ya koma cikin gidan ya samu Juwairiyya tana tattare kan dinning inda ya gama cin abinci. Tana jin shigowarshi ta juyo tana tambayarshi ko ya manta wani abu ne amma bai amsa mata ba ya rungumeta tsamtsam a jikinshi. Murmushi tayi ta fara tsokanarshi ko zai fasa tafiyan ne ya dawo su zauna?

"Duk abun da ya faru ki sani ina sonki Juwairiyya, and please take care of yourself for me. Kin ji?"

"Na ji Daddy kuma Babyn Juwairiyya."

Da haka ya saketa yayi kissing goshinta kana ya fita cikin sauri ta bishi da addu'a fuskarta É—auke da murmushi.

A bakin window ta tsaya tana leƙenshi har ya shiga mota suka fita daga gidan sannan ta juya ta cigaba ta aikinta. Tana gama gyaran falo ta koma ɗakinshi nan ma ta fara gyarawa tana tattare kayanshi da ya cire tare da sauran tarkace. Sai da ta gama ta hango wani damin kuɗi mai yawa akan bedside tare da wani paper a ƙasanshi. Murmushi ta yi domin ta san Daddy ya manta ne dasu domin ya tura mata kuɗi cikin Account ɗinta wanda in tana buƙatar wani abu ta saya duk da cewa suna da komai a gidan.

Kuɗin ta matsar gefe sannan ta ɗauki takardar kamar ba zata buɗe ba amma ta buɗe, contents ɗin da yake ciki yasa ta kwala ihu ta zube a gurin tana kama kanta da dukkan hannayenta, nan da nan kuma kuka mai ƙarfi ya kwace mata har numfashinta na ɗaukewa.

"Mugun mutum! Coward! Ka cuceni ka tona mini asiri. Me yasa ba zaka ƙara haƙuri ba?"

Da haka ta tashi ta ɗauki wayarta hannunta na karkarwa har bata ganin me take dannawa, hakan yasa ta goge fuskarta da hannunta sannan ta samu numbern Daddy ta danna kira amma aka ce mata is switch off. Da haka ta nemo na Abdul Jalil ta kirashi ya ɗauka babu ɓata lokaci,

"Aunty Juwai...." Bai kai ga ƙarisawa ba ta katseshi.

"Ina Daddy?"

"Tun ɗazu na sauƙeshi ni kuma ina dawowa gida. Wani abu ne ya faru?"

Wannan tambaya da ya mata shi yasa ta ƙara fashewa da kuka har tana sarƙewa, shi kuma Abdul jalil hankalinshi ne ya tashi ya fara tambayarta me yake faruwa. Da kyar ta saisaita kanta ta ce,

"Daddy ya sakeni, ya raba auren da ke tsakanina dashi Ya Abdul jalil."

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Me yasa?"

Bata bashi amsa ba ta jefar da wayar ta ƙara zama a ƙasan ɗakin tana kuka tana tausayin rayuwar da zata fuskanta nan gaba.

"Hafiz mutuwarka tonon asiri ne a gareni, rayuwata tana ta gararamba saboda rashinka. Allah ka kawo mini ɗauki, Allah ka ji tausayina ka taƙaita mini wannan wahalan rayuwar."

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064

(12)
Kafin Abdul Jalil ya dawo gida Juwairiyya ta kwashi iya abun da zata iya ɗauka na buƙatunta ta bar gidan. Tana shiga ta samu Mama tana gurin aiki sai Nan (Kakarsu) da kuma mai aiki ne kawai a gidan. Babu ɓata lokaci ta buɗe ɗakin da tayi zawarcinta a ciki ta kwanta akan katifa taci gaba da kuka har Nan ta shigo ta sameta a haka.

"Ke ƴar nan ina miki magana kika ƙi kulani sannan kika shigo nan kina kuka? Me ya faru kika bar gidan mijin naki?"

"Don Allah Nan ki barni da abun da yake damuna ki daina mini wasu tambayoyi." Ta faÉ—i hakan tana mai juyar da kanta É—ayan gefen inda ba zata ga Nan ba.

"Ki ji mini ja'irar yarinya da rashin kunya, don na tambayeki shine ya zama laifi. To mutuwa aka yi kike kukan?" Ta ƙara wata tambayar don bata haƙura ba.

"Ni nace miki wani ya mutu? Babu wanda ya mutu."

"To menene ya faru?"

Daga haka Juwairiyya bata ƙara kulata ba, hakan yasa Nan ta juya ta tafi tana cewa,

"Kici kanki ke É—aya."

Tunda Juwairiyya ta shiga ɗakin bata fito ba har Mama ta dawo daga aiki, Nan tana ganin ta dawo ta bata labarin cewa ga can Juwairiyya a ɗaki ta zo tana kuka. Gaban Mama ne ya faɗi rass wanda sai da ta ga duhu ya wuce lumm ta gabanta sannan ta dafe ƙirjinta ta nufi ɗakin da Juwairiyyan take tana haɗa hanya.

"Menene ya faru kika zo kina kuka Juwairiyya? Ki tashi ki faÉ—a mini abun da ya faru." FaÉ—in Mama tana shiga cikin É—akin ta tsaya kan Juwairiyya.

A hankali ta miƙe fuskar nan tata ta kumbura idanunta sun yi jajur kamar garwashi sannan sun ƙanƙance duk da girmansu. Hijabin da yake jikinta kuwa ya jiƙe da zufa, hawaye har da guntun majina. Buɗe baki tayi da niyyar magana sai kuma wani kukan ya kwace mata har tana sheshsheƙa.

"Juwairiyya ki faÉ—a mini abun da yake faruwa domin hankalina ya tashi wallahi. Ki daina kukan nan ki faÉ—a mini." FaÉ—in Mama wacce a yanzu tsoron ya yawaita a zuciyarta.

"Daddy ya sakeni Mama, ya mini saki É—aya."

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Haka tayi ta maimaitawa bayan ta samu guri ta zauna."Me kika mishi Juwairiyya ya sakeki? Rashin kunya kike mishi ko kuma wani abun?"

"Wallahi Mama babu abun da nake mishi mara daɗi, lafiya kalau muke zaune yau yayi tafiya muka rabu lafiya amma ina shiga ɗakinshi na samu takardar akan bedside. Ko a fuska bai nuna mini ya sakeni ba har muka yi sallama Mama." Faɗin Juwairiyya tana ƙara jin haushin Daddy a ranta.

Dama ga abun da take gudu domin duk yanda za'a yi babu mai yarda da cewa ba laifi ta mishi ya saketa ba. Kwata-kwata auren nasu yanzu ya cika wata bakwai da ɗori! Me yasa ba zai ƙara haƙuri har su shekara ba kafin ya ɗauki matakin ba?

"Haka kawai ba zai sakeki ba Juwairiyya dole akwai wani dalili. Ki faÉ—a mini tun wuri sai mu san yanda zamu gyara al'amarin."
Chapter 20 · 0% Book details